NA UKU
SASHEBacin Rai —Sa’ad da Wani Ya Bata Mana Rai
Wata Kirista mai suna Linda ta ce: “Wata ’yar’uwa a cikin ikilisiyarmu ta zarge ni da sace kuɗinta. Da wasu a cikin ikilisiyar suka ji labarin, sai suka soma goyon bayanta. Daga baya, ’yar’uwar ta gaya mini cewa ta sami bayani da ya nuna cewa ban saci kuɗinta ba. Ko da yake ta roƙi gafara, na ji kamar ba zan iya gafarta mata ba saboda yanayin da ta sa ni a ciki.”
AN TAƁA ɓata maka rai kamar yadda aka ɓata wa Linda rai? Abin baƙin ciki, wasu sukan bar halin wasu ya sa su yi sanyin gwiwa a ibadarsu ga Jehobah. Hakan ya taɓa faruwa da kai?
Babu Wanda Zai Iya “Raba Mu da Ƙaunar Allah”
Hakika, idan wani ɗan’uwa ya yi abin da ya ɓata mana rai, yakan yi mana wuya mu gafarta masa. Hakan ba abin mamaki ba ne don ya kamata Kiristoci su ƙaunaci juna. (Yohanna 13:34, 35) Mukan yi baƙin ciki sosai idan wani ɗan’uwa ya ɓata mana rai.—Zabura 55:12.
Littafi Mai Tsarki ya ce a wani lokaci Kiristoci sukan ɓata wa juna rai. (Kolosiyawa 3:13) Idan wani ɗan’uwa ko wata ’yar’uwa ta ɓata mana rai, bi da wannan yanayin yadda ya kamata ba zai zama da sauƙi ba. Shin mene ne ya kamata mu yi? Ga wasu ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki guda uku da za su taimaka mana:
Ubanmu na sama ya san abin da ke faruwa. Jehobah yana lura da duk abubuwan da ke faruwa kuma hakan ya haɗa da duk wani rashin adalci da aka yi mana da kuma wahalar da muke sha a sakamakon haka. (Ibraniyawa 4:13) Ƙari ga haka, Jehobah ba ya jin daɗi sa’ad da muke shan wahala. (Ishaya 63:9) Ba zai taɓa yarda “ƙunci, ko raɗaɗi” ko wani abu, ko kuma wani bawansa ya “raba mu da ƙaunar Allah” ba. (Romawa 8:35, 38, 39) Ya kamata sanin hakan ya sa mu yi ƙudiri cewa babu wani abu ko wani mutum da zai raba dangantakarmu da Jehobah, ko ba haka ba?
Gafarta wa mutum ba ya nufin amincewa da laifinsa. Idan muka gafarta wa waɗanda suka yi mana laifi, hakan ba ya nufin cewa abin da suka yi yana da kyau ko kuma muna ɗaura musu gindi. Jehobah ba ya amincewa da zunubi, amma yana gafarta wa mutane idan yin hakan ya dace. (Zabura 103:12, 13; Habakkuk 1:13) Jehobah yana gaya mana mu riƙa gafarta wa mutane domin yana so mu yi koyi da shi. Ba ya “fushi har abada.”—Zabura 103:9; Matta 6:14.
Za mu amfani kanmu idan muna gafarta wa mutane. Ta yaya? Ka yi la’akari da wannan misalin. A ce ka miƙa hannunka kana ɗauke da dutse da bai da nauyi sosai. Wataƙila ba za ka gaji ba idan ka riƙe shi na ɗan lokaci. Amma idan ka daɗe kana riƙe da shi fa? Babu shakka, hannunka zai soma yi maka zafi! Hakan ba ya nufin cewa dutsen ya ƙara nauyi, amma idan ka riƙe dutsen na tsawon lokaci, za ka ji kamar ya ƙara nauyi. Hakazalika, idan muka ci gaba da riƙe mutum a zuciya, za mu ƙara ɓata wa kanmu rai. Shi ya sa Jehobah ya ƙarfafa mu mu riƙa gafarta wa mutane da suka yi mana laifi. Hakika, za Misalai 11:17.
mu amfani kanmu idan muna gafarta wa mutane.—“Na Ji Kamar Jehobah Yana Magana da Ni”
Mene ne ya taimaka wa Linda kada ta riƙe ’yar’uwar da ta yi mata laifi a zuciya? Ta ɗauki wasu matakai kuma ta yi bimbini a kan dalilan da Littafi Mai Tsarki ya bayar na gafartawa. (Zabura 130:3, 4) Abin da ya ƙarfafa Linda shi ne sanin cewa Jehobah zai gafarta mana idan muka gafarta wa mutane da suka yi mana laifi. (Afisawa 4:32–5:2) Sanin hakan ya taimaka mata sosai kuma ta ce: “Na ji kamar Jehobah yana magana da ni.”
Da shigewar lokaci, Linda ta daina fushi kuma ta gafarta wa ’yar’uwar, yanzu su abokai ne na kud da kud. Linda ta ci gaba da hidimarta ga Jehobah. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah yana son ya taimaka maka ka yi hakan.