Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 47

Ta Yaya Za Mu Sani Cewa Armageddon Ya Yi Kusa

Ta Yaya Za Mu Sani Cewa Armageddon Ya Yi Kusa

KA SAN abin da alama take nufi, ko ba ka sani ba?— A Babi na 46 mun karanta game da alama da Allah ya bayar cewa ba zai sake halaka duniya da ambaliya ba. Har ila, manzanni sun nemi sanin alama na lokacin da Yesu zai dawo da kuma sa’ad da ƙarshen duniya, ko kuma wannan zamanin ya yi kusa.—Matta 24:3.

Tun da Yesu zai kasance a sama ba za a iya ganinsa ba, ana bukatar alama da mutane za su gani da za ta nuna cewa ya riga ya fara sarauta. Saboda haka, Yesu ya faɗi game da abubuwan da almajiransa za su lura da su a nan duniya. Sa’ad da waɗannan abubuwa suka faru, zai nuna cewa ya riga ya dawo kuma ya fara Sarauta a sama.

Domin ya koya wa almajiransa muhimmancin yin tsaro, Yesu ya gaya musu: “Ku lura da itacen ɓaure da dukan itatuwa: sa’ad da suna tohuwa, ku kan gani, kuna sani kuma cikin rayukanku bazara ta kusa.” Ka san yadda za ka gane idan bazara ta yi kusa. Za ka iya ganewa sa’ad da Armageddon ya yi kusa sa’ad da ka ga abubuwa da Yesu ya faɗa suna faruwa.—Tafiyar tsutsa tamu ce; Luka 21:29, 30.

Wane darasi Yesu yake koyarwa sa’ad da ya yi maganar ɓaure?

A wannan shafi da na gaba, za mu ga hotuna na abubuwa da Yesu ya ce za su ba da alamar cewa Mulkin Allah ya yi kusa. Sa’ad da dukan waɗannan abubuwa suke faruwa, Mulkin Allah da Kristi ne Sarki zai halaka dukan gwamnatoci, kamar yadda muka karanta a Babi na 46.

Ka dubi hotunan waɗannan shafuffuka biyu kafin wannan a hankali, za mu yi magana a kansu. A Matta 24:6-14 da Luka 21:9-11, za mu iya karanta game da abubuwa da ake gani a waɗannan hotunan. Ka lura kuma da waɗannan ƙananan lamba da take kan kowanne hoto. Irin wannan lambar ce aka fara kowanne sakin layi da ya kwatanta hoton. Bari mu ga ko ɓangarori da yawa na wannan alama da Yesu ya bayar suna cika a yau.

(1) Yesu ya ce: “Kuma za ku ji labarin yaƙoƙi da zizar yaƙi: . . . al’umma za ta tasam ma al’umma, mulki kuma za ya tasam ma mulki.” Ka taɓa jin labarin yaƙi?— An yi yaƙin duniya na fari daga shekara ta 1914 zuwa 1918, sai kuma yaƙin duniya na biyu daga shekara ta 1939 zuwa 1945. Ba a taɓa yin yaƙin duniya ba kafin wannan lokacin! A yanzu ana yaƙe-yaƙe a dukan duniya. Kowacce rana mutane suna jin labaran yaƙi a telibijin, a rediyo, kuma muna karantawa a jarida.

(2) Yesu ya ce: “Za a yi yunwa . . . wurare dabam dabam.” Kamar yadda ka sani ba kowa ba ne yake da isashen abinci. Kowacce rana dubban mutane suna mutuwa domin ba su da isashen abinci.

(3) Yesu ya ce: “A wurare dabam dabam kuma za a yi annoba.” Ka san ko mecece annoba?— Cuta ce da take kashe mutane da yawa. Wata annoba mai girma da ake kira Spanish flu ta kashe kusan mutane miliyan 20 a cikin shekara guda. A zamaninmu, wataƙila mutane fiye da haka za su mutu daga ciwon ƙanjamau. Da akwai kuma ciwon daji, ciwon zuciya, da kuma wasu cututtuka da suke kashe dubban mutane kowacce shekara.

(4) Yesu ya ba da wani ɓangare na alamar yana cewa: “Za a yi . . . raye-rayen duniya wurare dabam dabam.” Ka san ko menene raye-rayen duniya?— Raye-rayen duniya zai sa ƙasa ta riƙa girgiza. Gidaje za su rurrushe, sau da yawa kuma mutane suna mutuwa. Tun daga shekara ta 1914, an yi girgizar ƙasa da yawa kowacce shekara. Ka taɓa ji game da girgizar ƙasa?—

(5) Yesu ya ce wata alama kuma ita ce ‘mugunta za ta yawaita.’ Abin da ya sa ke nan ake yawan sata da kuma faɗa. Mutane a ko’ina suna tsoro kada wani ya zo sata a gidansu. Ba a taɓa lokaci da yin laifi da mugunta suka yi yawa ba a dukan ɓangarorin duniya kamar yadda yake yanzu.

(6) Yesu ya ambata ɓangare mai muhimmanci na alamar sa’ad da ya ce: “Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida ga dukan al’ummai; sa’annan matuƙa za ta zo.” (Matta 24:14) Idan ka yarda da “wannan bishara,” to, ya kamata ka gaya wa wasu game da ita. Ta wannan hanyar za ka saka hannu wajen cika wannan alamar.

Wasu mutane za su ce abin da Yesu ya faɗa sun saba suna faruwa. Amma waɗannan abubuwa duka ba su taɓa faruwa ba a ɓangarorin duniya da yawa a lokaci guda. To, ka fahimci abin da alama take nufi?— Wannan yana nufi ne cewa idan muka ga dukan waɗannan abubuwa suna faruwa, ba zai daɗe ba wannan muguwar duniya za a sake ta da sabuwar duniya ta Allah.

Sa’ad da Yesu ya ba da wannan alamar, ya yi magana kuma game da lokaci mai muhimmanci na shekara. Ya ce: “Ku yi addu’a fa kada gudunku ya zama a cikin damina.” (Matta 24:20) Me kake tsammani yake nufi da wannan?—

Idan mutum zai guje wa bala’i a lokacin damina, lokaci ne da yanayi zai zama da wuya ko kuma zai kasance da haɗari a yi tafiya, me zai faru?— Idan ya tsira ma, zai kasance da wuya ƙwarai. Ba zai zama abin tausayi ba, in mutum ya mutu a cikin haɗarin domin ya shagala ƙwarai yana yin wasu abubuwa bai fara tafiyarsa da wuri ba?—

Sa’ad da Yesu ya yi magana game da gudu a lokacin damina, wane darasi yake koyarwa?

Ka fahimci abin da Yesu yake nufi da ya yi magana game da jira har sai lokacin damina a gudu?— Yana gaya mana ne cewa da yake mun san cewa Armageddon ya yi kusa, kada mu ɓata lokaci wajen nuna cewa muna ƙaunar Allah ta wajen bauta masa. Idan muka ɓata lokaci za mu makara. Sai mu zama kamar waɗanda suke zamanin Ambaliya da suka ji gargaɗin Nuhu amma suka ƙi shiga cikin jirgi.

Bari yanzu, mu yi magana game da abin da zai faru sa’ad da babban yaƙin Armageddon ya ƙare. Za mu koyi abin da Allah ya shirya wa dukan waɗanda suke ƙaunarsa kuma suke bauta masa a yau.

Waɗannan nassosi suna nuna cewa Armageddon ya yi kusa: 2 Timothawus 3:1-5 da kuma 2 Bitrus 3:3, 4.