Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Bitar Sashe na 4

Bitar Sashe na 4

Ka tattauna tambayoyi na gaba da malaminka:

  1. Ku karanta Karin Magana 13:20.

    • Me ya sa yake da muhimmanci mu zaɓi abokanmu da kyau?

      (Ka duba Darasi na 48.)

  2. Wace shawara ce daga Littafi Mai Tsarki za ta taimaka wa . . .

  3. Wace irin magana ce take faranta ran Jehobah? Wace irin magana ce take ɓata masa rai?

    (Ka duba Darasi na 51.)

  4. Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne za su taimaka maka ka yanke shawarwari masu kyau game da irin ado da shigar da kake yi?

    (Ka duba Darasi na 52.)

  5. Ta yaya za ka zaɓi nishaɗi da zai faranta ran Jehobah?

    (Ka duba Darasi na 53.)

  6. Ku karanta Matiyu 24:​45-47.

    • Wane ne “bawan nan mai aminci, mai hikima”?

      (Ka duba Darasi na 54.)

  7. Ta yaya za ka yi amfani da lokacinka da kuzarinka da kuma dukiyarka don ka taimaka a ikilisiya?

    (Ka duba Darasi na 55.)

  8. Ku karanta Zabura 133:1.

    • A waɗanne hanyoyi ne za ka iya sa ’yan’uwa a ikilisiya su kasance da haɗin kai?

      (Ka duba Darasi na 56.)

  9. Ta yaya Jehobah zai taimaka mana idan muka yi zunubi mai tsanani?

    (Ka duba Darasi na 57.)

  10. Ku karanta 1 Tarihi 28:9.

    • Ta yaya za ka nuna cewa kana bauta wa Jehobah da “dukan zuciyarka” sa’ad da wasu suka yi ƙoƙarin hana ka bauta wa Jehobah ko kuma suka daina bauta masa?

    • Shin kana bukatar ka yi canje-canje don ka riƙe aminci ga Jehobah kuma ka fito daga addinin ƙarya?

      (Ka duba Darasi na 58.)

  11. Ta yaya za ka yi shiri don tsanantawa?

    (Ka duba Darasi na 59.)

  12. Mene ne kake shirin yi don ka ci gaba da ­ƙarfafa dangantakarka da Jehobah?

    (Ka duba Darasi na 60.)