Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 28

Yadda Za Mu San Wanda Za Mu Yi Wa Biyayya

Yadda Za Mu San Wanda Za Mu Yi Wa Biyayya

WANI lokaci yana da wuya mu san wanda za mu yi wa biyayya. Mamarka ko Babanka zai ce maka ka yi wani abu. Amma malaminka ko kuma ɗan sanda zai ce maka ka yi wani abu dabam. Idan hakan ya faru, wanene cikinsu za ka yi wa biyayya?—

Da farko a wannan littafi, a Babi na 7, mun karanta Afisawa 6:1-3 daga Littafi Mai Tsarki. A wajen ya ce yara su yi wa iyayensu biyayya. “Ku yi biyayya da waɗanda suka haife ku cikin Ubangiji,” nassi ya ce. Ka san abin da ake nufi da “cikin Ubangiji”?— Iyaye da suke cikin Ubangiji suna koya wa yaransu su yi biyayya da dokokin Allah.—Tafiyar tsutsa tamu ce.

Amma wasu manyan mutane ba su gaskata da Jehovah ba. To, idan wani cikinsu ya ce daidai ne a yi satar amsa a jarrabawa na makaranta ko kuma a ɗauki wani abu a kanti ba tare da an biya ba fa? Daidai ne yaro ya yi cuta ko kuma ya yi sata?—

Ka tuna, Sarki Nebuchadnezzar ya taɓa ba da umurni cewa kowa ya bauta wa gunkinsa na zinariya da ya kafa. Amma Shadrach, Meshach, da kuma Abednego ba su bauta masa ba. Ka san abin da ya sa?— Domin Littafi Mai Tsarki ya ce Jehovah ne kawai mutane za su bauta wa.—Fitowa 20:3; Matta 4:10.

Menene Bitrus yake gaya wa Kayafa?

Bayan da Yesu ya mutu, an kawo manzanninsa gaban Majalisa, babban kotun addini na Yahudawa. Babban Firist Kayafa ya ce: “Muka dokace ku da ƙarfi, kada ku koyar cikin wannan suna [Yesu]: ga shi kuwa kun gama Urushalima da koyarwarku.” Me ya sa manzannin ba su yi wa Majalisar biyayya ba?— Bitrus da yake magana ga dukan manzannin ya ce wa Kayafa: “Dole mu yi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 5:27-29.

A lokacin, shugabannin addini na Yahudawa suna da iko sosai. Ƙasarsu tana ƙarƙashin sarautar gwamnatin Romawa. Shugaban wannan gwamnatin ana kiransa Kaisar. Ko da yake Yahudawan ba sa son Kaisar ya yi sarauta, gwamnatin Roma ta yi wa mutanen abubuwa da yawa masu kyau. Kuma gwamnatoci a yau suna yin abubuwa da yawa masu kyau ga talakawansu. Ka san wasu cikin waɗannan abubuwa?—

Gwamnatoci suna gyara hanya domin tafiya, suna biyan ’yan sanda da kuma masu kashe gobara su kāre mu. Wataƙila kuma sun kafa makaranta ga yara da kuma kula da lafiyar tsofaffi. Gwamnati tana kashe kuɗi wajen yin waɗannan abubuwa. Ka san inda gwamnati take samun kuɗi?— Daga wajen mutane ne. Kuɗin da mutane suke biyan gwamnati ana kiransa haraji.

Lokacin da Babban Malami yake duniya, Yahudawa da yawa ba sa so su biya gwamnatin Roma haraji. Wata rana sai firistocin suka yi hayar mutane su yi wa Yesu tambaya domin su saka shi cikin masifa. Tambayar ita ce, ‘Ya kamata ne mu bai wa Kaisar haraji, ko bai kamata ba?’ Wannan tambaya ce ta wayo. Idan Yesu ya ce, ‘E, dole ne ku biya haraji,’ yawancin Yahudawan ba za su so abin da ya ce ba. Amma Yesu ba zai ce, ‘A’a, kada ku biya haraji ba.’ Ba daidai ba ne ka faɗi haka.

To, menene Yesu ya yi? Yesu ya ce: ‘Ku nuna mini sule.’ Da suka ba shi guda, Yesu ya tambaye su: ‘Hoto da sunan waye ne a kai?’ Mutanen suka ce: “Kaisar.” Sai Yesu ya ce: “Abin da ke na Kaisar fa, ku bayar ga Kaisar; na Allah kuwa ku bayar ga Allah.”—Luka 20:19-26.

Yaya Yesu ya amsa tambayar wayo ta waɗannan mutane?

Babu wanda ya ga wani laifi a wannan amsar. Idan Kaisar yana yi wa mutane abubuwa, daidai ne a yi amfani da kuɗi da Kaisar ya yi a biya shi domin waɗannan abubuwa. A wannan hanyar, Yesu ya nuna cewa daidai ne a biya haraji ga gwamnati domin taimakon da muke samu.

Yanzu, ba ka kai ba tukun da za ka biya haraji. Amma da akwai abin da za ka bai wa gwamnati. Ka san abin nan?— Biyayya da dokokin gwamnati. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Ka yi biyayya ga masu iko.’ Waɗannan masu iko su ne waɗanda suke da iko a cikin gwamnati. Allah ne ya ce ya kamata mu yi biyayya ga dokokin gwamnati.—Romawa 13:1, 2.

Wataƙila doka ce da ta ce kada ka jefar da takarda ko kuma wasu abubuwa a kan titi. Ya kamata ka kiyaye wannan dokar ne?— E, Allah yana so ka yi biyayya. Ya kamata ka yi biyayya ga ’yan sanda ma?— Gwamnati tana biyan ’yan sanda su kāre mutane. Yi musu biyayya daidai yake da yi wa gwamnati biyayya.

Saboda haka, idan kana so ka ketare titi sai ɗan sanda ya ce maka “Ka tsaya!” me ya kamata ka yi?— Idan wasu suka ruga suka ƙetara, ya kamata kai ma ka yi haka ne?— Ya kamata ka tsaya, ko kai ne kawai kake jira. Allah ya ce ka yi biyayya.

Wataƙila da masifa a unguwar, ɗan sanda zai iya cewa: “Kada kowa ya fito kan titi. Kada ka fita waje.” Amma wataƙila ka ji kuwwa ka yi tunani me yake faruwa ne haka. Ya kamata ne ka fita waje domin ka gani?— Wannan zai kasance biyayya ne ga “ikon masu-mulki”?—

A wurare da yawa, gwamnati kuma ta gina makarantu, kuma tana biyan malamai. Kana tsammani cewa Allah yana so ka yi wa malami biyayya?— Ka yi tunaninsa. Gwamnati tana biyan malami ya koyar, kamar yadda take biyan ɗan sanda ya kāre mutane. Saboda haka, yin biyayya ga ɗan sanda ko kuma malami daidai yake da yin biyayya ga gwamnati.

Me ya sa za mu yi wa ɗan sanda biyayya?

Amma idan malami ya ce sai ka yi sujjada ga wani gunki fa? To, menene za ka yi?— Yahudawa uku ba su yi sujjada ga gunkin ba ko da yake Sarki Nebuchadnezzar ya ce musu su yi. Ka tuna da abin da ya sa?— Domin ba sa son su yi wa Allah rashin biyayya.

Marubucin tarihi mai suna Will Durant ya rubuta game da Kiristoci na farko ya ce ‘babban amincinsu ba ga Kaisar ba ne.’ A’a, na Jehovah ne! Saboda haka, ka tuna cewa Allah ne ya kamata ya kasance na farko a rayuwarmu.

Muna yi wa gwamnati biyayya domin abin da Allah yake so mu yi ne. Amma idan aka ce mu yi abin da Allah ya ce kada mu yi, me ya kamata mu ce?— Ya kamata mu faɗi abin da manzanni suka ce ga babban firist: “Dole sai mu fi biyayya ga Allah da mutane.”—Ayukan Manzanni 5:29.

An koyar da daraja doka a Littafi Mai Tsarki. Ka karanta abin da yake rubuce a Matta 5:41; Titus 3:1; da kuma 1 Bitrus 2:12-14.