Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 14

Abin da Ya Sa Ya Kamata Mu Yafe

Abin da Ya Sa Ya Kamata Mu Yafe

AKWAI wanda ya taɓa yi maka abin da ba shi da kyau?— Ya cuce ka ne ko kuma ya yi maka rashin adalci?— Ya kamata ka yi masa rashin adalci ne kamar yadda ya yi maka?—

Idan wani ya cuce su, mutane da yawa za su rama cuta ga macucin. Amma Yesu ya koyar da cewa ya kamata mu yafe wa waɗanda suka yi mana laifi. (Matta 6:12) To, idan mutumin ya yi mana rashin adalci sau da yawa fa? Sau nawa ya kamata mu yafe masa?—

Wannan shi ne abin da Bitrus yake so ya sani. Saboda haka wata rana ya tambayi Yesu: ‘Dole ne in yafe masa har sau bakwai?’ Sau bakwai ya yi kaɗan. Yesu ya ce: ‘Ka yafe masa sau saba’in da bakwai’ idan mutumin ya yi maka laifi da yawa haka.

Menene Bitrus yake so ya sani game da yafewa?

Wannan yana da yawa! Ba za mu ma ƙirga irin wannan laifuffuka da mutum ya yi mana ba, ko ba haka ba? Wannan shi ne abin da Yesu yake gaya mana: Kar mu yi ƙoƙarin tuna yawan lokacin da wasu suka yi mana laifi. Idan suka roƙi a yafe musu, ya kamata mu yafe musu.

Yesu yana so ya nuna wa almajiransa yadda yake da muhimmanci su riƙa gafartawa. Saboda haka, bayan ya amsa tambayar Bitrus, ya ba almajiransa wani labari. Kana so ka ji labarin?—

An taɓa wani sarki nagari. Yana da kirki sosai. Yana ba wa bayinsa ma bashi idan suna bukatar taimako. Amma rana ta kai da sarkin yake so bayinsa su biya bashin. Aka kawo wani bawa wanda sarki yake bin sa bashin kuɗi sulalla miliyan 60. Kuɗin suna da yawa!

Menene ya faru sa’ad da bawan ya roƙi sarki ya ba shi lokaci domin ya biya shi?

Amma bawan ya riga ya kashe dukan kuɗin sarki kuma ba shi da kuɗin biya. Saboda haka, sarkin ya ba da umurni a sayar da mutumin. Sarkin ya ce a sayar da matar mutumin da yaransa da dukan abin da yake da shi. Sai a biya sarki da kuɗin da aka sayar da su. Yaya kake tsammanin bawan zai ji?—

Bayan ya durƙusa a gaban sarkin ya yi roƙo: ‘Don Allah, ka ƙara mini lokaci, zan biya ka dukan kuɗin da na karɓa.’ Idan kai sarki ne me za ka yi da bawan?— Sarkin ya ji tausayin bawan. Sai sarkin ya yafe masa. Ya gaya wa bawan ya bari kada ya biya ko kwabo cikin kuɗi sulalla miliyan 60 da ake bin shi. Lallai wannan ya sa bawan murna sosai!

Amma menene bawan ya yi? Da ya fita sai ya sadu da wani bawa da yake bi bashi, sulalla ɗari kawai. Ya kama wuyar ɗan’uwansa bawa ya shaƙe, yana cewa: ‘Ka biya ni sulalla ɗari da nake bin ka bashi!’ Kana tsammanin mutum zai yi irin wannan abu, musamman ma bayan sarki ya yafe masa kuɗi masu yawa?—

Yaya bawan ya yi da bawa ɗan’uwansa wanda bai biya shi abin da yake bin sa ba?

Bawan da ya ci bashin kuɗi sulalla ɗari kawai talaka ne. Ba shi da kuɗin da zai biya a take. Sai ya durƙusa a gaban ɗan’uwansa bawa ya yi roƙo: ‘Don Allah, ka ƙara ba ni lokaci, zan biya ka dukan abin da na ci bashi.’ Ya kamata mutumin ya ƙara wa ɗan’uwansa bawa lokaci ne?— Da kai ne me za ka yi?—

Mutumin ba shi da kirki kamar yadda sarkin ya yi masa kirki. Yana son a ba shi kuɗinsa a take. Kuma domin ɗan’uwansa bawa bai biya shi ba, ya sa aka jefa shi a kurkuku. Wasu bayi sun ga dukan abin da ya faru, kuma ba su ji daɗinsa ba. Sun ji tausayin bawa da aka jefa a kurkuku. Saboda haka, suka je suka gaya wa sarki.

Sarkin bai ji daɗin abin da ya faru ba. Ya yi fushi sosai da bawan da ya ƙi ya yafe wa ɗan’uwansa. Saboda haka, ya kira shi ya ce masa: ‘Kai mugun bawa, ban yafe maka bashin da nake bin ka ba ne? Bai kamata kai ma ka yafe wa ɗan’uwanka ba?’

Menene sarki ya yi da bawan da ba ya yafewa?

Ya kamata da bawa wanda ya ƙi ya yafe wa ɗan’uwansa ya koyi darasi daga wannan sarki mai kirki. Amma bai koya ba. Saboda haka, sarki ya sa aka jefa shi a kurkuku har sai ya biya kuɗi sulalla miliyan 60 da yake bin shi. Kuma a kurkuku ba zai iya samun kuɗi ba da zai biya sarki. Saboda haka, zai zauna a wurin har mutuwarsa.

Da Yesu ya gama ba su wannan labarin, ya gaya wa mabiyansa: “Hakanan kuma Ubana na sama za ya yi muku, idan cikin zuciyarku ba ku gafarta ma ’yan’uwanku” ba.—Matta 18:21-35.

Ka gani, Allah yana bin dukanmu bashi mai yawa. Ranmu ma daga wurin Allah ne! Saboda haka, idan aka gwada da abin da Allah yake bin mu, abin da muke bin wasu mutane kaɗan ne kawai. Abin da muke bin su kamar kuɗi sulalla ɗari ne da ɗayan bawan yake bin ɗan’uwansa. Amma abin da Allah yake bin mu domin laifi da muke yi kamar kuɗi sulalla miliyan 60 ne da sarki yake bin wannan bawan.

Allah yana da kirki sosai. Ko da yake muna yin abin da ba shi da kyau, yana yafe mana. Ba ya sa mu biya shi ba ta wajen ɗaukan ranmu har abada. Amma wannan shi ne darasi da muke so mu riƙa tunawa: Allah zai yafe mana ne idan mun yafe wa mutane da suka yi mana laifi. Ya kamata mu yi tunani a kan wannan, ko ba haka ba?—

Me za ka yi idan wani ya roƙe ka ka yafe masa?

To, idan wani ya yi maka abin da ba shi da kyau, sai kuma ya ce, ka yi haƙuri, me za ka yi? Za ka yafe masa?— To, idan ya yi maka laifi sau da yawa fa? Har ila za ka yafe masa?—

Idan mu ne muke roƙo a yafe mana, za mu so mutumin ya yafe mana, ko ba haka ba?— Saboda haka, ya kamata mu ma mu yafe wa wasu. Kada kawai mu ce mun yafe masa, amma ya kamata mu yafe masa da gaske daga zuciyarmu. Sa’ad da muka yi haka, muna nunawa da gaske cewa muna so mu zama mabiyan Babban Malami.

Domin mu fahimci muhimmancin yafewa, bari mu karanta Misalai 19:11; Matta 6:14, 15; da kuma Luka 17:3, 4.