DARASI NA 22
Ta Yaya Za Ka Soma Yin Wa’azi?
Yayin da kake koyan gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, za ka iya ce, ‘Ya kamata kowa ya san abin da nake koya!’ Babu shakka, ya kamata kowa ya ji. Amma, wataƙila kana jin tsoron gaya wa mutane abubuwan da kake koya. Bari mu tattauna yadda za ka daina jin tsoro kuma ka soma yin wa’azi.
1. Ta yaya za ka soma yi wa mutanen da ka sani wa’azi?
Almajiran Yesu sun ce: “Ba za mu iya yin shiru a kan abin da muka ji, muka kuma gani ba.” (Ayyukan Manzanni 4:20) Sun so gaskiyar da ke Kalmar Allah sosai har sun so su gaya wa kowa game da ita. Haka kai ma kake ji? Idan haka ne, ka nemi zarafin gaya wa ’yan gidanku da abokanka abubuwan da kake koya.—Karanta Kolosiyawa 4:6.
Yadda za ka soma wa’azi
-
Sa’ad da kake tattaunawa da wani danginka, za ka iya soma gaya masa cewa: “Na koyi wani abu mai muhimmanci a wannan makon.”
-
Ka karanta wa abokinka da yake cikin damuwa ko rashin lafiya wani nassi mai ban ƙarfafa.
-
Idan abokan aikinka suka tambaye ka ‘yaya al’amura?’ Kana iya gaya musu abin da ka koya sa’ad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki ko kuma taron ikilisiya.
-
Ka nuna wa abokanka dandalin jw.org/ha.
-
Ka gaya wa abokanka su zo su ga yadda ake nazari da kai ko kuma ka nuna musu yadda za su tura saƙo a dandalin jw.org/ha don a yi nazari da su.
2. Me ya sa yin wa’azi da ikilisiya ya dace?
Ba mutanen da almajiran Yesu suka sani kaɗai ne suka yi ma wa’azi ba. Yesu “ya aike su biyu-biyu su yi gaba zuwa garuruwa” don su yi wa’azi. (Luka 10:1) Yadda Yesu ya tsara wa’azin nan ya ba mutane da yawa damar jin bishara. Almajiran sun yi farin ciki sosai da suka yi wa’azi tare. (Luka 10:17) Za ka so ka soma fita yin wa’azi tare da ’yan’uwa a ikilisiya?
KA YI BINCIKE SOSAI
Za mu koyi abin da zai sa ka rage jin tsoro kuma ka yi farin cikin yi wa mutane wa’azi.
3. Jehobah zai kasance tare da kai
Wasu suna yin jinkiri don suna tunanin yadda mutane za su ɗauke su ko kuma abin da za su faɗa idan sun gan su suna wa’azi.
-
Kana jin tsoron gaya wa mutane abin da kake koya? Me ya sa kake jin tsoro, ko kuma me ya sa ba ka jin tsoro?
Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.
-
Ta yaya waɗannan matasa suka daina jin tsoro?
Ku karanta Ishaya 41:10, sai ku tattauna tambayar nan:
-
Me ya sa ya kamata ka yi addu’a idan kana jin tsoron yin wa’azi?
Ka sani?
Shaidun Jehobah da yawa a dā suna ganin ba za su taɓa samun ƙarfin zuciyar yin wa’azi ba. Alal misali, wani mai suna Sergey yana ganin ba shi da daraja, kuma yana yi masa wuya ya yi magana da mutane. Amma, da ya fara nazarin Littafi Mai Tsarki, sai ya ce: “A dā, ina jin tsoron soma yi wa mutane magana game da abin da nake koya. Amma na yi mamaki da na ga cewa yi wa mutane wa’azi ya sa na kasance da ƙarfin zuciya. Kuma gaya wa mutane game da imanina ya ƙarfafa bangaskiyata.”
4. Ka riƙa daraja mutane
Kafin ka yi wa mutane wa’azi, ka yi tunanin abin da za ka faɗa da yadda za ka faɗe shi. Ku karanta 2 Timoti 2:24 da 1 Bitrus 3:15, sai ku tattauna tambayoyin nan:
-
Ta yaya za ka yi amfani da waɗannan ayoyin sa’ad da kake wa’azi?
-
Wasu cikin danginka ko abokanka ba za su yarda da abin da kake gaya musu ba. Me za ka yi? Mene ne bai kamata ka yi ba?
-
Me ya sa zai fi kyau ka yi tambayoyi cikin basira maimakon ka yi ƙoƙarin cusa musu ra’ayinka?
5. Yin wa’azi yana sa mu farin ciki
Jehobah ne ya umurci Yesu ya yi wa’azi. Ta yaya Yesu ya ɗauki aikin nan? Ku karanta Yohanna 4:34, sai ku tattauna tambayoyin nan:
-
Cin abinci mai kyau zai sa mu ci gaba da rayuwa kuma mu yi farin ciki. Me ya sa Yesu ya ce yin nufin Allah, har da yin wa’azi yana kama da cin abinci?
-
Waɗanne albarku ne za ka samu idan kana yin wa’azi?
Abubuwan da za su taimaka
-
Sa’ad da ka halarci taron tsakiyar mako, ka nemi abubuwan da za su taimaka maka ka soma tattaunawa da mutane.
-
Ka tambayi malaminka abin da za ka iya yi don ka cancanci yin aiki a taron tsakiyar mako. Yin hakan zai taimaka maka ka yi shirin yin wa’azi.
-
Ka yi amfani da sashen nan “Wasu Sun Ce” ko “Wani Yana Iya Cewa” da ke wannan littafin don ka shirya yadda za ka amsa tambayoyin da aka saba yi a yankinku.
WANI YANA IYA CEWA: “Yaya al’amura?”
-
Ta yaya za ka yi amfani da wannan damar don ka gaya wa mutumin abin da ka koya sa’ad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki?
TAƘAITAWA
Yi wa mutane wa’azi yana sa mu farin ciki, kuma somawa yana da sauƙi fiye da yadda kake tsammani.
Bita
-
Me ya sa ya dace ka yi wa mutane wa’azi?
-
Ta yaya za ka daraja mutane da kake musu wa’azi?
-
Ta yaya za ka daina jin tsoron yin wa’azi?
KA BINCIKA
Ku kalli bidiyon nan don ku ga hanyoyi biyu masu sauƙi da za ku iya yin amfani da katin jw.org a wa’azi.
Ku karanta talifin nan don ku ga halaye huɗu da za su taimaka wa mutum ya riƙa yin wa’azi.
“Kana a Shirye Ka Sa Mutane Su Soma Bauta wa Jehobah?” (Hasumiyar Tsaro, Satumba 2020)
Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wani labari da ke Littafi Mai Tsarki zai iya taimaka mana mu kasance da ƙarfin zuciyar yin wa’azi, ko da mu yara ne.
Ku karanta talifin nan don ku ga yadda za mu iya yi wa danginmu wa’azi.
“Yadda Za Mu Iya Ratsa Zukatan Danginmu da Ba Shaidu Ba” (Hasumiyar Tsaro, 15 ga Maris, 2014)