Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 22

Abin da Ya Sa Bai Kamata Mu Yi Karya Ba

Abin da Ya Sa Bai Kamata Mu Yi Karya Ba

A CE WATA yarinya ta ce wa mamarta: “Idan aka tashi a makaranta zan dawo gida babu ɓata lokaci.” Amma sai ta tsaya ta yi wasa da ƙawayenta ta zo ta gaya wa mamarta: “Malaminmu ne ya sa na ɓata lokaci bayan an tashi a makaranta.” Zai dace ta faɗi haka?—

Menene wannan yaron ya yi da ba daidai ba?

Ko kuma yaro ya gaya wa babansa: “Ba ni na buga kwallo a cikin gida ba.” Amma kuma idan shi ya buga da gaske fa? Ba zai dace ba ne ya ce shi ya buga?—

Babban Malami ya nuna mana abin da ya dace mu yi. Ya ce: ‘Bari zancenku ya zama, I, I; A’a, kuma a’a; abin da ya wuce waɗannan duka daga wurin mugun ne.’ (Matta 5:37) Menene Yesu yake nufi?— Abin da yake nufi shi ne mu yi abin da muka ce.

Da akwai wani labari a cikin Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa yana da muhimmanci mu faɗi gaskiya. Game da mutane biyu ne waɗanda suka ce su almajiran Yesu ne. Bari mu ga abin da ya faru.

Bai kai wata biyu ba bayan da Yesu ya mutu, mutane da yawa daga wurare masu nisa suka je Urushalima domin wani biki mai muhimmanci na Yahudawa da ake kira Faska. Manzo Bitrus ya ba da jawabi na musamman, a cikin jawabin ya gaya wa mutanen game da Yesu, wanda Jehovah ya ta da shi daga matattu. Lokaci na farko ke nan da wasu da suka je Urushalima suka koyi game da Yesu. Suna son ƙarin bayani. To, me suka yi?—

Suka yi fiye da kwanakin da suke tsammani. Bayan ɗan lokaci, kuɗin wasu tsakaninsu ya ƙare kuma suna bukatar kuɗi domin su sayi abinci. Almajiran da suke Urushalima suna so su taimaki baƙin. Saboda haka, da yawa cikinsu suka sayar da abin da suke da shi suka kai kuɗin ga manzannin Yesu. Sai manzannin suka ba wa waɗanda suke da bukata kuɗin.

Hananiya da matarsa, Safiratu, waɗanda suke cikin ikilisiyar Kirista ta Urushalima, suka sayar da filin da suke da shi. Babu wanda ya gaya musu su sayar da filin. Su suka yi shawarar haka da kansu. Amma abin da suka yi ba domin suna ƙaunar sababbin almajiran Yesu ba ne. Hananiya da Safiratu suna so ne mutane su yi tunanin cewa suna da kirki. Saboda haka, suka ce za su bayar da dukan kuɗin a taimaki wasu. Amma suna so su bayar da wasu ne cikin kuɗin da suka ce gaba ɗaya za su bayar. Me kake ji game da wannan?—

Sai Hananiya ya je wajen manzannin. Ya ba su kuɗin. Hakika Allah ya sani cewa ba dukan kuɗin ba ne ya bayar. Sai Allah ya sanar da manzo Bitrus cewa Hananiya ba shi da gaskiya a wannan batun.

Wace ƙarya Hananiya yake yi wa Bitrus?

Sai Bitrus ya ce: ‘Hananiya, me ya sa ka bar Shaiɗan ya sa ka ka yi haka? Filin naka ne. Ba dole sai ka sayar ba. Kuma bayan ka sayar ma, ai sai yadda ka yi da kuɗin. Amma me ya sa kake nuna cewa dukan kuɗin ka bayar sa’ad da wasu kawai cikin kuɗin ka bayar? Domin wannan ka yi ƙarya ba a gare mu ba kawai, amma har wa Allah.’

Wannan batu ne mai tsanani. Hananiya maƙaryaci ne! Bai yi abin da ya ce zai yi ba. Yana da’awar cewa yana yi. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana abin da ya faru daga baya. Ya ce: ‘Da jin maganar Bitrus, Hananiya ya faɗi ya mutu.’ Allah ya kashe Hananiya! Daga baya aka ɗauki gawarsa aka binne.

Me ya sami Hananiya domin ƙarya da ya yi?

Bayan kamar sa’o’i uku, Safiratu ta shigo. Ba ta san abin da ya faru da mijinta ba. Sai Bitrus ya tambaye ta: ‘Kun sayar da filin a kan kuɗin da kuka ba mu ne?’

Safiratu ta amsa: ‘E, haka muka sayar da filin.’ Amma ƙarya ta yi! Sun rage kuɗin da suka sayar da filin. Sai Allah ya kashe Safiratu ma.—Ayukan Manzanni 5:1-11.

Menene za mu koya daga abin da ya faru da Hananiya da Safiratu?— Ya koya mana cewa Allah ba ya son ƙarya. Yana son mu faɗi gaskiya ko da yaushe. Amma mutane da yawa sun ce daidai ne a yi ƙarya. Kana tsammanin gaskiyar waɗannan mutanen ne?— Ka san cewa ciwo, azaba, da kuma mutuwa a duniya suna faruwa ne domin an yi ƙarya?—

Waye Yesu ya ce ya yi ƙarya ta farko, kuma menene sakamakon haka?

Ka tuna, Iblis ya yi wa mace ta farko, Hauwa’u ƙarya. Ya gaya mata cewa ba za ta mutu ba idan ta yi wa Allah rashin biyayya ta ci ’ya’yan itacen da Allah ya ce kada ta ci. Hauwa’u ta gaskata Iblis ta ci ’ya’yan itacen. Ta sa Adamu ma ya ci. Suka zama masu zunubi kuma dukan ’ya’yansu ma aka haife su masu zunubi. Kuma domin su masu zunubi ne, dukan ’ya’yan Adamu suna wahala kuma suna mutuwa. Ta yaya dukan wannan masifa ta fara?— Da ƙarya ta fara.

Ba mamaki da Yesu ya ce Iblis “maƙaryaci ne shi, da uban ƙarya kuma”! Shi ne ya fara yin ƙarya. Idan wani ya yi ƙarya yana yin abin da Iblis ya yi ne da farko. Ya kamata mu tuna wannan idan muka ji kamar za mu yi ƙarya.—Yohanna 8:44.

Yaushe ne za ka ji kamar ka yi ƙarya?— Ba lokacin da ka yi laifi ba ne?— Ko ba ka yi niyya ba, wataƙila ka fasa wani abu. Idan aka tambaye ka game da shi, ya kamata ka ce ɗan’uwanka ne ko kuma ’yar’uwarka ce ta fasa? Ko kuma ya kamata ka yi kamar ba ka san yadda abin ya faru ba?—

Yaushe ne za ki ji kamar ki yi ƙarya?

To, idan ya kamata ka yi aikin da aka ba ka na gida, amma ka yi wasu ne cikinsu kawai fa? Ya kamata ne ka ce ka yi duka, sa’ad da ba ka yi ba?— Ya kamata mu tuna da Hananiya da Safiratu. Ba su faɗi gaskiya ba. Kuma Allah ya nuna cewa hakan ba shi da kyau ta wajen kashe su.

 

Saboda haka, ko menene muka yi, zai ƙara ɓata al’amari ne idan muka yi ƙarya. Kada ma mu faɗi rabi gaskiya. Littafi Mai Tsarki ya ce: Ka “faɗi gaskiya.” Kuma ya ƙara cewa: “Kada ku yi ma juna ƙarya.” Jehovah yana faɗan gaskiya kullum, kuma yana son mu ma mu faɗi gaskiya.—Afisawa 4:25; Kolossiyawa 3:9.

Ya kamata mu faɗi gaskiya ko da yaushe. Wannan ne abin da yake cikin Fitowa 20:16; Misalai 6:16-19; 12:19; 14:5; 16:6: da kuma Ibraniyawa 4:13.