BABI NA 15
Darasi A Kan Zama Mai Kirki
KA SAN abin da ƙiyayya take nufi?— Ƙiyayya ƙin mutane ne domin kawai sun bambanta ko kuma domin suna wani yare. Saboda haka, ƙiyayya ƙin ko kuma gaskata wani abu ne game da wani kafin ma ka san mutumin.
Kana tsammanin daidai ne ka ƙi mutum kafin ka san wane irin mutum ne wannan ko kuma kawai domin dabam yake?— A’a, ƙiyayya ba daidai ba ne, kuma rashin kirki ne. Bai kamata mu yi wa mutum rashin kirki ba kawai domin ya bambanta da mu.
Ka yi tunani game da wannan. Ka san wani da launin fatarsa ya bambanta da naka ko kuma wanda yake wani yare da ya bambanta da naka?— Wataƙila ka san mutanen da suka bambanta domin sun wahala ko kuma domin ba su da lafiya. Kana ƙauna da kuma yin kirki ga waɗanda suka bambanta da kai?—
Idan mun saurari Babban Malami, Yesu Kristi, za mu yi wa kowa kirki. Babu ruwanmu da ƙasar da mutum ya fito ko kuma launin fatarsa. Ya kamata mu yi musu kirki. Ko da yake ba haka dukan mutane suka gaskata ba, darasi ne da Yesu ya koyar. Bari mu yi magana game da shi.
Wani Bayahude da yake ƙin wasu mutane ya zo wurin Yesu ya tambaye shi, ‘Menene zan yi in rayu har abada?’ Yesu ya sani cewa mutumin wataƙila yana ƙoƙarin ya sa shi ya ce ya kamata mu yi kirki ga mutane da garinmu ɗaya da su ne. Amma maimakon ya amsa wannan tambayar da kansa, Yesu ya tambayi mutumin: ‘Menene Dokar Allah ta ce dole mu yi’?
Mutumin ya amsa: ‘Dole ne mu yi ƙaunar Jehovah Allahnmu da
dukan zuciyarmu, kuma dole ne mu yi ƙaunar maƙwabcinmu kamar kanmu.’ Yesu ya ce: ‘Ka ba da amsa daidai. Ka ci gaba da yin haka za ka samu rai madawwami.’Amma mutumin ba ya so ya yi kirki ko kuma ya yi ƙaunar mutanen da suka bambanta da shi ba. Saboda haka, ya nemi hujja. Sai ya tambayi Yesu: “Wanene maƙwabcina?” Wataƙila yana son Yesu ya ce: “Maƙwabtanka abokananka ne,” ko kuma “Mutane da suka yi kama da kai.” Domin ya amsa tambayar mutumin, Yesu ya ba da wani labari game da Bayahude da Basamariye. Buɗe kunnenka ka sha labari.
Wani mutum yana tafiya a kan hanyar da ta taso daga Urushalima zuwa Jericho. Wannan mutumin Bayahude ne. Da yake cikin tafiya sai ɓarayi suka kama shi. Suka nannaushe shi har ya faɗi, suka kwashi kuɗinsa da tufafinsa. Ɓarayin sun yi masa dūka suka bar shi ya kusan ya mutu a bakin hanya.
Ba da daɗewa ba, firist ya zo wucewa. Ya ga mutumin nan da ya ji ciwo sosai. Da me za ka yi?— Firist ɗin ya wuce kawai abinsa ta
wancan ɓangaren hanyar. Bai ma tsaya ba. Bai yi ƙoƙarin ya taimaki mutumin ba ma.Wani mutum kuma mai ibada sosai ya biyo ta hanyar. Balawi ne wanda yake hidima a haikali a Urushalima. Zai tsaya ne ya yi taimako?— A’a. Ya yi kamar yadda firist ɗin ya yi.
A ƙarshe, sai wani Basamariye ya biyo hanyar. Ka gan shi yana zuwa a kan hanyar? Ya ga Bayahude yana kwance ya ji ciwo sosai. Ka tuna cewa, yawancin Samariyawa da Yahudawa ba sa ƙaunar juna. (Yohanna 4:9) To, wannan Basamariye zai ƙyale wannan mutumin ne ba tare da taimakonsa ba? Zai gaya wa kansa ne: ‘Me ya sa zan taimaki wannan Bayahude? Da zai taimake ni ne idan na ji ciwo?’
Basamariyen ya dubi mutumin da yake kwance a bakin hanya, ya ji tausayinsa. Ba zai ƙyale shi ba ya mutu a nan. Sai ya sauƙo a kan jakinsa, ya je wurin mutumin, ya fara kula da ciwon da ya ji. Ya zuba musu mai da giya. Wannan zai sa ciwon ya warke. Sai ya ɗaure ciwon da ƙyalle.
Basamariyen a hankali ya ɗauki mutumin ya ɗora a kan jakinsa. Suka fara tafiya a hankali a kan hanyar har sai da suka kawo ga wani masauƙi, ko kuma wani ƙaramin otel. A nan Basamariyen ya nemi wurin kwana ga mutumin, kuma ya kula da shi da kyau.
Yesu ya tambayi mutumin da yake magana da shi: ‘Wanene tsakanin mutanen nan uku kake tsammani maƙwabci ne na kirki?’ Waye kake tsammani? Firist ɗin ne, ko Balawi, ko kuma Basamariye?—
Mutumin ya amsa: ‘Mutumin da ya tsaya ya taimaki mutumin da ya ji ciwo shi ne maƙwabci na kirki.’ Yesu ya ce: ‘Gaskiyarka. Ka yi tafiyarka ka yi hakanan kai ma.’—Luka 10:25-37.
Wannan ba labari ba ne mai kyau? Ya bayyana su wanene ne maƙwabtanmu. Ba abokananmu ba ne kawai. Ba mutane ba ne kawai da muke da irin launin fata
ɗaya da su ko kuma waɗanda muke yare ɗaya. Yesu ya koya mana mu yi kirki ga mutane ko daga ina suka fito, ko yaya kamaninsu, ko kuma yaren da suke yi.Haka Jehovah Allah yake yi. Ba shi da ƙiyayya. ‘Ubanmu wanda yake sama yana sa rana ta haska mutane masu mugunta da masu nagarta,’ in ji Yesu. ‘Kuma ya yi ruwan sama ga mutane masu nagarta da masu mugunta.’ Saboda haka, ya kamata mu yi kirki ga dukan mutane, kamar yadda Allah yake.—Matta 5:44-48.
Saboda haka idan wani ya ji ciwo, menene za ka yi?— To yaya idan mutumin ya zo ne daga wata ƙasa ko kuma launin fatarsa ya bambanta da naka? Har yanzu maƙwabcinka ne, kuma ya kamata ka taimake shi. Idan kana jin kai ƙarami ne ba za ka iya taimako ba, to, sai ka gaya wa babban mutum ya yi taimako. Ko kuma ka kira ɗan sanda ko kuma malamin makaranta ya yi taimako. Wannan yin kirki ne, kamar na Basamariye.
Babban Malami yana so mu zama masu kirki. Yana so mu taimaki wasu, ko su wanene ne. Abin da ya sa ke nan ya ba da labari game da Basamariye mai kirki.
Game da wannan darasi na yin kirki ga mutane ko ina ne ƙasarsu da kuma launin fatarsu, ka karanta Misalai 19:22; Ayukan Manzanni 10:34, 35; da kuma 17:26.