Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 10

Ta Yaya Za Ka Amfana Daga Taron Shaidun Jehobah?

Ta Yaya Za Ka Amfana Daga Taron Shaidun Jehobah?

An taɓa gayyatar ka zuwa taron Shaidun Jehobah? Idan wannan ne karo na farko da za ka halarci taron, wataƙila kana ɗan jin tsoro. Za ka iya yin tunani cewa: ‘Yaya ake gudanar da waɗannan taron? Me ya sa taron yake da muhimmanci? Me ya sa ya kamata in riƙa halarta?’ A wannan darasin, za ka koyi yadda halartan taron Shaidun Jehobah zai sa ka kusaci Jehobah da kuma yadda zai taimaka maka a rayuwa.

1. Me ya sa Shaidun Jehobah suke yin taro?

Ka lura da yadda wani marubucin Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalili mafi muhimmanci na halartan taro. Ya ce: “A cikin babban taron jama’a zan yabi” Jehobah. (Zabura 26:12) Hakazalika, halartan taro yana sa Shaidun Jehobah farin ciki. A dukan faɗin duniya, suna halartan taro kowane mako don su bauta wa Allah, su rera waƙa kuma su yi addu’a. Suna kuma halartan manyan taro sau uku a kowace shekara.

2. Me za ka koya a taronmu?

A taronmu, muna tattauna Kalmar Allah, kuma muna ‘bayyana ma’anarta dalla-dalla.’ (Karanta Nehemiya 8:8.) Idan ka halarci taronmu, za ka koyi abubuwa da dama game da Jehobah da kuma halayensa. Yayin da kake ƙara sanin yadda yake ƙaunar ka, za ka kusace shi. Za ka kuma koyi yadda zai taimaka maka ka yi rayuwa mai gamsarwa.​—Ishaya 48:​17, 18.

3. Ta yaya za ka amfana daga yin ma’amala da mutane a taronmu?

Jehobah ya umurce mu mu riƙa “lura da juna ta yadda za mu iza juna ga nuna ƙauna da yin aikin nagarta. Kada mu bar yin taron sujada.” (Ibraniyawa 10:​24, 25) A taronmu, za ka haɗu da mutanen da suka damu da juna, kuma suke so su koyi abubuwa game da Allah kamar yadda kake so. Za ka ji suna yin kalami don su ƙarfafa juna a lokacin taron da kuma bayan taron. (Karanta Romawa 1:​11, 12.) Ƙari ga haka, za ka san mutanen da suke farin ciki duk da matsalolin da suke fuskanta. Waɗannan ne wasu daga cikin dalilan da suka sa Jehobah yake so mu riƙa yin taro a kai a kai!

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi abin da Shaidun Jehobah suke yi a taronsu da kuma abin da ya sa halartar wannan taron zai amfane mu.

4. Taron Shaidun Jehobah

A ƙarni na farko, Kiristoci suna yin taro a kai a kai don su bauta wa Jehobah. (Romawa 16:​3-5) Ku karanta Kolosiyawa 3:​16, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya Kiristoci a ƙarni na farko suka bauta wa Jehobah?

A yau, Shaidun Jehobah suna yin taro a kai a kai don su bauta wa Allah. Don ka ga yadda suke yin taron, ku kalli BIDIYON nan. Bayan haka, ku kalli hoton nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A ganinka, ta yaya abin da ake yi a Majami’ar Mulki ya jitu da abin da ke Kolosiyawa 3:16?

  • A bidiyon ko kuma a hoton, ka lura da wani abu da ake yi a taron da ya burge ka?

Ku karanta 2 Korintiyawa 9:​7, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa Shaidun Jehobah ba sa karɓan baiko a taronsu?

Kai da mai nazari da kai ku duba abin da za a tattauna a taro na gaba.

  • Wane sashen taron ne kake ganin za ka fi jin daɗinsa?

Ka sani?

A dandalin jw.org, za ka iya samun wuri da kuma lokacin da ake taro a faɗin duniya.

  1. A taronmu, ana yin jawabai, ana kallon bidiyoyi, kuma ana koya wa mutane yin wa’azi. Ana soma taron da waƙa da addu’a kuma a kammala da waƙa da addu’a

  2. A taron ana ba masu sauraro damar amsa tambayoyi

  3. Kowa yana iya halartan taron

  4. Ba a karɓan baiko a taron. Ba a biyan kuɗin shiga kuma ba a zagayawa da faranti

5. Kana bukatar ka yi wasu sadaukarwa don ka halarci taro

Ka yi la’akari da abin da Yesu da iyayensa da kuma ’yan’uwansa suka yi. A kowace shekara, suna yin tafiya wajen kwana uku da kafa a hanyar da akwai tudu da gangare sosai don su je Urushalima daga Nazarat su halarci wani taron da ake yi sau ɗaya a shekara. Ku karanta Luka 2:​39-42, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kana ganin sun yi sadaukarwa don su yi wannan tafiyar?

  • Me ya sa kake bukatar ka ƙoƙarta sosai don ka halarci taro?

  • Kana ganin zai dace ka halarci taro, ko da yin hakan yana da wuya? Me ya sa?

Littafi Mai Tsarki ya ce halartan taro yana da muhimmanci sosai. Ku karanta Ibraniyawa 10:​24, 25, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa ya kamata mu riƙa halartan taro a kai a kai?

WASU SUN CE: “Ba ka bukatar ka halarci taro. Za ka iya karanta Littafi Mai Tsarki a gidanka kawai!”

  • Wane nassi ko kuma misali a Littafi Mai Tsarki ne ya nuna abin da Jehobah yake so?

TAƘAITAWA

Halartan taro zai taimaka maka ka koyi abubuwa da yawa game da Jehobah, ka ƙarfafa dangantakarka da shi kuma ka bauta masa tare da bayinsa.

Bita

  • Me ya sa Jehobah yake ƙarfafa mu mu yi taro?

  • Mene ne za ka koya a taron Shaidun Jehobah?

  • Kana ganin halartan taro zai taimaka maka?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Idan kana jin tsoron halartan taro fa? Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wani mutum ya ji sa’ad da ya halarci taro da farko da kuma yadda ya so taron daga baya.

Ba Za Mu Taɓa Manta da Gaisuwar Ba (4:16)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wani matashi ya ji daɗin taro da kuma abin da ya yi don ya ci gaba da halarta.

Na Ji Daɗin Taronsu Sosai! (4:33)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda wasu da suka halarci taronmu suka ji.

“Me Ya Sa Kake Bukatar Ka Riƙa Halartar Taro a Majami’ar Mulki?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda wani babban ɓarawo ya canja rayuwarsa bayan ya halarci taron Shaidun Jehobah.

“Ba Inda Nake Zuwa Ba Tare da Bindiga Ba” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Yuli, 2014)