Wasika Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah
Ɗan’uwa:
Kamar yadda ka sani, Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran mutane. Maza da mata da yawa daga cikinsu amintattu ne da suka fuskanci irin matsalolin da muke fuskanta a yau. Su mutane ne kamar mu. (Yaƙub 5:17) Wasu sun yi baƙin ciki saboda matsaloli da damuwa. Wasu kuma, sun fuskanci matsaloli daga iyalinsu da kuma wasu da suke bauta wa Jehobah. Ƙari ga haka, wasu sun yi baƙin ciki saboda kurakuran da suka yi.
Waɗannan matsalolin ya sa wasu a cikin su sun nisanta kansu da Jehobah. Shin sun daina bauta masa gaba ɗaya ne? A’a. Yanayinsu ya yi daidai da na wani marubucin zabura da ya yi addu’a cewa: ‘Na ɓace kamar ɓatacciyar tunkiya; ka nemi bawanka; gama ban manta da dokokinka ba.’ (Zabura 119:176) Ka taɓa kasancewa a cikin irin wannan yanayin?
Jehobah ba ya mantawa da bayinsa da suka bar garkensa. A maimakon haka, yana biɗansu kuma yakan yi amfani da wasu bayinsa don ya taimaka musu. Alal misali, ka yi la’akari da yadda Jehobah ya taimaka wa bawansa Ayuba da ya fuskanci matsaloli dabam-dabam. Hakan ya haɗa da asarar dukiya, rasuwar ’ya’yansa da kuma ciwo mai tsanani. Ban da haka, abokansa da ya kamata su ƙarfafa shi suka gaya masa baƙar magana. Ko da yake Ayuba ya yi wasu tunani da ba su dace ba, bai bijire wa Jehobah ba. (Ayuba 1:22; 2:10) Ta yaya Jehobah ya taimaka wa Ayuba ya daidaita tunaninsa?
Wata hanyar da Jehobah ya taimaka wa Ayuba ita ce ta yin amfani da wani bawansa mai suna Elihu. Sa’ad da Ayuba ya faɗi abin da yake damunsa, Elihu ya saurare shi kafin ya furta albarkacin bakinsa. Me ya ce? Ya kushe ko kuma ya matsa wa Ayuba ta wajen nuna masa cewa ya yi laifi ne? Shin Elihu ya ɗauki kansa da muhimmanci fiye da Ayuba ne? A’a. Ruhun Allah ya motsa Elihu kuma ya ce: “A wurin Allah kamarku ni ke: Daga cikin ƙasa aka ɗauke ni, aka sifanta [ni].” Bayan haka, sai ya ƙarfafa Ayuba cewa: ‘Ba mai-ban razana ne ni da zan tsoratar da kai ba, ba kuwa zan danne ka da nauyi ba.’ (Ayuba 33:6, 7) Elihu bai sa Ayuba baƙin ciki kamar yadda abokansa suka yi ba. A maimakon haka, ya ƙarfafa shi kuma abin da Ayuba yake bukata ke nan!
Hakazalika, muna so ka san cewa mun shirya wannan ƙasidar ce don mu ƙarfafa ka. Da farko, mun saurari ra’ayin wasu ’yan’uwan da suka yi sanyin gwiwa a ibadarsu kuma mun yi la’akari da yanayinsu. (Misalai 18:13) Bayan haka, mun yi addu’a kuma mun bincika labaran Littafi Mai Tsarki game da bayin Jehobah da suka fuskanci irin wannan yanayin. Sai muka haɗa waɗannan nassosin Littafi Mai Tsarki da labaran wasu ’yan’uwa a zamaninmu don mu shirya wannan ƙasidar. Saboda haka, muna gayyatarka ka bincika abin da ke ciki. Muna maka fatan alheri don muna ƙaunarka sosai.
Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah