Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 08

Za Ka Iya Zama Aminin Jehobah

Za Ka Iya Zama Aminin Jehobah

Jehobah yana so ka san shi sosai. Me ya sa? Ya san cewa za ka so ka zama amininsa idan ka koya game da shi da halayensa da yadda yake sha’ani da mutane da kuma abubuwa da yake so ka yi. Za ka iya zama aminin Allah da gaske? (Karanta Zabura 25:14.) Mene ne za ka yi don ka zama amininsa? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshin waɗannan tambayoyin. Kuma ya bayyana abin da ya sa babu wani babban aminin da kake da shi da ya kai Jehobah.

1. Mene ne Jehobah ya ce ka yi?

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.” (Yakub 4:8) Mene ne hakan yake nufi? Jehobah yana so ka zama amininsa. Wasu suna ganin cewa zama aminin Jehobah zai yi wuya domin ba ma iya ganin sa. Duk da haka, Jehobah ya bayyana mana kome game da kansa a cikin Kalmarsa domin yana so mu kusace shi. Idan muka karanta Littafi Mai Tsarki, dangantakarmu da Jehobah za ta yi danƙo duk da cewa ba mu taɓa ganin sa ba.

2. Me ya sa babu Amini kamar Jehobah?

Babu wanda yake ƙaunar ka kamar Jehobah. Yana so ka riƙa farin ciki kuma ka yi addu’a sa’ad da kake bukatar taimako. Kana iya ‘danƙa masa dukan damuwarka, gama shi ne mai lura da kai.’ (1 Bitrus 5:7) A kowane lokaci, Jehobah yana a shirye ya taimaka wa aminansa, ya ƙarfafa su, kuma ya saurare su.​—Karanta Zabura 94:​18, 19.

3. Me Jehobah yake so aminansa su yi?

Jehobah yana ƙaunar dukan mutane, “amma yana amincewa da mai gaskiya a zuci.” (Karin Magana 3:32) Jehobah yana so aminansa su riƙa yin abubuwa masu kyau kuma su guji yin abubuwan da ba ya so. Wasu suna ganin cewa ba za su iya bin dokokin Allah ba. Amma Jehobah mai jin tausayi ne sosai. Jehobah yana amincewa da duk wanda yake ƙaunar sa kuma yake iya ƙoƙarinsa don ya faranta ran Jehobah.​—Zabura 147:11; Ayyukan Manzanni 10:​34, 35.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za ka iya zama aminin Jehobah da kuma dalilin da ya sa babu Amini kamarsa.

4. Ibrahim aminin Jehobah ne

Labarin Ibrahim a cikin Littafi Mai Tsarki ya sa mun fahimci abin da zama aminin Jehobah yake nufi. Ku karanta game da Ibrahim a littafin Farawa 12:​1-4. Sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Mene ne Jehobah ya gaya wa Ibrahim ya yi?

  • Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa Ibrahim?

  • Mene ne Ibrahim ya yi sa’ad da Jehobah ya ba shi umurni?

5. Abin da Jehobah yake so aminansa su yi

Mukan so abokanmu su yi mana wasu abubuwa.

  • Waɗanne abubuwa ne za ka so abokanka su yi maka?

Ku karanta 1 Yohanna 5:​3, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me Jehobah yake so aminansa su yi?

Don mu yi wa Jehobah biyayya, muna bukatar mu canja halayenmu. Ku karanta Ishaya 48:​17, 18, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa Jehobah yake gaya wa aminansa su yi canje-canje a salon rayuwarsu?

Abokin kirki zai gaya mana abin da zai amfane mu da kuma kāre mu. Abin da Jehobah yake wa aminansa ke nan

6. Abin da Jehobah yake yi don ya taimaka wa aminansa

Jehobah yana taimaka wa abokansa su jimre da matsaloli. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Ta yaya Jehobah ya taimaka wa matar da aka ambata a bidiyon ta daina yawan baƙin ciki?

Ku karanta Ishaya 41:​10, 13, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa dukan aminansa?

  • Kana ganin Jehobah amini ne na ƙwarai? Me ya sa ka ce hakan?

Abokai na kud da kud za su taimaka maka sa’ad da kake bukatar taimako. Jehobah ma zai taimaka maka

7. Don mu zama aminan Jehobah, muna bukatar mu riƙa tattaunawa da shi kuma mu saurare shi

Abokai suna kusantar juna idan suna tattaunawa a kai a kai. Ku karanta Zabura 86:​6, 11, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Ta yaya za mu iya tattaunawa da Jehobah?

  • Ta yaya Jehobah yake tattaunawa da mu?

Muna tattaunawa da Jehobah ta addu’a, shi kuma yana amfani da Littafi Mai Tsarki don ya tattauna da mu

WASU SUN CE: “Ba zai yiwu mu zama aminan Allah ba.”

  • Wane nassi ne za ka yi amfani da shi don ka nuna cewa za mu iya zama aminan Jehobah?

TAƘAITAWA

Jehobah yana so ya zama Amininka, kuma zai taimaka maka ka kusace shi.

Bita

  • Ta yaya Jehobah yake taimaka wa abokansa?

  • Me ya sa Jehobah yake gaya wa abokansa su canja salon rayuwarsu?

  • Kana ganin Jehobah yana bukatar abokansa su yi abin da ya fi ƙarfinsu ne? Me ya sa ka ce haka?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda zama aminin Allah yake da amfani.

“Jehobah Allah Ne da Ya Cancanci Mu San Shi” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Fabrairu, 2003)

Ku karanta talifin nan don ku ga dalilin da ya sa wata mata take ganin dangantakarta da Jehobah ya taimaka mata.

“A Dā Ina Tsoron Mutuwa!” (Hasumiyar Tsaro Na 1 2017)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da wasu matasa suka ce game da Jehobah.

Ta Yaya Mutum Zai Zama Aminin Allah? (1:46)