Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 42

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Aure da Rashin Aure.

Abin da Littafi Mai Tsarki Ya Ce Game da Aure da Rashin Aure.

A wasu wurare, mutane suna ganin mutum ba zai yi farin ciki ba idan bai yi aure ba. Duk da haka, ba dukan ma’aurata ba ne suke farin ciki kuma ba dukan waɗanda ba su yi aure ba ne suke baƙin ciki. Littafi Mai Tsarki ya ce, da aure da rashin yin aure, duka abubuwa masu kyau ne a wurin Jehobah.

1. Ta yaya mutum zai amfana idan bai yi aure ba?

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Wanda ya yi aure ya yi daidai, amma wanda bai yi ba ma ya fi.” (Karanta 1 Korintiyawa 7:​32, 33, 38.) Ta yaya wanda bai yi aure ba ya fi? Waɗanda ba su yi aure ba, ba su da hakkin kula da mata ko miji. Hakan ya sa sun fi samun ’yanci. Alal misali, wasu suna ƙara ƙwazo a hidimar Jehobah a hanyoyi dabam-dabam, kamar zuwa wasu wurare don yin wa’azi. Mafi muhimmanci ma, suna da zarafin yin abubuwa da za su sa su ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah.

2. Ta yaya mutum zai amfana idan ya yi aure yadda ya dace?

Kamar waɗanda ba su yi aure ba, waɗanda suka yi aure ma suna amfana. Littafi Mai Tsarki ya ce “Gwamma mutum biyu da mutum ɗaya.” (Mai-Wa’azi 4:9) Hakan zai yiwu idan ma’aurata suka bi ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki. Mace da namiji da suka yi aure yadda ya dace, sun ɗau alkawari cewa za su ƙaunaci juna da daraja juna da kuma mutunta juna. Saboda haka, za su fi waɗanda suke zaman dadiro kasancewa da kwanciyar hankali. Yaransu ma za su kasance da kwanciyar hankali.

3. Mene ne ra’ayin Jehobah game da aure?

Sa’ad da Jehobah ya haɗa aure na farko, ya ce: “Mutum zai bar babansa da mamarsa ya manne wa matarsa.” (Farawa 2:24) Jehobah yana so mata da miji su ƙaunaci juna kuma su zauna tare muddar ransu. Amma ya ba su dama su kashe auren idan ɗaya daga cikinsu ya yi zina. A irin wannan yanayin, an ba marar laifin dama ya zaɓa ko zai kashe auren ko ya ci gaba da zama da mai laifin. a (Matiyu 19:9) Jehobah bai amince Kiristoci su auri fiye da mace ɗaya ba.​—1 Timoti 3:2.

KA YI BINCIKE SOSAI

Za mu koyi yadda za mu yi farin ciki kuma mu faranta ran Jehobah, ko da mun yi aure ko ba mu yi ba.

4. Ka yi amfani da damarka na marar aure da kyau

Yesu ya ce, baiwa ce mutum ya zama marar aure. (Matiyu 19:​11, 12) Ku karanta Matiyu 4:​23, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Ta yaya Yesu ya yi amfani da baiwarsa na marar aure don ya bauta wa Jehobah kuma ya taimaka wa mutane?

Kiristoci da ba su yi aure ba za su iya farin ciki idan suka yi amfani da yanayinsu na marasa aure kamar yadda Yesu ya yi. Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • A waɗanne hanyoyi ne Kiristoci marasa aure za su yi amfani da damarsu da kyau?

Ka sani?

Littafi Mai Tsarki bai faɗi ainihin shekaru da mutum zai kai kafin ya yi aure ba. Amma ya umurci mutum ya jira har sai ya “wuce lokacin da sha’awar yin jima’i yake da ƙarfi sosai,” domin a lokacin zai yi wa mutum wuya ya yanke shawara mai kyau.​—1 Korintiyawa 7:​36, NWT.

5. Kada ka yi gaggawar yin aure

Wata shawara mafi muhimmanci da mutum zai yanke a rayuwa ita ce zaɓan wanda zai aura. Ku karanta Matiyu 19:​4-6, 9, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa bai kamata mutum ya yi hanzarin yin aure ba?

Littafi Mai Tsarki zai taimaka muku ku zaɓi miji ko mace da ta dace da ku. Abin da ya fi muhimmanci shi ne cewa wadda ka zaɓa tana ƙaunar Jehobah. b Ku karanta 1 Korintiyawa 7:39 da 2 Korintiyawa 6:14. Sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Me ya sa ya kamata mu auri mutumin da ke bauta wa Jehobah?

  • Yaya kake ganin Jehobah zai ji idan mutum ya yanke shawarar auran mutumin da ba ya ƙaunar Jehobah?

Idan aka haɗa dabbobi biyu waɗanda girmansu da ƙarfinsu ba ɗaya ba don su yi noma tare, za su sha wahala. Hakazalika, idan Kirista ya auri wadda ba ta bauta wa Jehobah, zai fuskanci matsaloli da yawa

6. Ka kasance da ra’ayin Jehobah game da aure

A zamanin Isra’ilawa, wasu maza suna kashe aurensu don dalilin da bai taka-kara-ya-karya ba. Ku karanta Malakai 2:​13, 14, 16, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Me ya sa Jehobah yake so mu bi ƙa’idodinsa idan muna so mu kashe aurenmu?

Idan ɗaya daga cikin ma’aurata ya yi zina kuma suka kashe aurensu, hakan zai sa marar laifin da yaransu sha wahala

Ku kalli BIDIYON nan, sai ku tattauna tambayar da ke gaba.

  • Idan ka yi aure kuma abokiyar aurenka ba ta bauta wa Jehobah, me za ka yi don ku zauna lafiya?

7. Ka bi ƙa’idodin Jehobah game da aure

Mutum yana bukatar ya yi ƙoƙari sosai don ya bi ƙa’idodin Jehobah game da aure. c Duk wanda ya yi hakan, Jehobah zai albarkace shi. Ku kalli BIDIYON nan.

Ku karanta Ibraniyawa 13:​4, sai ku tattauna tambayoyin nan:

  • Kana ganin ƙa’idodin Jehobah game da aure sun dace? Me ya sa?

A yawancin ƙasashe, gwamnati takan bukaci mutane su kasance da takardar shaidar aure ko kuma takardar shaidar kashe aure. Jehobah yana so Kiristoci su bi wannan dokar. Ku karanta Titus 3:​1, sai ku tattauna tambayar nan:

  • Idan kana da aure, ka tabbata cewa ka yi hakan bisa dokar da gwamnati ta kafa?

WANI YANA IYA CEWA: “Me amfanin yin aure? Mace da namiji ba za su iya zaman dadiro ba?”

  • Me za ka ce masa?

TAƘAITAWA

Idan mun yi aure ko ba mu yi aure ba dukansu baiwa ce daga wurin Jehobah. Dukansu za su iya sa mu farin ciki idan muka bi ƙa’idodin Jehobah.

Bita

  • Ta yaya mutum zai yi amfani da damarsa na marar aure a hanyar da ta dace?

  • Me ya sa Littafi Mai Tsarki ya ce mutum ya auri mai bauta wa Jehobah kaɗai?

  • Mene ne Littafi Mai Tsarki ya ce zai iya sa mutum ya kashe aure?

Maƙasudi

KA BINCIKA

Ku karanta talifin nan don ku ga abin da yake nufi “mutum ya auri mai bin Ubangiji.”

“Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu” (Hasumiyar Tsaro, 1 ga Yuli, 2004)

Ku kalli bidiyoyi biyun nan don ku ga abin da zai taimaka wa mutum ya yanke shawarwari masu kyau game da fita zance da kuma aure.

Yadda Za Ka Yi Shirin Yin Aure (11:53)

Ku kalli bidiyon nan don ku ga abin da ya sa wani ɗan’uwa ya ce, albarkun da Jehobah ya ba shi sun fi abubuwan da ya rasa.

Na Sa Rai ko Za Ta Bauta wa Jehobah (1:56)

Ku karanta talifin nan don ku ga wasu abubuwan da ya kamata mutane su yi tunani a kansu kafin su kashe aurensu ko su rabu.

Ku Riƙa Daraja “Abin da Allah Ya Haɗa” (Hasumiyar Tsaro, Disamba 2018)

a Ka duba Ƙarin Bayani na 4 game da rabuwa idan ba wanda ya yi zina a cikin ma’auratan.

b A wasu wurare, iyaye ne suke zaɓar wa yaransu wanda za su aura. Idan haka ne, ya kamata iyaye su zaɓi wanda yake ƙaunar Jehobah, ba don yana da kuɗi ko matsayi ba.

c Idan mace da namiji suna zaman dadiro, su da kansu ne za su yanke shawara ko za su yi aure ko za su rabu.