Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

SASHE NA ƊAYA

Zan Nemo Wanda Ya Bata

Zan Nemo Wanda Ya Bata

Tunkiyar ta ruɗe. Ta ɓace ne yayin da take cin ciyawa da ke ɗan nesa da garken. Yanzu, ta rasa inda makiyayin da garken suke kuma dare ya soma yi. Ba mai kāre ta kuma namomin daji kamar su kura suna yawo a kwarin. Ana nan, sai tunkiyar ta ji muryar makiyayinta kuma ta gan shi yana zuwa a guje don ya ɗauke ta ya kai ta gida.

JEHOBAH ya kwatanta kansa da makiyayi. A cikin Kalmarsa ya ba mu wannan tabbaci: “Zan biɗi tumakina, in bi sawunsu.”—Ezekiyel 34:11, 12.

Tumakin Garken Jehobah

Su wane ne tumakin Jehobah? Su ne mutanen da suke bauta wa Jehobah domin suna ƙaunarsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mu yi sujjada mu yi ruku’u, mu durƙusa a gaban Ubangiji Mahaliccinmu: Gama shi Allahnmu ne, mu mutanen makiyayarsa ne, tumakin hannunsa.” (Zabura 95:6, 7) Bayin Jehobah suna son bin jagorarsa kamar yadda tumaki suke bin makiyayinsu. Shin su kamiltattu ne? A’a. A wani lokaci, wasu bayin Jehobah sukan zama kamar tumakin da suka “watse” ko kuma “ɓatattun tumaki.” Hakika, wasu daga cikinsu suna “ɓacewa kamar tumaki.” (Ezekiyel 34:12; Matta 15:24; 1 Bitrus 2:25) Amma Jehobah ba ya yin watsi da bawansa da ya daina tarayya da mutanensa.

Kana ganin Jehobah shi ne Makiyayinka har ila? Ta yaya Jehobah yake kula da tumakinsa a yau. Bari mu tattauna hanyoyi uku.

Yana koyar da mu. Jehobah ya ce zai yi kiwon tumakinsa a “makiyaya mai-kyau” kuma “za su kwanta a garke mai-kyau; a wuri mai-albarka za su yi kiwo.” (Ezekiyel 34:14) Jehobah bai taɓa fasa ba mu abubuwan da muke bukata don mu ƙarfafa dangantakarmu da shi ba. Wataƙila wani talifi da ka karanta ko jawabi da ka saurara ko kuma wani bidiyonmu da ka kalla ya taimaka maka sosai kuma haka ya tabbatar maka cewa Jehobah yana ƙaunarka.

Yana kāre mu kuma yana tallafa mana. Jehobah ya ce: “Zan . . . komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗaura karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi.” (Ezekiyel 34:16, Littafi Mai Tsarki) Jehobah yana ƙarfafa marasa ƙarfi da masu baƙin ciki. Yana kula da waɗanda suka raunana wataƙila saboda abin da wasu ’yan’uwa suka yi musu. Ya taimaka musu su warware daga matsalolin. Ƙari ga haka, yana dawowa da waɗanda suka yi makuwa, wato waɗanda suka bar garke saboda baƙin ciki.

Ya san hakkinsa ne ya kula da mu. Jehobah ya ce zai ‘cece su daga cikin dukan wuraren da aka warwatsar da su,’ kuma zai ‘nemo [wanda] ya ɓace.’ (Ezekiyel 34:12, 16) A gaban Jehobah, wanda ya ɓace bai yi nisan da ba zai ji kira ba. Idan tunkiya ta ɓata, Jehobah yana sane da hakan. Zai biɗi tunkiyar kuma idan ya samu, yana farin ciki. (Matta 18:12-14) Shi ya sa ya ce bayinsa ‘tumakin’ garkensa ne. (Ezekiyel 34:31) Kana ɗaya daga cikin waɗannan tumakin.

A gaban Jehobah, wanda ya bace bai yi nisan da ba zai ji kira ba. Zai bidi tunkiyar kuma idan ya samu, yana farin ciki

“Ka Sabonta Kwanakinmu Kamar Dā”

Me ya sa Jehobah yake biɗanka don ka dawo gare shi? Me ya sa yake kiran ka ka dawo gare shi? Don yana so ka yi farin ciki. Ya yi alkawari cewa zai yi wa mutanensa albarka. (Ezekiyel 34:26) Wannan ba alkawarin banza ba ne. Ka riga ka shaida shi mai yi wa mutanensa albarka ne.

Ka tuna da abubuwan da suka faru da kai sa’ad da ka soma bauta wa Jehobah. Alal misali, yaya ka ji sa’ad da ka koyi gaskiya game da sunan Allah da kuma alkawarin aljanna a duniya? Shin ka tuna da yadda ka yi farin ciki sa’ad da kake halartan manyan taro tare da ’yan’uwa? Sa’ad da wani ya ji daɗin wa’azin bisharar da ka yi masa, hakan bai sa ka farin ciki a ranar ba?

Za ka iya sake yin farin ciki kamar yadda ka yi a lokacin. Bayin Jehobah na dā sun roƙi Allah suna cewa: “Ka maishe mu wurinka, ya Ubangiji, mu kuma za mu juya: Ka sabonta kwanakinmu kamar dā.” (Makoki 5:21) Jehobah ya amsa addu’ar da suka yi kuma mutanensa sun dawo suka ci gaba da bauta masa da farin ciki. (Nehemiya 8:17) Kai ma Jehobah zai taimaka maka ka komo gareshi.

Duk da haka, komawa ga Jehobah bai da sauƙi. Ka yi la’akari da wasu matsalolin da za ka iya fuskanta da kuma yadda za ka magance su.