Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 34

Menene Zai Faru Idan Muka Mutu?

Menene Zai Faru Idan Muka Mutu?

KAMAR yadda ka sani, mutane a yau suna tsufa, su yi ciwo, kuma su mutu. Har wasu yara ma suna mutuwa. Ya kamata ne ka ji tsoron mutuwa ko kuma wanda ya riga ya mutu?— Ka san abin da yake faruwa idan muka mutu?—

Babu mutumin da yake rayuwa a yau da ya taɓa mutuwa kuma ya dawo ya gaya mana. Amma sa’ad da Yesu Babban Malami yake duniya an taɓa irin wannan mutumin. Za mu iya sanin abin da yake faruwa da waɗanda suka mutu ta wajen karanta labarin shi. Mutumin abokin Yesu ne da yake zama a Bait’anya, ƙaramin gari ne ba shi da nisa da Urushalima. Sunansa Li’azaru, kuma yana da yayarsa Martha da Maryamu ƙanwarsa. Bari mu ga abin da Littafi Mai Tsarki ya ce ya faru.

Wata rana Li’azaru ya yi rashin lafiya mai tsanani. A wannan lokaci Yesu yana wuri mai nisa. Martha da Maryamu suka aiki manzo ya gaya wa Yesu cewa ɗan’uwansu, Li’azaru ba shi da lafiya. Sun yi haka ne domin sun sani cewa Yesu zai iya zuwa ya warkar da ɗan’uwansu. Yesu ba likita ba ne, amma yana da iko daga wurin Allah da zai yi amfani da shi ya warkar da kowacce irin cuta.—Matta 15:30, 31.

Kafin Yesu ya je ya ga Li’azaru, Li’azaru ya yi ciwo sosai har ya mutu. Amma Yesu ya gaya wa almajiransa cewa Li’azaru yana barci kuma zai je ya tashe shi. Almajiran ba su fahimci abin da Yesu yake nufi ba. Saboda haka, Yesu ya gaya musu kai tsaye: “Li’azaru ya mutu.” Menene wannan ya nuna game da mutuwa?— Hakika, kamar barci ne mai zurfi. Barci ne mai zurfi sosai da mutumin ba zai yi mafarki ba ma.

Yesu yana zuwa ya ziyarci Martha da Maryamu. Abokansu da yawa ma sun isa gidan. Sun zo su yi wa ’yan’uwan ta’aziyya domin ɗan’uwansu ya mutu. Sa’ad da Martha ta ji cewa Yesu yana zuwa, ta je ta tare shi. Ba da daɗewa ba Maryamu ma ta fita ta ga Yesu. Tana kukan baƙin ciki, ta durƙusa a gabansa. Wasu abokanta da suka bi ta su ma suna kuka.

Babban Malami ya tambaya inda aka ajiye Li’azaru. Sai mutane suka kai Yesu kabarin da aka binne Li’azaru. Sa’ad da Yesu ya ga dukan mutanen suna kuka, shi ma ya fara kuka. Ya san yana da ban ciwo a yi rashin wanda ake ƙauna.

Da dutse a gaban kabarin, sai Yesu ya ce: “Ku kawar da dutsen.” Ya kamata ne su yi haka?— Martha tana ganin ba daidai ba ne. Ta ce: “Ubangiji, yanzu ya yi ɗoyi; gama kwanansa huɗu yanzu da mutuwa.”

Yesu ya gaya mata: “Ban ce miki ba, Idan kin bada gaskiya za ki ga girman Allah?” Yesu yana nufi ne cewa Martha za ta ga abin da zai kawo girmamawa ga Allah. Menene Yesu zai yi? Sa’ad da aka kawar da dutsen, Yesu ya yi addu’a da babbar murya ga Jehovah. Sai Yesu ya ce da babbar murya: “Li’azaru, ka fito!” Zai fito ne? Zai iya fitowa?—

Za ka iya ka tashi mutumin da yake barci?— E, idan ka yi kira da babbar murya, zai tashi. Amma za ka iya ka tashi mutumin da yake barcin mutuwa?— A’a. Ko yaya ƙarfin yadda ka yi kira, wanda ya mutu ba zai ji ba. Babu abin da kai ko ni ko kuma wani mutum yau a duniya zai iya yi domin ya tashi matacce.

Menene Yesu ya yi wa Li’azaru?

Amma Yesu dabam ne. Yana da iko na musamman daga wurin Allah. Saboda haka, da Yesu ya kira Li’azaru, abin mamaki ya faru. Mutumin da kwanansa huɗu da mutuwa ya fito daga kabari! An mai da masa rai! Zai iya numfashi ya yi tafiya ya yi magana kuma! Hakika, Yesu ya ta da Li’azaru daga matattu.—Yohanna 11:1-44.

Ka yi tunani game da shi: Menene ya faru da Li’azaru sa’ad da ya mutu? Wani ɓangarensa—kurwa ko kuma ruhu—ya bar jikinsa ne ya je ya zauna a wani wuri? Li’azaru ya je sama ne? Yana raye ne a waɗannan kwanaki huɗu tare da Allah da kuma mala’iku masu tsarki?—

A’a. Ka tuna Yesu ya ce Li’azaru yana barci. Yaya kake sa’ad da kake barci? Sa’ad da kake barci mai zurfi, ka san abin da yake faruwa ne?— Kuma sa’ad da ka farka, ba za ka san ko barcin awa nawa ka yi ba sai ka duba agogo.

Haka yake da mutane da suka mutu. Ba su san kome ba. Ba sa jin kome. Kuma ba za su iya yin kome ba. Haka ya faru da Li’azaru sa’ad da ya mutu. Mutuwa kamar barci ne mai zurfi da mutum ba zai tuna kome ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Matattu ba su san kome ba.”—Mai-Wa’azi 9:5, 10.

Yaya yanayin Li’azaru yake sa’ad da ya mutu?

Ka yi tunanin wannan ma: Idan Li’azaru yana sama a kwanaki huɗun, da ba zai faɗi wani abu ba ne game da sama?— Kuma da yana sama ne, da Yesu zai mai da shi duniya daga wannan wurin mai ban sha’awa?— A’a!

Duk da haka, mutane da yawa sun ce muna da kurwa, kuma sun ce kurwar tana rayuwa bayan jiki ya mutu. Sun ce kurwar Li’azaru tana da rai a wani wuri. Amma Littafi Mai Tsarki bai faɗi haka ba. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya halicci mutum na farko Adamu “rayayye mai rai.” Adamu kurwa ne. Kuma Littafi Mai Tsarki ya ce sa’ad da Adamu ya yi zunubi, ya mutu. Ya zama “gawa,” kuma ya koma turɓaya da aka yi shi. Kuma Littafi Mai Tsarki ya ce ’ya’yan Adamu sun gaji zunubi da mutuwa.—Farawa 2:7; 3:17-19; Litafin Lissafi 6:6; Romawa 5:12.

Saboda haka, ba mu da kurwa da ta bambanta daga jikin mutum. Kowannenmu kurwa ne. Kuma tun da mutane sun gaji zunubi daga mutum na fari, Adamu, Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Mai-rai da ya yi zunubi, shi za ya mutu.’—Ezekiel 18:4.

Me ya sa babu dalilin jin tsoron matattu?

Wasu mutane suna tsoron matattu. Ba za su iya zuwa kusa da kabari ba domin suna tsammanin matattu suna da kurwa da take dabam daga jiki da za ta iya yi musu lahani. Amma mataccen mutum zai iya yi wa wanda yake da rai lahani ne?— Ba zai iya ba.

Wasu mutane ma sun gaskata cewa matattu za su iya ziyartar masu rai cikin ruhu. Saboda haka, suke ajiye abinci wa matattu. Mutane da suke yin haka ba su yarda da abin da Allah ya ce ba game da matattu. Idan mun gaskata da abin da Allah ya ce, ba za mu ji tsoron matattu ba. Kuma idan da gaske muna godiya ga Allah domin rai, za mu nuna haka ta wurin yin abin da Allah ya yarda da shi.

Amma kana iya mamaki: ‘Shin Allah zai kawo yara ne da suka mutu su sake rayuwa? Yana so ya yi haka kuwa?’ Bari mu yi magana game da wannan a gaba.

Bari mu ƙara karanta yanayin matattu da kuma game da mutum mai rai [kurwa] a Zabura 115:17 (113:17, “Dy”); 146:3, 4 (145:3, 4, “Dy”); 146:3, 4; da kuma Irmiya 2:34.