Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 20

Kana So Kullum Ka Kasance Na Farko?

Kana So Kullum Ka Kasance Na Farko?

KA SAN wani da kullum yana so ya kasance na farko?— Zai iya ture wani domin ya kasance na fari a layi. Ka taɓa ganin wannan ya faru?— Babban Malami ya ga manyan mutane ma da suke so su zama na farko, ko kuma su sami wajaje masu muhimmanci. Kuma ba ya son haka. Saboda haka, bari mu ga abin da ya faru.

Ka taɓa ganin mutane suna ƙoƙarin su zama na farko?

Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa an gayyaci Yesu zuwa wata babbar liyafa a gidan wani Bafarisi, wanda shugaban addini ne mai matsayi. Bayan da Yesu ya isa, ya fara ganin wasu baƙi suna shigowa suna zaɓan wurare masu kyau. Saboda haka, ya ba waɗanda aka gayyace su wani labari. Kana so ka ji labarin?—

Yesu ya ce: ‘Idan wani ya gayyace ka zuwa bikin aure, kada ka nemi wuri da ya fi kyau, ko kuma da ya fi muhimmanci.’ Ka san abin da ya sa Yesu ya faɗi haka?— Ya yi bayani cewa wataƙila an gayyace mutumin da ya fi ka daraja. Kamar yadda kake gani a wannan hoton, mutumin da yake bikin ya zo, ya ce: ‘Ka ba wannan mutumin wuri, kai kuwa je ka can ka zauna.’ Yaya baƙon zai ji?— Zai ji kunya domin dukan wasu baƙin za su ga ya koma wurin da ba shi da muhimmanci.

Yesu ya nuna cewa ba shi da muhimmanci mu nemi wurin da ya fi kyau. Saboda haka, ya ce: ‘Idan aka gayyace ka zuwa bikin aure, ka je ka nemi wurin da ba na muhimmanci ba ne. Sai wanda ya gayyace ka ya zo ya ce, ‘Aboki, ka koma wuri mai kyau.’ Sai ka samu daraja a idanun dukan baƙin sa’ad da ka koma wuri da ya fi kyau.’—Luka 14:1, 7-11.

Wane darasi Yesu yake koyarwa sa’ad da ya yi magana game da waɗanda suke zama a wuri mafi muhimmanci, ko kuma na farko?

Ka fahimci labarin Yesu?— Bari mu ba da misali mu ga ko ka fahimta. Ka yi tunanin ka shiga cikin mota da ta cika da mutane. Ya kamata ka yi sauri ne ka zauna ka bar tsohon mutum a tsaye?— Yesu zai so idan ka yi haka?—

Wani zai ce abin da muka yi ba zai dami Yesu ba. Ka yarda da wannan?— Sa’ad da Yesu ya je babbar liyafa a gidan Bafarisi, ya lura da mutane suna zaɓan kujerunsu. Kana tsammanin bai damu da abin da muke yi ba ne a yau?— Yanzu da Yesu yana sama, yana inda zai iya ganinmu da kyau.

Sa’ad da wani yake ƙoƙarin ya zama na fari zai iya jawo masifa. Sau da yawa ana jayayya, kuma mutane sukan yi fushi. A wasu lokatai kuma wannan yana faruwa ne lokacin da yara suka fita yawo tare. Idan aka buɗe ƙofar mota, yara suna rige-rige. Suna son kujeru masu kyau waɗanda suke kusa da taga. Menene zai faru?— Sai su yi fushi da junansu.

Ƙoƙarin zama na farko zai iya jawo masifu da yawa. Har ma ya jawo rigima tsakanin manzannin Yesu. Kamar yadda muka koya a Babi na 6 na wannan littafin, sun yi musu tsakaninsu a kan ko wanene ya fi girma. Menene Yesu ya yi a lokacin?— Hakika, ya yi musu gyara. Amma daga baya sun sake yin musu kuma. Bari mu ga yadda ya faru.

Manzannin, tare da wasu, suna tafiya na ƙarshe da Yesu zuwa birnin Urushalima. Yesu yana yi musu magana game da Mulkinsa, sai Yaƙub da Yohanna suna tunani game da sarauta tare da shi. Sun ma yi magana da mamarsu, Salome, game da shi. (Matta 27:56; Markus 15:40) Sa’ad da suke kan hanyar zuwa Urushalima, Salome, ta zo wurin Yesu, ta durƙusa a gabansa, ta roƙe shi.

“Me ki ke so?” Yesu ya yi tambaya. Ta amsa cewa tana son Yesu ya sa ’ya’yanta su zauna a kusa da shi a Mulkinsa, ɗaya a hannun dama ɗayan kuma a hannun hagu. Sa’ad da sauran manzanni goma suka ji abin da Yaƙub da Yohanna suka biɗa ta wurin mamarsu, yaya kake tsammanin za su ji?—

Menene Salome ta roƙi Yesu, kuma menene ya faru?

Hakika, sun yi fushi da Yaƙub da Yohanna. Saboda haka, Yesu ya ba wa dukan almajiransa shawara mai kyau. Yesu ya gaya musu cewa sarakunan duniya suna son su zama manya kuma masu matsayi. Suna son waje mai muhimmanci, wurin da kowa zai yi musu biyayya. Amma Yesu ya gaya wa mabiyansa bai kamata su su zama haka ba. Maimakon haka, Yesu ya ce: “Dukan wanda ya ke so shi zama babba a cikinku, baranku za ya zama.” Ka yi tunanin wannan!—Matta 20:20-28.

Ka san abin da bawa yake yi?— Yana yin hidima ga wasu mutane, ba ya bukatar mutane su yi masa hidima. Shi yake zama a wuri marar muhimmanci, ba wuri na farko ba. Shi yake yi kamar ba shi da amfani, ba kamar wanda ya fi muhimmanci ba. Kuma ka tuna cewa Yesu ya ce wanda yake so ya zama na farko ya kamata ya zama bawan wasu.

Me kake tsammanin wannan yake nufi a gare mu?— Bawa zai yi musu ne da maigidansa game da wanda ya kamata ya zauna a wuri mafi kyau? Zai yi musu ne game da wanda ya kamata ya ci abinci da farko? Me ka gani?— Yesu ya yi bayani cewa bawa kullum yana saka maigidansa a gaba da shi.—Luka 17:7-10.

To, maimakon mu yi ƙoƙarin zama na farko, me ya kamata mu yi?— Ya kamata mu zama kamar bawa ga wasu. Kuma wannan yana nufin saka wasu gaba da mu. Yana nufin yin la’akari da cewa wasu sun fi mu muhimmanci. Za ka iya tunanin hanyar da za ka saka wasu gaba da kanka?— Ka koma shafi na 40 da 41 ka duba hanyoyin da za ka iya saka wasu a gaba ta wajen yi musu hidima da farko.

Za ka tuna cewa Babban Malami ya saka wasu gaba da kansa ya yi musu hidima. Yammarsa ta ƙarshe da manzaninsa, ya durƙusa ya wanke sawayen manzanninsa. Idan muka saka wasu farko, za mu faranta wa Babban Malami rai da kuma Ubansa Jehovah Allah.

Bari mu karanta wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki da suka ƙarfafa mu mu saka wasu gaba da kanmu: Luka 9:48; Romawa 12:3; da kuma Filibbiyawa 2:3, 4.