Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 7

Biyayya Tana Kāre Ka

Biyayya Tana Kāre Ka

ZA KA so idan za ka iya dukan abin da kake so? Da akwai lokatai ne da kake ji babu wanda zai gaya maka abin da za ka yi? Yanzu, ka faɗa mini gaskiyar abin da kake tunani.—

Me ya sa ya kamata ka yi wa manya biyayya?

Wanne ne ya fi maka? Yana da kyau ne ka yi dukan abin da kake so? Ko kuma abubuwa suna fin kyau idan ka yi wa babanka da mamarka biyayya?— Allah ya ce ya kamata ka yi wa iyayenka biyayya, saboda haka da kyakkyawan dalili na yin haka. Bari mu gani ko za ka fahimci dalilin.

Shekarunka nawa ne?— Ka san ko nawa ne shekarun babanka?— Ko nawa ne shekarun mamarka ko na kakarka da kakanka?— Sun rayu da daɗewa kafin a haife kai. Kuma idan mutum yana rayuwa na dogon lokaci, yana da lokaci da yawa na koyon abubuwa. Yana jin abubuwa da yawa kuma yana ganin abubuwa da yawa kowacce shekara. Saboda haka, yara za su koya daga manya.

Ka san wani wanda ka girme shi?— Ka san abubuwa fiye da yadda ya ko ta sani?— Me ya sa ka san abubuwa fiye da shi ko ita?— Domin ka girme su. Ka sami lokaci da yawa na koyon abubuwa fiye da wanda ka girme shi.

Waye ya rayu na dogon lokaci fiye da kai ko ni ko kuma dukan mutane?— Jehovah Allah ne. Yana da sani fiye da kai, yana kuma da sani fiye da ni. Idan ya gaya mana mu yi wani abu, za mu iya tabbata cewa abin da ya dace a yi ne, ko da yake zai yi wuyan yi. Ko ka san cewa har Babban Malami ya taba yi masa wuya ya yi biyayya?—

A wani lokaci Allah ya ce wa Yesu ya yi wani abu mai wuya. Yesu ya yi addu’a game da shi, kamar yadda muke gani a nan. Ya yi addu’a: “In ka yarda, ka kawar mini da wannan ƙoƙo.” Ta wajen wannan addu’a, Yesu ya nuna cewa ba kullum ba ne yake da sauƙi a yi nufin Allah. Amma yaya Yesu ya kammala addu’arsa? Ka sani?—

Menene za mu koya daga addu’ar Yesu?

Yesu ya kammala addu’arsa da cewa: “Amma dai ba nawa nufi ba, naka za a yi.” (Luka 22:41, 42) Hakika, yana son ya yi nufin Allah ba nasa ba. Kuma ya ci gaba ya yi abin da Allah ya bukace shi ya yi maimakon abin da shi yake gani zai fi kyau.

Menene za mu koya daga wannan?— Mun koyi cewa, daidai ne mu yi nufin Allah ko da yaushe, ko ba shi da sauƙi. Amma kuma mun koyi wani abu. Ka san ko menene wannan?— Cewa Allah da Yesu ba ɗaya suke ba, kamar yadda wasu mutane suke faɗa. Jehovah Allah shi ne babba kuma ya san abubuwa fiye da Ɗansa, Yesu.

Idan muka yi wa Allah biyayya muna nuna cewa muna ƙaunarsa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa.” (1 Yohanna 5:3) Ka gani, dukanmu muna bukatar mu yi wa Allah biyayya. Kana so ka yi masa biyayya, ko ba ka so ne?—

Bari mu buɗe Littafi Mai Tsarki mu ga abin da Allah ya gaya wa yara su yi. Za mu karanta abin da Littafi Mai Tsarki ya ce a Afisawa sura 6, ayoyi na 1, 2, da ta 3. Sun ce: “Ku ’ya’ya, ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku cikin Ubangiji: gama wannan daidai ne. Ka girmama babanka da mamarka ita ce doka ta fari tare da wa’adi, domin ka sami alheri, ka yi tsawon rai kuma cikin ƙasan.”

Jehovah Allah ne da kansa yake ce maka ka yi biyayya ga babanka da mamarka. Menene yake nufi a “girmama” su? Yana nufin a ba su daraja. Kuma Allah ya yi alkawarin cewa idan ka yi biyayya ga iyayenka, za ka samu “alheri.”

Bari in gaya maka labarin wasu mutane da aka ceci ransu domin sun yi biyayya. Waɗannan mutane sun rayu a can dā a Urushalima babban birni. Yawancin mutane a birnin ba su saurari Allah ba, domin haka, Yesu ya yi musu gargaɗi cewa Allah zai halaka birninsu. Yesu kuma ya gaya musu yadda za su tsira idan suna ƙaunar abin da yake da kyau. Ya ce: ‘Idan kun ga abokan gaba a dukan Urushalima, za ku sani cewa halakarta ta yi kusa. To lokaci ne da za ku gudu daga Urushalima zuwa kan duwatsu.’—Luka 21:20-22.

Ta yaya biyayya ga umurnin Yesu ya kāre waɗannan mutane?

Kamar yadda Yesu ya faɗa, abokan gaba suka kawo wa Urushalima hari. Sojojin Roma suka zagaya ta. Domin wasu dalilai sojojin suka tafi. Mutane da yawa suna tsammanin haɗarin ya wuce. Saboda haka suka zauna a cikin birnin. Amma menene Yesu ya ce ya kamata su yi?— Menene za ka yi idan kana cikin Urushalima?— Waɗanda suka gaskata da Yesu da gaske sun bar gidajensu suka gudu zuwa duwatsu da nesa daga Urushalima.

Babu abin da ya sami Urushalima shekara guda bayan haka. A cikin shekara ta biyu, babu abin da ya faru. Kuma a cikin shekara ta uku, babu abin da ya faru. Wasu mutane wataƙila sun yi tunanin cewa waɗanda suka bar birnin wawaye ne. Amma a shekara ta huɗu, sojojin Roma suka sake zuwa. Suka sake zagaya Urushalima. A yanzu babu daman tsira. A wannan lokacin sojojin suka halaka birnin. Yawancin mutane da suke ciki suka mutu, sauran kuma aka kwashe su zuwa kurkuku.

Amma menene ya sami waɗanda suka yi wa Yesu biyayya?— Sun tsira. Suna da nesa da Urushalima. Saboda haka ba su wahala ba. Biyayya ta kāre su.

Idan kana biyayya, za ta kāre ka?— Iyayenka za su ce maka kada ka yi wasa a kan titi. Me ya sa suka faɗi haka?— Domin mota za ta iya buge ka. Amma wata rana za ka yi tunani: ‘Ai yanzu babu motoci. Ba zan ji ciwo ba. Wasu yara suna wasa a kan titi, kuma ban taɓa ganin sun ji ciwo ba.’

Me ya sa za ka yi biyayya sa’ad da ba ka ga wasu haɗari ba?

Haka yawancin mutane da suke Urushalima suka ji. Bayan sojojin Roma suka tafi, kamar babu haɗari. Wasu suna zaune a cikin birnin. Sai su ma suka zauna. An yi musu gargaɗi amma ba su saurara ba. Domin haka suka yi hasarar rayukansu.

Bari mu ga wani misali. Ka taɓa wasa da ashana?— Kamar abin wasa ne idan ka ƙetta ashana kana kallon wutar. Amma wasa da ashana yana da haɗari ƙwarai. Dukan gida zai iya ƙonewa ƙurmus, kuma za ka iya mutuwa!

Ka tuna, yin biyayya wani lokaci kawai bai isa ba. Amma idan kana biyayya ko da yaushe, wannan babu shakka za ta kāre ka. Kuma waye ne ya gaya muku cewa “ ’Ya’ya ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku”?— Allah ne. Kuma, ka tuna cewa ya faɗi haka ne domin yana ƙaunarka.

Za mu karanta waɗannan nassosi da suka nuna muhimmancin biyayya: Misalai 23:22; Mai-Wa’azi 12:13; Ishaya 48:17, 18; da kuma Kolossiyawa 3:20.