BABI NA 37
Ka Tuna da Jehovah da Kuma Dansa
A CE WANI ya ba ka kyauta ta musamman. Me za ka yi game da wannan?— Za ka ce na gode ne kawai ka mance da mutumin da ya yi maka kyautar? Ko kuma dai za ka tuna ne da shi da kuma kyautar da ya ba ka?—
Jehovah Allah ya ba mu kyauta ta musamman. Ya aiko Ɗansa duniya ya mutu dominmu. Ka san abin da ya sa dole ne Yesu ya mutu dominmu?— Wannan abu ne mai muhimmanci da ya kamata mu fahimta.
Kamar yadda muka koya a Babi na 23, Adamu ya yi zunubi sa’ad da ya karya kamiltacciyar doka ta Allah. Mu kuma mun gaji zunubi daga wurin Adamu, babanmu duka. To, me kake tsammani muke bukata?— Muna bukatar wani baba dabam, wanda ya yi kamiltacciyar rayuwa a duniya. Waye kake tsammanin zai iya zama wannan baban gare mu duka?— Yesu ne.
Jehovah ya aiko Yesu duniya saboda ya zama kamar shi ne babanmu maimakon Adamu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mutum na fari Adamu ya zama rayayyen rai. Adamu na ƙarshe ya zama ruhu mai-rayarwa.” Waye ne Adamu na fari?— Hakika, mutum wanda Allah ya halitta daga turɓayar ƙasa ne. Waye ne Adamu na biyu?— Yesu ne. Littafi Mai Tsarki ya nuna haka sa’ad da ya ce: “Mutum na fari [Adamu] daga ƙasa ne, ba-turɓaya: mutum na biyu [Yesu] daga sama ya ke.”—Tafiyar tsutsa tamu ce; 1 Korinthiyawa 15:45, 47; Farawa 2:7.
Tun da Allah ya ɗauki ran Yesu daga sama ya saka a cikin Maryamu, Luka 1:30-35) Abin da ya sa ke nan ma mala’ika ya gaya wa makiyaya sa’ad da aka haifi Yesu: “An haifa muku Mai-ceto.” (Luka 2:11) Amma domin ya zama Mai Cetonmu menene jariri Yesu yake bukatar ya yi?— Yana bukatar ya yi girma ya kai mutum, kamar Adamu. Sa’an nan ne Yesu zai zama ‘Adamu na biyu.’
Yesu bai gaji zunubi ba daga wurin Adamu. Abin da ya sa ke nan Yesu ya kasance kamilin mutum. (Yesu Mai Cetonmu zai kuma zama ‘Ubanmu madawwami.’ Haka aka kira shi a cikin Littafi Mai Tsarki. (Ishaya 9:6, 7) Hakika, Yesu kamiltacce zai iya zama ubanmu maimakon Adamu, da ya zama ajizi sa’ad da ya yi zunubi. A wannan hanyar za mu iya mu zaɓi ‘Adamu na biyu’ ya zama babanmu. Hakika, Yesu kansa Ɗan Jehovah Allah ne.
Idan muka san Yesu, za mu karɓe shi ya zama mai cetonmu. Ka san abin da muke neman a cece mu daga wurinsa?— E, daga wurin zunubi da mutuwa da muka gada daga wurin Adamu. Kamiltaccen rai da Yesu ya ba da shi hadaya dominmu, ana kiransa fansa. Jehovah ya yi tanadin fansa domin a kawar mana da zunubanmu.—Matta 20:28; Romawa 5:8; 6:23.
Hakika ba ma so mu manta da abin da Allah da kuma Ɗansa suka yi mana, ko ba haka ba?— Yesu ya nuna wa mabiyansa hanya ta musamman da za ta taimake mu mu tuna da
abin da ya yi mana. Bari mu yi taɗi a kanta.Ka yi tunanin kana cikin ɗaki a gidan sama a Urushalima. Dare ya yi. Yesu da manzanninsa suna zaune a kan kujeru a gaban teburi. A kan teburin da akwai naman rago da aka gasa, da gurasa da kuma jar giya. Suna cin dina ce ta musamman. Ka san abin da ya sa?—
Wannan abincin domin ya tuna musu ne abin da Jehovah ya yi shekaru ɗarurruwa da suka shige, sa’ad da mutanensa, Isra’ilawa, suke bauta a ƙasar Masar. A wannan lokacin Jehovah ya gaya wa mutanensa: ‘Kowace iyali ta yanka rago, kuma
ta shafa jinin a ƙofar gidajensu.’ Sai ya ƙara cewa: ‘Ku shiga cikin gidajenku ku ci ragon.’Isra’ilawan sun yi haka. A wannan daren mala’ikan Allah ya wuce ta cikin ƙasar Masar. A yawancin gidaje mala’ikan ya kashe ’ya’yan fari. Amma sa’ad da mala’ikan ya ga jinin rago a ƙofar gida sai ya ƙetare gidan. A waɗannan gidajen babu yara da suka mutu. Fir’auna, sarkin Masar, ya ji tsoro domin abin da mala’ikan Jehovah ya yi. Saboda haka Fir’auna ya gaya wa Isra’ilawa: ‘Kun sami ’yanci. Ku fita daga Masar!’ Sai suka kwashi kayansu a kan raƙuma da jakuna suka bar ƙasar.
Jehovah ba ya son mutanensa su manta yadda ya cece su. Saboda haka ya ce: ‘Sau ɗaya kowacce shekara ku ci irin wannan abincin da kuka ci daddaren nan.’ Suna kiran wannan abinci na musamman Idin Ƙetarewa. Ka san abin da ya sa?— Domin a wannan daren mala’ikan Allah ya ‘ƙetare’ gidajen da suke da alama ta jini.— Fitowa 12:1-13, 24-27, 31.
Yesu da manzanninsa suna tunanin wannan sa’ad da suke cin abincin ƙetarewan. Daga baya Yesu ya yi wani abu da yake da muhimmanci ƙwarai. Amma kafin ya yi abin, ya sallami manzo marar aminci, Yahuda. Sa’an nan Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi addu’a a kanta, ya gutsura ya bai wa almajiransa. “Ku karɓa ku ci,” in ji shi. Sai ya gaya musu: ‘Wannan gurasar a maimakon jikina ne da zan bayar sa’ad da na mutu dominku.’
Daga baya Yesu ya ɗauki kwaf na jar giya. Bayan ya sake wata addu’ar godiya, ya ba su kuma ya ce: “Dukanku ku sha daga cikinsa.” Kuma ya gaya musu: ‘Wannan giyar tana maimakon jinina ne. Ba da daɗewa ba za a zubar da jinina domin a cece ku daga zunubi. Ku ci gaba da yin wannan domin ku tuna da ni.’—Matta 26:26-28; 1 Korinthiyawa 11:23-26.
Ka lura cewa Yesu ya ce almajiransa su ci gaba da yin wannan domin su tuna da shi?— Ba za su sake cin abincin ƙetarewa ba kuma. Maimakon haka, sau ɗaya kowacce shekara su ci wannan abinci na musamman domin su tuna Yesu da kuma mutuwarsa. Ana kiran wannan dina Abincin Maraice na Ubangiji. A yau muna yawan kiransa Bikin Tuna Mutuwar Yesu. Me ya sa?— Domin yana tuna mana abin da Yesu da Ubansa, Jehovah Allah, suka yi dominmu.
Gurasar ya kamata ta sa mu tuna da jikin Yesu. Yana shirye ya yi hadayar wancan jikin domin mu sami rai na har abada. To, jar giyar fa?— Wannan ya kamata ta tuna mana tamanin jinin Yesu. Ya fi jinin ragon Ƙetarewa muhimmanci. Ka san abin da ya sa?— Littafi Mai Tsarki ya ce jinin Yesu zai sa a gafarta mana zunubanmu. Kuma sa’ad da zunubinmu gaba ɗaya suka ƙare, ba za mu yi rashin lafiya ba, ba za mu tsufa ba, ba za mu mutu ba. Ya kamata mu yi tunanin wannan lokacin da muka halarci Bikin Tuna Mutuwar Yesu.
Ya kamata kowa ya ci gurasan ne ya kuma sha giyar a lokacin Bikin Tuna Mutuwar Yesu?— Yesu ya gaya wa waɗanda suka ci kuma suka sha: ‘Za ku samu matsayi a mulkina kuma ku zauna a kan kujerun sarauta a sama tare da ni.’ (Luka 22:19, 20, 30) Wannan yana nufi ne cewa za su tafi sama su zama sarakuna tare da Yesu. Saboda haka, waɗanda suke da begen sarauta da Yesu ne kawai ya kamata su ci gurasar kuma su sha giyar.
Waɗanda ba sa cin gurasar da kuma shan giyar ya kamata su halarci Bikin Tuna Mutuwar. Ka san abin da ya sa?— Domin Yesu ya bayar da ransa dominmu ma. Ta wurin halartar Bikin Tuna Mutuwarsa, ya nuna cewa ba mu manta ba. Mun tuna da kyauta ta musamman da Allah ya ba mu.
Nassosi da suka nuna muhimmancin fansar Yesu sun haɗa da 1 Korinthiyawa 5:7; Afisawa 1:7; 1 Timothawus 2:5, 6; da kuma 1 Bitrus 1:18, 19.