Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 5

“Wannan Dana Ne”

“Wannan Dana Ne”

IDAN yara suka yi abin da yake da kyau, waɗanda suke kula da su suna yin farin ciki. Idan yarinya ta yi abin da yake daidai, babanta zai yi farin ciki ya gaya wa wasu: “Wannan ’yata ce.” Ko kuma idan yaro ya yi abin da yake da kyau, baban zai yi murna ya ce: “Wannan ɗana ne.”

Yesu koyaushe yana yin abin da yake faranta wa Ubansa rai. Saboda haka Ubansa yake alfahari da shi. Ka tuna abin da Uban Yesu ya yi wata rana sa’ad da Yesu yake tare da mabiyansa guda uku?— E, Allah ya yi magana daga sama ya gaya musu: “Wannan Ɗana ne ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai.”—Matta 17:5.

Yesu yana murna ko da yaushe ya yi abin da yake faranta wa Ubansa rai. Ka san abin da ya sa? Domin yana ƙaunar Ubansa da gaske. Idan mutum yana yin abu ne domin kawai dole ne ya yi, wannan zai kasance da wuya. Amma sa’ad da yake yi da yardar rai, haka sai ya zama da sauƙi. Ka san abin da ake nufi da yardar rai?— Yana nufin son yin abu da gaske.

Kafin Yesu ya zo duniya ma, yana shirye ya yi dukan abin da Ubansa ya ce ya yi. Wannan domin yana ƙaunar Ubansa ne, Jehovah Allah. Yesu yana da matsayi a sama tare da Ubansa. Amma Allah yana da aiki na musamman da Yesu zai yi. Domin ya yi wannan aiki, dole ne Yesu ya bar sama. Dole ne a haife shi jariri a duniya. Yesu yana son ya yi haka domin Jehovah yana so ya yi hakan.

Menene mala’ika Jibra’ilu ya gaya wa Maryamu?

Domin a haife shi jariri a duniya, Yesu yana bukatar uwa. Ka san ko wacece ita?— Sunanta Maryamu. Jehovah ya aiko mala’ikansa Jibra’ilu ya yi magana da Maryamu. Jibra’ilu ya gaya mata cewa za ta haifi ɗa. Za a raɗa wa yaron suna Yesu. To, wa zai zama baban yaron?— Mala’ikan ya ce Baban yaron Jehovah Allah ne. Abin da ya sa ke nan ake kiransa Ɗan Allah.

Yaya kake tsammani Maryamu ta ji game da wannan?— Ta ce, “Ba na so in zama mamar Yesu”? A’a, Maryamu tana shirye ta yi abin da Allah yake so. Amma ta yaya za a haifi Ɗan Allah ya zama jariri a duniya? Ta yaya haihuwar Yesu ta bambanta da haihuwar dukan wasu jarirai? Ka sani?—

Allah ya yi iyayenmu na fari, Adamu da Hauwa’u, su sadu da juna ta hanya mai ban mamaki. Bayan haka, jariri zai fara girma a cikin mamarsa. Mutane sun ce wannan mu’ujiza ce! Na tabbata za ka yarda.

A yanzu Allah ya yi abin da ya fi ma ban al’ajabi. Ya ɗauki ran Ɗansa daga sama ya saka shi a cikin Maryamu. Allah bai taba yin haka ba a dā, kuma bai sake yinsa ba tun daga lokacin. Domin wannan mu’ujiza, Yesu ya fara girma a cikin Maryamu kamar yadda wasu jarirai suke girma a cikin mamarsu. Bayan haka, Maryamu ta auri Yusufu.

Da lokaci ya yi a haifi Yesu, Yusufu da Maryamu suka ziyarci Baitalami. Amma ta cika da mutane. Babu ko ɗaki ga Maryamu da Yusufu, saboda haka, ya zama dole su zauna a wurin da ake ajiye dabbobi. A nan Maryamu ta haihu, kuma an ajiye Yesu a kan sakarkari, kamar yadda kake gani a nan. Sakarkari wuri ne da ake ajiye abincin shanu da kuma wasu dabbobi.

Me ya sa aka saka Yesu a sakarkari?

Abin mamaki ya faru a daren da aka haifi Yesu. A kusa da Baitalami, mala’ika ya bayyana ga makiyaya. Ya gaya musu cewa Yesu mutum ne mai muhimmanci. Mala’ikan ya ce: ‘Ga shi, ina gaya muku bishara da zai sa mutane farin ciki. A yau an haifa muku wani da zai ceci mutane.’—Luka 2:10, 11.

Wace bishara ɗaya cikin waɗannan mala’iku ya gaya wa makiyaya?

Mala’ikan ya gaya wa makiyayan cewa za su sami Yesu a Baitalami, yana kwance cikin sakarkari. Sai, farat ɗaya, wasu mala’iku a sama suka haɗa kai da mala’ikan wajen yabon Allah. “Alhamdu ga Allah,” mala’ikun suka rera, “a duniya kuma salama wurin mutanen da ya ke murna da su sarai.”—Luka 2:12-14.

Sa’ad da mala’ikun suka tafi, makiyayan suka je Baitalami suka sami Yesu. A nan suka gaya wa Yusufu da Maryamu dukan kyawawan abubuwa da suka ji. Za ka iya ƙaga irin farin cikin Maryamu da take shirye ta zama mamar Yesu?

Daga baya, Yusufu da Maryamu suka ɗauki Yesu zuwa birnin Nazarat. A nan Yesu ya girma. Sa’ad da ya girma, ya fara aikinsa mai girma na koyarwa. Wannan shi ne ɓarin aiki da Jehovah Allah yake so Ɗansa ya yi a duniya. Yesu yana shirye ya yi wannan aikin domin Yesu yana ƙaunar Ubansa na samaniya ƙwarai.

Kafin Yesu ya fara aikinsa na Babban Malami, Yohanna Mai Baftisma ya yi masa baftisma a Kogin Urdun. Wani abin mamaki ya faru! Da Yesu yake fitowa daga cikin ruwan, Jehovah ya yi magana daga sama, yana cewa: “Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena wanda raina ya ji daɗinsa sarai.” (Matta 3:17) Kana jin daɗi idan iyayenka suka ce maka suna ƙaunarka?— Za mu tabbata cewa Yesu ma ya ji daɗi.

Yesu koyaushe yana yin abin da yake daidai. Ba ya ɓoye halinsa. Bai gaya wa mutane ba cewa shi Allah ne. Mala’ika Jibra’ilu ya riga ya gaya wa Maryamu cewa za a kira Yesu Ɗan Allah. Yesu kansa ya ce shi ɗan Allah ne. Kuma bai gaya wa mutane ba cewa yana da sani fiye da Ubansa. Ya ce: “Uba ya fi ni girma.”—Yohanna 14:28.

Har a sama, sa’ad da Uban Yesu ya ba shi aiki ya yi, Yesu ya yi. Bai ce zai yi ba amma sai ya je ya yi wani abu dabam. Yana ƙaunar Ubansa. Saboda haka ya saurari abin da Ubansa ya ce. Sai kuma sa’ad da Yesu ya zo duniya, ya yi abin da Ubansa na samaniya ya aiko shi ya yi. Bai yi amfani da lokacinsa yana yin wani abu dabam ba. Babu shakka da Jehovah yake farin ciki da Ɗansa!

Mu ma muna so mu faranta wa Jehovah rai, ba ma so ne?— To, dole ne mu nuna cewa muna sauraron Allah da gaske, kamar yadda Yesu ya yi. Allah ya yi magana da mu ta wajen Littafi Mai Tsarki. Ba zai yi daidai ba mu nuna muna sauraron Allah amma sai mu gaskata kuma mu yi abubuwa da suka saɓa wa Littafi Mai Tsarki, zai yi kyau ne?— Kuma ka tuna cewa, za mu yi farin cikin faranta masa rai idan muna ƙaunarsa.

Ka karanta waɗannan ayoyi na Littafi Mai Tsarki da suka nuna abin da muke bukatar mu sani kuma gaskata game da Yesu: Matta 7:21-23; Yohanna 4:25, 26; da kuma 1 Timothawus 2:5, 6.