DARASI NA 20
Yadda Aka Tsara Ikilisiya
Jehobah Allah ne mai tsara abubuwa da kyau. (1 Korintiyawa 14:33, 40) Saboda haka, ya kamata masu bauta masa ma su riƙa tsara abubuwa da kyau. Yaya ake gudanar da ayyuka a ikilisiya? Me za mu yi don a riƙa yin kome yadda ya kamata?
1. Wane ne shugaban ikilisiya?
“Almasihu [ne] shugaban ikilisiya.” (Afisawa 5:23, Littafi Mai Tsarki) Daga sama ne yake ja-gorancin ayyukan Shaidun Jehobah a faɗin duniya. Yesu ne ya naɗa “bawan nan mai aminci, mai hikima” wato, Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah. (Karanta Matiyu 24:45-47.) Kamar manzanni da kuma dattawan da ke ƙarni na farko a Urushalima, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne suke ja-goranci a dukan ikilisiyoyi a duniya. (Ayyukan Manzanni 15:2) Amma su ba shugabanni ba ne a ƙungiyar Jehobah. Suna karanta Littafi Mai Tsarki don su fahimci abin da Jehobah yake so su yi, kuma suna bin umurnin Yesu.
2. Su waye ne dattawa kuma wane aiki ne suke yi?
Dattawa maza ne da suka ƙware kuma suna koya wa mutanen Jehobah Littafi Mai Tsarki da taimaka musu da kuma ƙarfafa su. Ba a biyan su kuɗi don aikin da suke yi. A maimakon haka, suna ‘yin shi da yardar ransu yadda Allah yake so,’ ba don suna neman ribar banza ba, amma don suna da niyyar yin hidima. (1 Bitrus 5:1, 2) Bayi masu hidima maza ne da suke taimaka wa dattawa a ikilisiya. Da shigewar lokaci, su ma za su zama dattawa idan suka cancanci hakan.
Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ne suke zaɓan wasu dattawa don su zama masu kula da da’ira. Suna ziyartar ikilisiyoyi dabam-dabam don su ja-goranci ’yan’uwa da kuma ƙarfafa su. Masu kula da da’ira suna bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki don su ga ko wani ɗan’uwa ya cancanci zama bawa mai hidima ko dattijo.—1 Timoti 3:1-10, 12; Titus 1:5-9.
3. Mene ne aikin kowannenmu a ikilisiya?
Dukan ’yan’uwa a ikilisiya suna yabon “sunan Yahweh” ta yin kalami da jawabai, da rera waƙa da kuma yin wa’azi daidai gwargwadon ƙarfinsu.—Karanta Zabura 148:12, 13.
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu san ko wane irin shugaba ne Yesu, da yadda dattawa suke bin misalinsa, da kuma yadda za mu bi umurnin Yesu kuma mu goyi bayan dattawa.
4. Yesu shugaban kirki ne
Yesu ya ƙarfafa mu mu nemi taimakonsa. Ku karanta Matiyu 11:28-30, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Yaya Yesu yake so mu ji game da shugabancinsa?
Ta yaya dattawa suke yin koyi da misalin Yesu? Ku kalli BIDIYON nan.
Littafi Mai Tsarki ya nuna yadda ya kamata dattawa su yi aikinsu.
Ku karanta Ishaya 32:2 da 1 Bitrus 5:1-3, sai ku tattauna tambayoyin nan:
-
Yaya kake ji don yadda dattawa suke bin misalin Yesu wajen ƙarfafa mutane?
-
A waɗanne hanyoyi ne kuma dattawa suke bin misalin Yesu?
5. Dattawa suna koyar da mu ta wurin halayensu masu kyau
Yaya Yesu yake so dattawa su riƙa ɗaukan aikinsu? Ku kalli BIDIYON nan.
Yesu ne ya kafa ƙa’idodin da masu ja-goranci a ikilisiya suke bi. Ku karanta Matiyu 23:8-12, sai ku tattauna tambayoyin nan:
-
Waɗanne ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki ne dattawa suke bi? Kana ganin malaman addinai suna bin abin da Littafi Mai Tsarki ya ce kuwa?
-
Dattawa suna ƙarfafa dangantakarsu da Jehobah kuma suna taimaka wa iyalansu su yi hakan
-
Dattawa suna kula da ’yan’uwan da ke ikilisiyarsu
-
Dattawa suna wa’azi kowane lokaci
-
Dattawa suna koyar da ’yan’uwa a ikilisiya. Suna yin shara da kuma wasu ayyuka
6. Za mu iya bin ja-gorancin dattawa
A cikin Littafi Mai Tsarki an ambata dalili mai muhimmanci da zai sa mu bi abin da dattawa suka ce. Ku karanta Ibraniyawa 13:17, sai ku tattauna tambayoyin nan:
-
Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa biyayya ga waɗanda suke mana ja-goranci? Yaya kake ji game da hakan?
Ku karanta Luka 16:10, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Me ya sa za mu yi abin da dattawa suka ce har a abubuwan da muke ganin ba su da muhimmanci sosai?
WASU SUN CE: “Za mu iya bauta wa Allah yadda muka ga dama.”
-
Me ya sa kake ganin ya dace mutum ya riƙa bauta wa Allah tare da ’yan’uwa a ikilisiya?
TAƘAITAWA
Yesu ne shugaban ikilisiya. Muna jin daɗin yin biyayya ga dattawa don Yesu ne shugabansu, suna ƙarfafa mu kuma za mu iya yin koyi da halayensu masu kyau.
Bita
-
Wane ne shugaban ikilisiya?
-
Ta yaya dattawa suke taimakawa a ikilisiya?
-
Mene ne aikin kowanne bawan Jehobah a ikilisiya?
KA BINCIKA
Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu da dattawa suka damu da ’yan’uwa a yau.
Ku kalli bidiyon nan don ku ga irin hidimar da masu kula da da’ira suke yi.
Ku karanta talifin nan don ku koyi game da hidimar da mata suke yi a ikilisiya.
“Shaidun Jehobah Suna Barin Mata Su Koyar da Mutane Ne?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Oktoba, 2012)
Ku karanta talifin nan don ku ga yadda dattawa suke aiki tuƙuru don su ƙarfafa ’yan’uwansu.
“Dattawa Kirista Suna Aiki Don Mu Yi ‘Farin Ciki’” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Janairu, 2013)