Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 12

Yesu Ya Koya Mana Addu’a

Yesu Ya Koya Mana Addu’a

KANA yin magana da Jehovah Allah kuwa?— Yana so ka yi magana da shi. Sa’ad da ka yi magana da Allah, ana kiran wannan addu’a. Sau da yawa Yesu ya yi magana da Ubansa na sama. A wasu lokatai yana so ya kaɗaita sa’ad da yake yin magana da Allah. Sau ɗaya, Littafi Mai Tsarki ya ce, “Ya hau dutse, shi ɗaya, garin yin addu’a: sa’anda maraice ya yi, yana nan shi kaɗai.”—Matta 14:23.

Ina za ka je ka yi wa Jehovah addu’a kai kaɗai?— Wataƙila za ka iya yin magana da Jehovah kafin ka yi barci. Yesu ya ce: “Lokacinda ka ke yin addu’a, shiga cikin lolokinka, bayanda ka rufe ƙofarka kuma, ka yi addu’a ga Ubanka.” (Matta 6:6) Kana yi wa Jehovah addu’a kowanne dare kafin ka yi barci?— Ya kamata ka yi haka.

Yesu ya yi addu’a sa’ad da yake shi kaɗai . . . da kuma sa’ad da yake tare da mutane

Yesu kuma ya yi addu’a sa’ad da wasu mutane na tare da shi. Sa’ad da abokinsa Li’azaru ya mutu, Yesu ya yi addu’a tare da wasu a inda aka binne Li’azaru. (Yohanna 11:41, 42) Yesu kuma yana addu’a sa’ad da suka taru da almajiransa. Kana zuwa taro a inda ake yin addu’a?— A wajen dattijo yake yin addu’a. Ka saurari abin da yake faɗa domin yana yi wa Allah ne magana dominmu. Sa’an nan za ka iya cewa “Amin” ga addu’ar tasa.

Me ya sa za ka saurara ga addu’o’in da ake yi a taro?

Ka san abin da yake nufi a ce “Amin” a ƙarshen addu’a?— Yana nufin cewa kana son addu’ar. Yana nufin cewa ka yarda da addu’ar kuma kana so ta zama taka addu’ar kai ma. Yesu ya yi addu’a a lokacin cin abinci ma. Ya yi wa Jehovah godiya domin abincinsa. Kana yin addu’a kafin ka ci abinci?— Yana da kyau mu yi wa Jehovah godiya domin abincinmu kafin mu ci. Wani zai yi addu’a idan za ku ci abinci tare. To, idan kana ci kai kaɗai fa? Ko kuma kana cin abinci da mutane da ba sa yi wa Jehovah godiya fa?— Sai ka yi addu’arka.

Dole ne ko da yaushe ka ɗaga murya kana addu’a? Ko kuma Jehovah zai saurare ka ne idan ka yi addu’arka a zuciyarka?— Za mu samu amsa daga abin da ya faru da Nehemiah. Shi mai bauta wa Jehovah ne kuma yana aiki a fadar Sarkin Pashiya Artaxerxes. Wata rana Nehemiah ya yi baƙin ciki domin ya ji cewa garun Urushalima, ainihin birnin mutanensa, ya rushe.

Yaushe ne za ka iya yin addu’a a zuciyarka, kamar yadda Nehemiah ya yi?

Sa’ad da sarkin ya tambayi Nehemiah dalilin da ya sa yake baƙin ciki, Nehemiah da farko ya yi addu’a a cikin zuciyarsa. Sai Nehemiah ya gaya wa sarkin dalilin da ya sa yake baƙin ciki kuma ya tambaye shi izini ya je Urushalima ya sake gina garun. Menene ya faru?—

Hakika, Allah ya amsa addu’ar Nehemiah. Sarkin ya ba shi izini! Har sarkin ya ba Nehemiah katakai da yawa da zai yi amfani da su wajen ginin. Saboda haka Allah zai iya amsa addu’o’inmu, ko ma a zuciya muka yi su.—Nehemiah 1:2, 3; 2:4-8.

Ka yi tunani game da wannan. Ya kamata ka sunkuyar da kanka ne sa’ad da kake addu’a? Ko kuma ya kamata ka durƙusa ne? Me ka ce?— A wasu lokatai Yesu ya durƙusa sa’ad da yake addu’a. A wasu lokatai kuma ya tsaya a tsaye. Kuma a wasu lokatai ya ɗaga kansa sama sa’ad da yake addu’a, kamar yadda ya yi sa’ad da yake addu’a domin Li’azaru.

To, menene wannan ya nuna?— Wannan ya nuna cewa yadda ka tsaya ba shi ne abu mafi muhimmanci ba. Wasu lokatai yana da kyau mu sunkuyar da kanmu kuma mu rufe idanunmu. A wasu lokatai kuma za ka iya durƙusawa, kamar yadda Yesu ya yi. Amma ka tuna, za mu iya yi wa Allah addu’a a kowanne lokaci dare da rana, kuma zai saurare mu. Abu mafi muhimmanci game da addu’a shi ne mu gaskata da cewa Jehovah yana sauraron addu’armu. Ka yarda cewa Jehovah yana sauraron addu’arka?—

Menene za ka gaya wa Allah cikin addu’a?

Menene za mu faɗa cikin addu’armu ga Jehovah?— Gaya mini: Sa’ad da kake addu’a, menene kake magana game da shi ga Allah?— Jehovah yana ba mu abubuwa da yawa masu kyau, kuma daidai ne mu yi masa godiya dominsu, ko ba haka ba ne?— Za mu yi masa godiya domin abinci da muke ci. Amma ka taɓa yi masa godiya domin gajimare, itatuwa, da kuma furanni?— Shi ne ma ya yi su.

Almajiran Yesu sun taɓa ce masa ya koya musu yadda za su yi addu’a. Saboda haka Babban Malami ya koya musu, kuma ya gaya musu abubuwa masu muhimmanci da za su yi addu’a a kai. Ka san ko menene waɗannan abubuwa?— Ka ɗauki Littafi Mai Tsarki naka ka buɗe Matta sura 6. A ayoyi na 9 zuwa 13, za mu ga abin da mutane da yawa suke kira Ubanmu ko kuma Addu’ar Ubangiji. Bari mu karanta tare.

A nan mun koyi cewa Yesu ya gaya mana mu yi addu’a game da sunan Allah. Ya ce mu yi addu’a a tsarkake sunan Allah. Menene sunan Allah?— Babu shakka, sunan Jehovah ne, kuma ya kamata mu ƙaunaci wannan sunan.

Na biyu, Yesu ya koya mana mu yi addu’a domin Mulkin Allah ya zo. Mulkin yana da muhimmanci domin zai kawo salama a duniya kuma ya mayar da ita aljanna.

Na uku, Babban Malami ya ce mu yi addu’a a yi nufin Allah a duniya kamar yadda ake yinsa a cikin sama. Idan muka yi addu’a domin waɗannan, to, ya kamata mu yi abin da Allah yake so.

Na gaba, Yesu ya koya mana mu yi addu’a domin abinci na yini. Kuma ya gaya mana mu roƙi Allah ya gafarta mana idan muka yi abin da ba shi da kyau. Kuma ya kamata mu ce Allah ya gafarta mana. Amma kafin ya yi haka, dole ne mu yafe wa wasu idan suka yi mana abin da ba shi da kyau. Yana da sauƙi ne mu yi hakan?—

A ƙarshe, Yesu ya ce, ya kamata mu yi addu’a Jehovah ya kāre mu daga mugun, Shaiɗan Iblis. Dukan waɗannan abubuwa ne masu kyau da ya kamata mu yi wa Allah addu’a a kai.

Ya kamata mu gaskata cewa Jehovah yana sauraron addu’o’inmu. Ban da roƙonsa ya taimake mu, ya kamata mu ci gaba da yi masa godiya. Yana farin ciki sa’ad da muka yi gaskiya bisa abin da muka ce a addu’armu da kuma sa’ad da muka roƙe shi domin abubuwa da suke da kyau. Kuma zai ba mu waɗannan abubuwa. Ka gaskata da wannan?—

Shawarwari masu kyau game da addu’a suna cikin Romawa 12:12; 1 Bitrus 3:12; da kuma 1 Yohanna 5:14.