Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 15

Wane ne Yesu?

Wane ne Yesu?

Kusan dukan mutane sun taɓa ji game da Yesu, amma ba dukansu ba ne suka san shi sosai ba. Kuma mutane da yawa suna da ra’ayi dabam-dabam game da Yesu. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da shi?

1. Wane ne Yesu?

Yesu ruhu ne mai iko sosai a sama. Jehobah ya halicce shi kafin ya halicci sauran abubuwa. Shi ya sa ake kiran Yesu “Ɗan fari gaban dukan halitta.” (Kolosiyawa 1:15) Littafi Mai Tsarki ya ce Yesu shi ne “makaɗaicin Ɗan” Allah, a domin Jehobah ne ya halicce shi da kansa. (Yohanna 3:16) Yesu ne ya taimaka wa Jehobah ya halicci sauran abubuwa. (Karanta Karin Magana 8:30.) Yesu ya ci gaba da kasancewa da dangantaka na kud da kud da Jehobah. An kira Yesu “Kalman nan” domin yana magana a madadin Allah, yana idar da saƙonni da kuma umurnai daga wurin Allah.​—Yohanna 1:14.

2. Me ya sa Yesu ya zo duniya?

A wajen shekaru 2,000 da suka shige, ta hanyar mu’ujiza, Jehobah ya mayar da ran Yesu daga sama zuwa mahaifar wata budurwa mai suna Maryamu. Ta hakan ne aka haifi Yesu a matsayin mutum. b (Karanta Luka 1:​34, 35.) Yesu ya zo duniya a matsayin Almasihu ko Kristi yadda aka yi alkawari, don ya ceci ’yan Adam. Yesu ya cika dukan annabcin da aka yi a cikin Littafi Mai Tsarki game da Almasihu. Hakan ya taimaka wa mutane su san cewa Yesu ne “Almasihu, Ɗan Allah mai rai.”​—Matiyu 16:16.

3. A ina ne Yesu yake yanzu?

Bayan Yesu ya mutu, Allah ya ta da shi kuma ya koma sama ya zama ruhu. Sa’an nan “Allah ya ɗaukaka shi fiye da kome.” (Filibiyawa 2:9) Yanzu Yesu mala’ika ne mai iko sosai, Jehobah ne kaɗai ya fi shi iko.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi gaskiya game da Yesu da kuma abin da ya sa yake da muhimmanci mu koyi abubuwa game da shi.

4. Yesu ba shi ne Allah Mafi Iko Duka ba

Littafi Mai Tsarki ya ce duk da cewa Yesu mala’ika ne mai iko sosai a sama, yana biyayya ga Jehobah, Allahnsa. Me ya sa aka ce haka? Ku kalli BIDIYON nan don ku ga abin da Littafi Mai Tsarki ya koyar game da bambanci da ke tsakanin Yesu da Allah mafi iko duka.

Nassosi da ke gaba za su taimaka mana mu fahimci dangantakar da ke tsakanin Jehobah da Yesu. Ku karanta kowane nassi, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

Ku karanta Luka 1:30-32.

  • Yaya wani mala’ika ya kwatanta dangantakar da ke tsakanin Yesu da Jehobah, Allah “Mafi Ɗaukaka”?

Ku karanta Matiyu 3:​16, 17.

  • Sa’ad da Yesu ya yi baftisma, me aka ji wata murya daga sama ta ce?

  • Wane ne mai muryar?

Ku karanta Yohanna 14:28.

  • Wane ne ya fi girma da iko? Uba ko kuma ɗa?

  • Yesu ya kira Jehobah Ubansa, me hakan ya koya mana?

Ku karanta Yohanna 12:49.

  • Shin Yesu yana ganin cewa shi da Ubansa ɗaya ne? Mene ne ra’ayinka?

5. Mene ne ya nuna cewa Yesu ne Almasihu?

Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da annabce-annabce da yawa da za su taimaka wa mutane su san Almasihu. Shi ne Allah ya zaɓa ya ceci ’yan Adam. Ku kalli BIDIYON nan don ku koya game da wasu annabce-annabce da Yesu ya cika sa’ad da ya zo duniya.

Ku karanta waɗannan annabce-annabcen, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba:

Ku karanta Mika 5:2 don ku san wurin da aka ce za a haifi Almasihu. c

  • A wurin da aka ce za a haifi Yesu ne aka haife shi?​—Matiyu 2:1.

Ku karanta Zabura 34:20 da Zakariya 12:10 don ku koyi annabcin da aka yi game da mutuwar Almasihu.

  • Waɗannan annabcin sun cika kuwa?​—Yohanna 19:​33-37.

  • Kana ganin Yesu ne ya sa waɗannan annabcin su cika?

  • Mene ne wannan ya nuna maka game da Yesu?

6. Za mu amfana idan muka koya game da Yesu

Littafi Mai Tsarki ya ce yana da muhimmanci mu koya game da Yesu. Ku karanta Yohanna 14:6 da 17:3, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa yake da muhimmanci mu koya game da Yesu?

Yesu ne ya buɗe mana hanyar zama aminan Allah. Ya koya mana gaskiya game da Jehobah, kuma ta wurin sa ne za mu sami rai na har abada

WASU SUN CE: “Shaidun Jehobah ba su yi imani da Yesu ba.”

  • Me za ka ce?

TAƘAITAWA

Yesu ruhu ne mai iko sosai. Shi Ɗan Allah ne da kuma Almasihu.

Bita

  • Me ya sa aka kira Yesu “ɗan fari gaban dukan halitta”?

  • Mene ne Yesu ya yi kafin ya zo duniya?

  • Ta yaya muka san cewa Yesu ne Almasihu?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ƙara koya game da yadda za mu san cewa Yesu ne Almasihu.

“Annabce-annabce Game da Almasihu Sun Nuna Cewa Yesu Ne Almasihu Kuwa?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga ko Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa Allah mahaifin Yesu ne kamar yadda ’yan Adam suke haifan yara.

“Me Ya Sa Aka Kira Yesu Dan Allah?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga ko akwai koyarwar Allah-Uku-Cikin-Ɗaya a Littafi Mai Tsarki.

“Yesu Shi ne Allah?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Afrilu, 2009)

Ku karanta talifin nan don ku ga yadda rayuwar wata mata ta canja bayan ta yi bincike a kan abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da Yesu.

“Wata Bayahudiya Ta Bayyana Abin da Ya Sa Ta Sake Bincika Imaninta” (Awake!, Mayu 2013)

a Littafi Mai Tsarki bai koyar cewa Allah yana da ɗa yadda ’yan Adam suke haifan yara ba.

b A darasi na 26 da 27, za mu tattauna abin da ya sa ’yan Adam suke bukatar ceto da kuma yadda Yesu ya cece mu.

c Ka duba Ƙarin Bayani na 2 don ka ga annabcin da aka yi game da lokacin da Yesu zai bayyana a duniya.