Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Na Shirya?

Na Shirya?

Na Shirya Yin Wa’azi Tare da ’Yan’uwa a Ikilisiya?

Za ka iya zama mai shela da bai yi baftisma ba idan . . .

  • Kana nazarin Littafi Mai Tsarki a kai a kai da yin addu’a da kuma halartan taro.

  • Kana so kuma ka amince da abin da kake koya, kuma kana marmari ka gaya wa mutane.

  • Kana ƙaunar Jehobah kuma abokanka masu ƙaunarsa ne.

  • Ka cire hannunka daga kowace ƙungiyar siyasa ko addinan ƙarya.

  • Kana rayuwa da ta jitu da ƙa’idodin Jehobah kuma kana so ka zama Mashaidin Jehobah.

Idan kana ganin ka shirya yin wa’azi tare da ’yan’uwa a ikilisiya, malaminka zai shirya yadda za ku haɗu da dattawa don ku tattauna game da hakan.

Na Shirya Yin Baftisma Kuwa?

Za ka iya yin baftisma idan . . .

  • Ka zama mai shela da bai yi baftisma ba.

  • Kana iya ƙoƙarinka kana wa’azi a kai a kai.

  • Kana goyon baya da kuma bin umurnin da “bawan nan mai aminci, mai hikima” ke bayarwa.—Matiyu 24:45-47.

  • Ka riga ka yi wa Jehobah alkawarin bauta masa har abada.

Idan kana ganin ka shirya yin baftisma, malaminka zai shirya yadda za ku haɗu da dattawa don ku tattauna game da hakan.