Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 25

Wadanda Suke Yin Mugun Abu Za Su Iya Canjawa Kuwa?

Wadanda Suke Yin Mugun Abu Za Su Iya Canjawa Kuwa?

BA ZAI yi kyau ba ne idan kowa yana abin da yake da kyau?— Amma babu mutumin da yake yin abin da yake da kyau kullum. Ka san abin da ya sa dukanmu wani lokaci muke yin abin da ba shi da kyau ko da yake muna so mu yi abin da yake da kyau?— Domin dukanmu an haife mu da zunubi. Amma wasu mutane suna yin munanan abubuwa da yawa. Ba sa son wasu mutane, kuma suna cutarsu da gangan. Kana tsammanin za su iya canjawa su yi abin da yake da kyau?—

Ka ga wannan saurayin da yake kula da kayan waɗannan da suke jifar Istifanus. Sunansa na Ibrananci Shawulu ne, amma sunansa na Romanci kuma Bulus. Yana farin ciki an kashe Istifanus, wanda almajirin Babban Malami ne. Bari mu ga abin da ya sa Shawulu ya yi irin wannan abin da ba shi da kyau.

Shawulu yana addini ne na Yahudawa waɗanda ake ce da su Farisawa. Farisawan suna da Kalmar Allah, amma sun mai da hankali sosai ga koyarwar wasu shugabannin addininsu. Wannan ya sa Shawulu yake munanan abubuwa.

Sa’ad da aka kama Istifanus a Urushalima, Shawulu yana wajen. An kai Istifanus kotu, inda wasu cikin alƙalan Farisawa ne. Ko da yake sun faɗi miyagun abubuwa game da Istifanus bai tsorata ba. Ya yi magana kuma ya yi wa alƙalan wa’azi game da Jehovah Allah da kuma Yesu.

Amma waɗannan alƙalan ba sa son abin da suka ji ba. Sun riga sun sani game da Yesu. Hakika, ba da daɗewa ba suka sa aka kashe Yesu. Amma daga baya, Jehovah ya mayar da Yesu zuwa sama. Yanzu, maimakon su canja ra’ayinsu, alƙalan suka yi hamayya da almajiran Yesu.

Alƙalan suka ɗauki Istifanus suka fitar da shi bayan gari. Suka buge shi ya faɗi, suka jejjefe shi da duwatsu. Kuma Shawulu yana wajen yana kallo, kamar yadda kake gani a wannan hoton. Yana tsammanin daidai ne a kashe Istifanus.

Me ya sa Shawulu ya yi tsammanin cewa daidai ne a kashe Istifanus?

Ka san abin da ya sa Shawulu ya yi tunani haka?— Dukan rayuwarsa Shawulu Bafarisi ne, kuma ya gaskata cewa koyarwar Farisawan gaskiya ce. Yana kula da waɗannan mutane, kuma yana bin misalinsu.—Ayukan Manzanni 7:54-60.

Bayan an kashe Istifanus, menene Shawulu ya yi?— Ya yi ƙoƙarin ya kawar da almajiran Yesu! Yana zuwa gidajensu ya jawo maza da mata waje. Kuma ya sa a jefa su a kurkuku. Da yawa cikin almajiran sun bar Urushalima, amma ba su daina wa’azi ba game da Yesu.—Ayukan Manzanni 8:1-4.

Wannan ya sa Shawulu ya sake tsanan almajiran. Saboda haka ya je wajen Babban Firist Kayafa ya karɓi izni ya kama Kiristoci a birnin Dimashƙa. Shawulu yana so ya kawo su fursunoni zuwa Urushalima domin a hore su. Amma sa’ad da yake kan hanyarsa ta zuwa Dimashƙa abin mamaki ya faru.

Waye yake magana da Shawulu, kuma menene ya aiki Shawulu ya yi?

Haske ya haskaka daga sama kuma murya ta ce: “Shawulu, Shawulu, don me ka ke tsanantata?” Yesu ne yake magana daga sama! Wutar tana da haske sosai har ta makantar da Shawulu, saboda haka mutane da suke tare da Shawulu suka ja masa gora zuwa Dimashƙa.

Bayan kwana uku Yesu ya bayyana a wahayi ga ɗaya daga cikin almajiransa a Dimashƙa mai suna Hananiya. Yesu ya gaya wa Hananiya ya ziyarci Bulus, ya kawar masa da makantarsa, kuma ya yi masa magana. Sa’ad da Hananiya ya yi masa magana, Shawulu ya yarda da gaskiya game da Yesu. Ya fara gani kuma. Dukan hanyar rayuwarsa ta canja, ya zama bawan Allah mai aminci.—Ayukan Manzanni 9:1-22.

Yanzu ka ga abin da ya sa Shawulu ya yi abin da ba shi da kyau?— Domin an koya masa abubuwa da ba su da kyau ne. Ya bi mutane da ba su da aminci ga Allah. Kuma ya kasance cikin rukunin mutane da suke ɗora ra’ayin mutane a gaba da Kalmar Allah. Amma me ya sa Shawulu ya canja rayuwarsa ya fara yin abin da yake da kyau, ko da yake wasu Farisawa suka ci gaba da yin yaƙi da Allah?— Domin Shawulu bai ƙi gaskiya ba ne da gaske. Saboda haka, da aka nuna masa abin da yake da kyau, yana shirye ya yi shi.

Ka san abin da Shawulu ya zama daga baya?— Hakika, an san shi da manzo Bulus, manzon Yesu. Kuma ka tuna, Bulus ya rubuta littattafai na Littafi Mai Tsarki fiye da kowane mutum.

Da akwai mutane da yawa kamar Bulus da za su iya canjawa. Amma ba shi da sauƙi domin akwai wanda yake aiki sosai ya sa mutane su yi abin da ba shi da kyau. Ka san kowanene ne wannan?— Yesu ya yi magana game da shi sa’ad da Yesu ya bayyana ga Shawulu a hanyar zuwa Dimashƙa. A nan Yesu ya yi magana da Shawulu daga sama ya ce: ‘Na aike ka ka buɗe idanun mutane, ka juyo su daga duhu zuwa haske daga ikon Shaiɗan zuwa Allah.’—Ayukan Manzanni 26:17, 18.

Hakika, Shaiɗan Iblis yana ƙoƙari ya sa kowa ya yi abin da ba shi da kyau. Wani lokaci yana yi maka wuya ka yi abin da yake da kyau?— Yana faruwa da dukanmu. Shaiɗan yana sa ya yi wuya. Amma da akwai wani dalili kuma da ya sa ba shi da sauƙi mu yi abin da yake da kyau. Ka san dalilin?— Domin an haife mu da zunubi.

Zunubi ne yake sa sau da yawa ya kasance da sauƙi mu yi abin da yake da muni fiye da abin da yake da kyau. Saboda haka, me muke bukata mu yi?— Hakika, dole ne mu yi kokawa domin mu yi abin da yake da kyau. Sa’ad da muka yi haka, za mu tabbata cewa Yesu wanda yake ƙaunarmu zai taimake mu.

Sa’ad da Yesu yake duniya, ya yi ƙaunar mutane da suke yin mugun abu amma waɗanda suka canja. Ya sani cewa yana da wuya su yi canji. Alal misali, da akwai mata da suke kwana da maza da yawa. Wannan hakika ba shi da kyau. Littafi Mai Tsarki ya kira waɗannan mata kilakai ko kuma karuwai.

Me ya sa Yesu ya gafarta wa wannan mata da ta yi abin da ba shi da kyau?

Wata rana, wata mace irin wannan ta ji game da Yesu, kuma ta zo wajen da yake a gidan Bafarisi. Ta zuba mai a sawun Yesu kuma ta share su daga sawunsa da gashinta. Ta yi kukan zunubinta, saboda haka, Yesu ya gafarta mata. Amma Bafaristin bai yi tsammanin ya kamata a gafarta mata ba.—Luka 7:36-50.

Ka san abin da Yesu ya ce game da wasu Farisawa?— Ya gaya musu: ‘Karuwai su za su riga ku shiga mulkin Allah.’ (Matta 21:31) Yesu ya faɗi haka domin karuwan sun gaskata da shi, kuma sun canja hanyoyinsu da ba shi da kyau. Amma Farisawan suka ci gaba da yin miyagun abubuwa ga almajiran Yesu.

Saboda haka, idan Littafi Mai Tsarki ya ce abin da muke yi ba shi da kyau, ya kamata mu canja. Kuma idan muka koyi abin da Jehovah yake so mu koya, ya kamata mu yi ɗokin yin haka. Jehovah zai yi farin ciki da mu kuma ya ba mu rai madawwami.

Domin ya taimake mu mu guji yin abubuwa da suke munana, bari mu karanta tare Zabura 119:9-11 (118:9-11, “Dy”); Misalai 3:5-7; da kuma 12:15.