Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 25

Me Ya Sa Allah Ya Halicce Mu?

Me Ya Sa Allah Ya Halicce Mu?

Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa kwanakin ’yan Adam “kaɗan ne, cike kuma da wahala.” (Ayuba 14:1) Shin irin rayuwa da Allah yake so mu yi ke nan? Idan ba haka ba, me ya sa ya halicce mu? Zai taɓa cika nufinsa kuwa? Littafi Mai Tsarki ya ba da amsar waɗannan tambayoyin.

1. Wane irin rayuwa ne Jehobah yake so mu yi?

Jehobah yana so mu ji daɗin rayuwa. Sa’ad da ya halicce Adamu da Hauwa’u, ya saka su cikin aljanna, wato lambun Adnin. Sai “Allah ya sa musu albarka ya ce, ‘Ku yi ta haifuwa sosai ku yalwata, ku ciccika duniya ku kuma sha ƙarfinta.’ ” (Farawa 1:28) Jehobah yana so su haifi yara, su sa dukan duniya ta zama aljanna kuma su kula da dabbobi. Jehobah yana so dukan mutane su kasance da ƙoshin lafiya kuma su yi rayuwa har abada.

Ko da yake nufin Allah bai cika ba, a har ila Allah yana so mu yi irin wannan rayuwar. (Ishaya 46:​10, 11) Allah yana so mutane su yi rayuwa har abada a yanayi mai kyau.​​—Karanta Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:​3, 4.

2. Ta yaya za mu ji daɗin rayuwa a yanzu?

Jehobah ya halicce mu da marmarin son ya yi mana ja-goranci. Shi ya sa muke so mu san shi da kuma bauta masa. (Karanta Matiyu 4:4; 5:​3-6.) Yana so mu yi abota da shi, mu ‘yi tafiya cikin hanyarsa, mu ƙaunace shi,’ kuma mu bauta masa ‘da dukan zuciyarmu.’ (Maimaitawar Shari’a 10:12; Zabura 25:14) Idan muka yi hakan, za mu yi farin ciki ko da muna fuskantar matsaloli. Bauta wa Jehobah za ta sa rayuwarmu ta kasance da ma’ana.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda Jehobah ya nuna ƙauna sosai sa’ad da yake halittar duniya da kuma dalilin da ya sa ya halicce mu.

3. Jehobah yana so mutane su ji daɗin rayuwa

Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Me ya sa Allah ya halicci duniya?

Ku karanta Mai-Wa’azi 3:​11, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Kamar yadda ayar nan ta nuna, mene ne nufin Jehobah a gare mu?

4. Dalilin da ya sa Jehobah ya halicci duniya bai canja ba

Ku karanta Zabura 37:​11, 29 da Ishaya 55:​11, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya muka san cewa dalilin da ya sa Jehobah ya halicci duniya bai canja ba?

5. Bauta wa Jehobah yana sa mu yi rayuwa mai ma’ana

Za mu riƙa farin ciki a rayuwa idan muka san dalilin da ya sa aka halicce mu. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Ta yaya Terumi ta amfana bayan da ta gane dalilin da ya sa aka halicce mu?

Ku karanta Mai-Wa’azi 12:​13, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya za mu nuna godiya ga Jehobah don abubuwan da ya yi mana?

WANI YANA IYA CEWA: “Me zai iya sa mutum farin ciki da gamsuwa?”

  • Me za ka ce masa?

TAƘAITAWA

Jehobah yana so mu ji daɗin rayuwa a duniya har abada. Idan muka bauta masa da dukan zuciyarmu, rayuwarmu za ta kasance da ma’ana ko a yanzu ma.

Bita

  • Wane irin rayuwa ne Jehobah ya so Adamu da Hauwa’u su yi?

  • Ta yaya muka san cewa dalilin da ya sa Allah ya halicce mu bai canja ba?

  • Ta yaya za ka iya yin rayuwa mai ma’ana?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya tabbatar da cewa akwai wurin da aka taɓa kira lambun Adnin.

“Labarin Lambun Adnin Gaskiya ne ko Tatsuniya Ce?” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Janairu, 2011, English)

Ku karanta talifin nan don ku koyi abin da ya sa muka tabbata cewa duniya za ta kasance har abada.

“Za A Hallaka Duniyar Nan Ne?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku fahimci abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da yadda za ka yi rayuwa mai ma’ana.

“Rayuwa Tana da Ma’ana Kuwa?” (Talifin jw.org)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga yadda wani mutum da ya ɗauka cewa ba abin da ya rasa a rayuwa ya gano abin da bai da shi.

Yanzu Ne Nake Jin Daɗin Rayuwa (3:55)

a A darasi na gaba, za mu koyi abin da ya sa ba ma irin wannan rayuwar a yanzu.