Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 37

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Aiki da Kudi

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Aiki da Kudi

Batun aiki ko kuɗi ya taɓa sa ka damuwa? Yakan yi wuya mu biya bukatunmu kuma mu bauta wa Jehobah yadda ya kamata. Akwai shawarwari da za su taimaka mana a Littafi Mai Tsarki.

1. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce game da aiki?

Allah yana so mu ji daɗin aikinmu. Littafi Mai Tsarki ya ce, “babu abin da ya fi kyau ga ’yan Adam fiye da su . . . ji daɗin aikinsu.” (Mai-Wa’azi 2:24) Jehobah yana aiki tuƙuru. Idan mun yi koyi da shi, za mu faranta masa rai kuma za mu yi farin ciki.

Yin aiki yana da muhimmanci. Amma, bai kamata mu bar shi ya fi ibadarmu ga Jehobah muhimmanci ba. (Yohanna 6:27) Jehobah ya yi alkawari cewa idan mun sa ibadarmu a kan gaba, zai biya bukatunmu.

2. Ta yaya za mu kasance da ra’ayin da ya dace game da kuɗi?

Ko da yake Littafi Mai Tsarki ya ce kuɗi yakan kāre mutum, amma ya yi gargaɗi cewa ba kuɗi ba ne kawai zai sa mu farin ciki ba. (Mai-Wa’azi 7:12) Saboda haka, an ƙarfafa mu kada mu so kuɗi, amma mu “gamsu da abin da muke da shi.” (Karanta Ibraniyawa 13:5.) Idan muna gamsuwa da abin da muke da shi, za mu guji baƙin ciki da ke tattare da neman kuɗi ido rufe. Kuma za mu guji cin bashi da bai kamata mu ci ba. (Karin Magana 22:7) Ban da haka, za mu guji yin caca da kuma neman yin arziki dare ɗaya.

3. Ta yaya za mu zama masu bayarwa hannu sake?

Jehobah Allah ne mai bayarwa hannu sake kuma muna koyi da shi sa’ad da muke “taimakon waɗansu.” (1 Timoti 6:18) Za mu nuna mu masu bayarwa ne idan muna ba da gudummawa a ikilisiya kuma muna taimaka wa waɗanda suke da bukata, musamman ’yan’uwanmu. Jehobah ba ya mai da hankali ga yawan kyautar da muke bayarwa, amma dalilin da ya sa muke yin hakan. Idan muna bayarwa da zuciya ɗaya, za mu yi farin ciki kuma za mu faranta ran Jehobah.​—Karanta Ayyukan Manzanni 20:35.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu ga amfanin kasancewa da ra’ayin da ya dace game da aiki da kuma yadda za mu gamsu da abin da muke da shi.

4. Ka daraja Jehobah ta yadda kake aiki

Ya kamata dangantakarmu da Jehobah ta shafi ra’ayinmu game da aiki. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A bidiyon, mene ne ya burge ka game da halin Jason a wurin aikinsa?

  • Mene ne ya yi don ya kasance da ra’ayin da ya dace game da aiki?

Ku karanta Kolosiyawa 3:​23, 24, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa halinmu game da aiki yake da muhimmanci?

Yin aiki yana da muhimmanci, amma bai kamata mu bar shi ya fi ibadarmu ga Jehobah muhimmanci ba

5. Muna amfana idan mun gamsu da abin da muke da shi

Mutane da yawa suna iya ƙoƙarinsu su tara dukiya sosai. Amma Littafi Mai Tsarki ya ba mu wata shawara dabam. Ku karanta 1 Timoti 6:​6-8, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu yi?

Za mu iya farin ciki ko da mu talakawa ne. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Ko da yake su talakawa ne, me ya sa waɗannan iyalan suke farin ciki?

Idan mu masu arziki ne kuma muna neman ƙarin abin duniya fa? Yesu ya ba da labarin da ya nuna cewa hakan bai da kyau. Ku karanta Luka 12:​15-21, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ka koya daga labarin da Yesu ya bayar?​—Ka duba aya ta 15.

Ku karanta Karin Magana 10:22 da 1 Timoti 6:10. Sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Wanne ne kake ganin ya fi muhimmanci? Kasancewa da dangantaka da Jehobah ko yin arziki sosai? Me ya sa?

  • Wace matsala ce za ka fuskanta idan kana neman kuɗi ido rufe?

6. Jehobah zai biya bukatunmu

A lokacin da ba mu da aiki ko muna fama da rashin kuɗi ne za mu san ko mun dogara ga Jehobah ko a’a. Ku kalli BIDIYON nan don ku ga yadda za mu iya jimre irin waɗannan matsalolin, sai ku tattauna tambayoyin da ke gaba.

  • A bidiyon, waɗanne matsaloli ne ɗan’uwan ya fuskanta?

  • Mene ne ya yi da ya taimaka masa?

Ku karanta Matiyu 6:​25-​34, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Wane alkawari ne Jehobah ya yi wa mutane da suka sa bautarsa a kan gaba a rayuwarsu?

WASU SUN CE: “Ba zan iya zuwa taron ikilisiya kowane mako ba domin ina bukatar yin aiki sosai don in biya bukatun iyalina.”

  • Wane nassi ne ya tabbatar maka da cewa saka bautar Jehobah a kan gaba ne ya fi kyau?

TAƘAITAWA

Muna bukatar yin aiki da kuma samun kuɗi, amma bai kamata mu bar hakan ya hana mu bauta wa Jehobah ba.

Bita

  • Me zai taimaka maka ka kasance da ra’ayin da ya dace game da aiki?

  • Ta yaya za ka amfana idan ka gamsu da abin da kake da shi?

  • Ta yaya za ka nuna ka gaskata da alkawarin da Jehobah ya yi cewa zai biya bukatun mutanensa?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga ko Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa kuɗi bai da kyau.

“Kudi Shi Ne Tushen Dukan Mugunta Kuwa?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga irin bayarwa da ke faranta wa Allah rai.

“Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Bayarwa?” (Talifin jw.org)

Ku karanta talifin nan don ku ga ko caca wasa ne kawai.

“Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce​—Caca” (Awake!, Maris 2015)

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da ya taimaka wa wani mutum ya daina caca da kuma sata.

“Ina Son Sukuwa Sosai” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Janairu, 2012)