Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Karin Bayanai

Karin Bayanai
  1.  Mece ce Babila Babba?

  2.  Wane Lokaci Ne Almasihu Zai Bayyana?

  3.  Hanyoyin Jinya da Suka Shafi Batun Jini

  4.  Abubuwan da za su iya sa ma’aurata su rabu

  5.  Ranakun Hutu da Bukukuwa

  6.  Cututtuka Masu Yaɗuwa

  7.  Kasuwanci da Dokokin Gwamnati

 1. Mece ce Babila Babba?

Ta yaya muka san cewa “Babila Mai Girma,” wato Babila Babba ce take wakiltar dukan addinan ƙarya? (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:5) Ka yi la’akari da waɗannan abubuwan:

  • Tana nuna ikonta a dukan duniya. Littafi Mai Tsarki ya ce Babila Babba tana zaune a kan “taro masu yawa, da al’ummai.” Ƙari ga haka, tana “mulki a kan sarakunan duniya.”​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​15, 18.

  • Ba ƙungiyar siyasa ko na kasuwanci ba ce. Ba za a halaka ta tare da “sarakunan duniya” da “ ’yan kasuwa” ba.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:​9, 15.

  • Tana ɓata sunan Allah. Littafi Mai Tsarki ya kira ta karuwa domin tana cuɗanya da gwamnatoci don ta sami goyon bayansu ko kuma arziki. (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 17:​1, 2) Tana ruɗin mutane daga ko’ina a duniya, kuma tana jawo mutuwar mutane da yawa.​—Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 18:​23, 24.

Return to lesson 13 point 6

 2. Wane Lokaci Ne Almasihu Zai Bayyana?

Littafi Mai Tsarki ya ce za a yi shekara arba’in da tara (49), da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu (434) kafin Almasihu ya bayyana.​—Karanta Daniyel 9:25.

  • Yaushe ne wannan lokacin ya soma? Ya soma a shekara ta 455 kafin haihuwar Yesu (K.H.Y). A lokacin, Nehemiya ya koma Urushalima don ya “sabunta” birnin kuma ya “sake gina” shi.​—Daniyel 9:25; Nehemiya 2:​1, 5-8.

  • Shekaru nawa ne wannan lokacin ya ɗauka? Idan muka haɗa shekara arba’in da tara (49), da shekara ɗari huɗu da talatin da huɗu (434), za mu sami shekara 483, wato (49+434=483).

  • Yaushe ne wannan lokacin ya ƙare? Idan muka ƙirga shekara 483, daga shekara ta 455 kafin haihuwar Yesu, zai kai mu shekara ta 29 bayan haihuwar Yesu (B.H.Y). a A shekarar ne Yesu ya yi baftisma kuma ya zama Almasihu!​—Luka 3:​1, 2, 21, 22.

Return to lesson 15 point 5

 3. Hanyoyin Jinya da Suka Shafi Batun Jini

Kiristoci ba sa amincewa da ƙarin jini kuma ba sa ba da jininsu don a yi wa wasu jinya da shi. Amma akwai hanyoyin jinya da ake amfani da jinin mutumin da shi. Alal misali, wasu mutane sukan ba da jininsu don a yi wa wasu jinya da shi. Ko kuma a ja jininsu a ajiye don a yi amfani da shi a lokacin da za a yi musu tiyata. Amma Kiristoci ba sa yin hakan.​—Maimaitawar Shari’a 15:23.

Akwai wasu hanyoyin jinya da Kiristoci za su iya amincewa da su. Waɗannan sun ƙunshi gwajin jini ko a sa jinin mutum ya bi wata na’ura inda mai yiwuwa a sa jinin ya daina gudu na wani lokaci ko a yi amfani da na’urar da ke tsabtace jini. Ko kuma a saka wa mutum na’urar da ke aiki a madadin zuciya ko huhu. Kowane Kirista ne zai zaɓi yadda za a yi amfani da jininsa sa’ad da ake masa tiyata ko sa’ad da ake masa gwaje-gwaje ko sa’ad da ake masa wata jinya. Likitoci suna iya yin wannan jinya ta hanyoyi dabam-dabam. Don haka, kafin ka amince da wata tiyata ko gwaji ko jinya, ka tabbata cewa ka san yadda likitan yake so ya yi amfani da jininka. Ka yi tunani a kan tambayoyin nan:

  • Idan aka janye jinina kuma aka adana shi na ɗan lokaci, shin zuciyata za ta amince na sake karɓan jinin maimakon a “zubar a ƙasa”?​—Maimaitawar Shari’a 12:​23, 24.

  • Shin zuciyata za ta dame ni idan na amince da wata irin jinya da za a janye jinina a tsabtace shi kuma a sake mayar da shi jikina. Ko zuciyata ba za ta dame ni ba idan na amince a min hakan?

Return to lesson 39 point 3

 4. Abubuwan da za su iya sa ma’aurata su rabu

Littafi Mai Tsarki ya ce kada mata da miji su rabu, kuma ya bayyana dalla-dalla cewa idan suka rabu, ba su da izini su sake yin wani aure. (1 Korintiyawa 7:​10, 11) Amma akwai wasu dalilai da za su iya sa wasu Kiristoci ma’aurata su rabu da juna. Ga wasu daga cikinsu.

  • Idan maigida ya ƙi kula da iyalinsa da gangan, wato ba ya ba su kuɗi ko abinci.​—1 Timoti 5:8.

  • Idan mijin yana cin zalin matarsa ko matar tana cin zalin mijinta kuma hakan ya sa ran mijin ko matar cikin haɗari.​—Galatiyawa 5:​19-21.

  • Idan mace tana hana mijinta ko mijin yana hana matarsa bauta wa Jehobah.​—Ayyukan Manzanni 5:29.

Return to lesson 42 point 3

 5. Ranakun Hutu da Bukukuwa

Kiristoci ba sa yin bukukuwa da Jehobah bai amince da su ba. Kowane Kirista ne zai yanke shawara game da abin da zai yi a lokacin da ake yin wasu bukukuwa. Ga wasu misalai.

  • A ce wani ya gaishe ka yadda suke yi sa’ad da ake wani biki. Idan wani ya ce maka, barka da Kirsimati ko barka da sabuwar shekara. Za ka iya ce masa “na gode.” Idan mutumin yana son ƙarin bayani, za ka iya bayyana masa dalilin da ya sa ba ka irin wannan bikin.

  • A ce mijinki ko matarka da ba Mashaidiya ba ta gayyace ka zuwa wata liyafa da iyalinta suka shirya a lokacin wani biki da Kiristoci ba sa yi. Za ka iya zuwa idan zuciyarka ba za ta dame ka ba, kuma za ka gaya wa matarka cewa idan za a yi wani abu a liyafar da ke da alaƙa da bautar ƙarya, ba za ka yi abin ba.

  • A ce wanda kake wa aiki ya ba ka kyautar kuɗi a lokacin wani biki. Za ka karɓi kuɗin? Wataƙila. Shin wanda kake wa aikin ya ba ka kyautar kuɗin don bikin da ake yi ne ko kuma don ya nuna godiyarsa don aikin da kake yi?

  • A ce wani ya ba ka kyauta a ranar wani biki. Wanda ya ba ka kyautar yana iya cewa: “Na san cewa ba ka yin bikin nan amma ina so in ba ka kyauta.” Wataƙila mutumin yana so ya yi maka alheri ne kawai. Amma kana ganin mutumin yana so ya jarraba ka ko kuma ya sa ka yi bikin ne da wayo? Bayan ka yi tunani a kan wannan, za ka iya zaɓa ka karɓi kyautar ko a’a. Muna so mu kasance da zuciya mai kyau da kuma aminci ga Jehobah sa’ad da muke yanke kowace irin shawara.​—Ayyukan Manzanni 23:1.

Return to lesson 44 point 1

 6. Cututtuka Masu Yaɗuwa

Muna ƙaunar mutane shi ya sa muke mai da hankali sosai don kada mu sa su kamu da cututtuka masu yaɗuwa. Muna mai da hankali sosai idan muna da wata cuta ko kuma muna ganin mun kamu da wata cuta da za mu iya yaɗawa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ka ƙaunaci kowa kamar kanka.”​—Romawa 13:​8-10.

Ta yaya mutum zai iya bin wannan umurnin? Ya kamata wanda ya kamu da cuta mai yaɗuwa ya guji shan hannu ko rungumar mutane ko yin sumba da dai sauransu. Bai kamata ya yi fushi ba idan wasu ba su gayyace shi zuwa gidansu ba domin suna so su kāre iyalinsu. Idan yana so ya yi baftisma, ya kamata ya gaya wa mai tsara ayyukan rukunin dattawa cewa yana da wata cuta. Yin hakan zai sa a shirya yadda za a yi masa baftisma a hanyar da ba za a yaɗa cutar ba. Zai dace duk waɗanda suka kamu da wata cuta su je su yi gwaje-gwaje kafin su yi alkawarin aure da wani ko wata. Yin hakan zai nuna cewa ba sa kula da kansu kaɗai, amma suna kula da waɗansu.​—Filibiyawa 2:4.

Return to lesson 56 point 2

 7. Kasuwanci da Dokokin Gwamnati

Za mu guji matsaloli da yawa idan muka rubuta yarjejeniyar kuɗi da kasuwanci da muka yi da wani har da ɗan’uwanmu Kirista. (Irmiya 32:​9-12) Har ila, Kiristoci suna iya samun saɓani da juna a kan batun kuɗi ko kuma wasu batutuwa. Ya kamata su kaɗai su sasanta irin waɗannan matsalolin ba tare da ɓata lokaci ba kuma su yi hakan cikin salama.

Amma ta yaya za mu sasanta matsaloli masu tsanani kamar zamba ko kuma tsegumi? (Karanta Matiyu 18:​15-17.) Yesu ya ba mu matakai uku da za mu ɗauka:

  1. Ku yi ƙoƙari ku sasanta matsalar tsakaninku.​—Ka duba aya ta 15.

  2.  

  3.  

Bai kamata mu kai ’yan’uwanmu kotu ba, don hakan zai ɓata sunan Jehobah da ikilisiya. (1 Korintiyawa 6:​1-8) Amma akwai wasu yanayoyi da kotu ce za ta iya sasanta matsalar, kamar: kashe aure ko riƙon yara ko ba mata kuɗi bayan an kashe auren ko matsalar inshora ko rashin biyan basusuka ko kuma tsai da shawara game da abin da wani mamaci ya rubuta. Duk Kirista da ya je kotu don ya sasanta irin waɗannan matsalolin bai taka dokar da ke Littafi Mai Tsarki ba.

Laifi mai tsanani kamar, fyaɗe ko ɓata yara ko kai wa mutum hari ko yin sata ko kisa kuma fa? Ba laifi ba ne idan Kirista ya kai ƙara wajen hukuma ba.

Return to lesson 56 point 3

a Idan muka ƙirga daga shekara ta 455 K.H.Y. zuwa shekara ta 1 K.H.Y., za mu sami shekaru 454. Daga shekara ta 1 K.H.Y. zuwa shekara ta 1 B.H.Y. shekara 1 ne. Daga shekara ta 1 B.H.Y. zuwa shekara ta 29 B.H.Y. shekaru 28 ne. Idan muka haɗa duka shekarun, za mu sami shekaru 483.