Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 36

Waye Za A Ta Da Daga Matattu? A Ina Za Su Zauna?

Waye Za A Ta Da Daga Matattu? A Ina Za Su Zauna?

A BABI biyu na baya, mutane nawa ne aka tashe su daga matattu da muka karanta game da su?— Mutane biyar ne. Yara nawa ne a cikinsu?— Uku. Kuma na huɗun an kira shi saurayi. Menene kake tsammani wannan ya nuna?—

Wannan ya nuna cewa Allah yana ƙaunar matasa. Amma kuma zai tashi mutane da yawa. Allah zai tashi waɗanda suka yi abin da yake da kyau ne kawai?— Ƙila haka kake tsammani. Amma, mutane da yawa ba su koyi gaskiya game da Jehovah Allah ba da kuma Ɗansa. Saboda haka, suna yin abin da yake mugu domin ba a koya musu abin da yake da kyau ba. Kana tsammanin Allah zai tashe irin waɗannan mutane?—

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Za a yi tashin matattu, na masu-adalci da na marasa-adalci.” (Ayukan Manzanni 24:15) Me ya sa za a tashi marasa adalci, ko kuma waɗanda ba su yi abin da yake da kyau ba?— Domin ba su sami zarafin su koyi game da Jehovah da kuma abin da yake so mutane su yi ba ne.

Me ya sa Allah zai tashe wasu waɗanda ba su yi abin da yake da kyau ba?

Yaushe ne kake tsammanin za a tashi mutane daga matattu?— Ka yi tunanin sa’ad da Li’azaru ya mutu kuma Yesu ya yi wa yayarsa Martha alkawari: “Ɗan’uwanki za ya tashi.” Martha ta amsa ta ce: “Na sani za ya tashi kuma a cikin tashin matattu a kan rana ta ƙarshe.” (Yohanna 11:23, 24) Menene Martha take nufi sa’ad da ta ce Li’azaru zai tashi a “rana ta ƙarshe”?—

Ina Aljannar da Yesu yake gaya wa mutumin game da ita take?

Martha ta ji alkawarin Yesu: ‘Dukan waɗanda suke cikin kabarbaru za su ji muryatasa, su fito kuma.’ (Yohanna 5:28, 29) Saboda haka, ‘rana ta ƙarshe’ ne za a ba da rai wa dukan waɗanda Allah ya tuna da su. Wannan rana ta ƙarshe ba kawai awoyi 24 ba ne. Tana da tsawon shekara dubu. Littafi Mai Tsarki ya ce, a wannan ranar ‘Allah zai yi wa mutanen duniya shari’a.’ Waɗanda zai yi wa shari’a za su haɗa da waɗanda aka tashe su daga matattu.—Ayukan Manzanni 17:31; 2 Bitrus 3:8.

Ka ga wannan za ta kasance rana ce ta farin ciki! A cikin wannan rana mai tsawon shekara dubu, miliyoyin mutane da suka mutu za a mai da musu rai. Yesu ya kira wannan wurin da za a mai da musu rai Aljanna. Bari mu ga inda Aljanna za ta kasance da kuma yadda rayuwa za ta kasance a wurin.

Awa uku kafin ya mutu a kan gungumen azaba, ya yi maganar Aljanna ga mutumin da ya ke rataye kusa da shi. An kashe mutumin domin laifin da ya yi. Amma da wannan mai laifin ya ga Yesu kuma ya ji abin da ake faɗa game da shi, ya fara yin imani da Yesu. Saboda haka, mai laifin ya ce: “Ka tuna da ni lokacinda ka shiga mulkinka.” Yesu ya amsa: “Gaskiya ina ce maka, yau kana tare da ni cikin [Aljanna].”—Luka 23:43.

Idan muka yi karatu game da Aljanna me ya kamata mu zana a zuciyarmu?

Menene Yesu yake nufi sa’ad da ya faɗi haka? Ina ne Aljanna?— Ka yi tunani game da wannan. A ina ne aljanna take da farko?— Ka tuna, Allah ya ba wa mutum na farko, Adamu, da matarsa aljanna su zauna a ciki a nan duniya. An kira ta lambun Adnin. Da akwai dabbobi a cikin wannan lambun, amma ba su yi wa kowa lahani ba. Da akwai itatuwa da yawa da ’ya’yansu masu zaƙi, da akwai kuma babban kogi. Waje ne mai kyau na zama!—Farawa 2:8-10.

Saboda haka sa’ad da muka karanta game da wannan mai laifi cewa yana cikin Aljanna, ya kamata mu zana wannan duniya ta zama wuri mai kyau domin rayuwa. Yesu zai zauna ne a nan duniya da wannan mai laifi na dā cikin Aljanna?— A’a. Ka san abin da ya sa ba zai yi haka ba?—

Domin Yesu zai zauna a sama ne yana sarauta bisa Aljanna a duniya. Saboda haka, Yesu zai kasance tare da wannan mutumin domin Yesu ne zai tashe shi daga matattu kuma ya biya masa bukatunsa. Me ya sa Yesu ya ƙyale mai laifi na dā ya zauna a cikin Aljanna?— Bari mu gani idan za mu iya samun amsa.

Kafin mai laifin ya yi wa Yesu magana, ya sani ne game da nufe-nufen Allah?— A’a, bai sani ba. Ya yi munanan abubuwa ne domin bai san gaskiya game da Allah ba. A Aljanna za a koya masa nufin Allah. A lokacin zai sami zarafin ya tabbatar da gaske cewa yana ƙaunar Allah kuma yana so ya yi nufinsa.

Dukan waɗanda aka tashe su daga matattu ne za su rayu a Aljanna a duniya?— A’a ba duka ba ne. Ka san abin da ya sa?— Domin waɗansu za a tashe su su zauna da Yesu a sama. Za su yi sarauta tare da shi bisa Aljanna a duniya. Bari mu ga yadda muka san wannan.

A daren da zai mutu, Yesu ya gaya wa manzanninsa: ‘A cikin gidan Ubana akwai wurin zama dayawa; zan tafi garin in shirya muku wuri.’ Sai Yesu ya yi musu alkawari: ‘Zan sake dawowa, in karɓe ku wurina; domin wurin da ni ke, ku zauna kuma.’—Yohanna 14:2, 3.

Ina Yesu ya tafi bayan ya tashi daga matattu?— Hakika, ya koma sama ya zauna da Ubansa. (Yohanna 17:4, 5) Saboda haka, Yesu ya yi wa manzanninsa da kuma wasu mabiyansa alkawarin zai tashe su daga matattu saboda su kasance tare da shi a sama. Menene za su yi a can tare da Yesu?— Littafi Mai Tsarki ya ce almajiransa da suke cikin “tashi na fari” za su zauna a sama kuma su yi “mulki kuma tare da shi shekara dubu.”—Ru’ya ta Yohanna 5:10; 20:6; 2 Timothawus 2:12.

Mutane nawa ne za su samu “tashi na fari” kuma su yi sarauta tare da Yesu?— Yesu ya gaya wa almajiransa: “Ku ƙaramin garke, kada ku ji tsoro; gama Ubanku yana jin daɗi shi ba ku mulkin.” (Tafiyar tsutsa tamu ce; Luka 12:32) Wannan “ƙaramin garken,” da aka tashe su su kasance tare da Yesu a Mulkin sama yana da adadi. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa an tashi ‘dubu ɗari da arba’in da huɗu’ daga duniya.—Ru’ya ta Yohanna 14:1, 3.

A ina waɗanda aka tashe su daga matattu za su zauna, kuma me za su yi?

Mutane nawa ne za su zauna a cikin Aljanna a duniya?— Littafi Mai Tsarki bai faɗa ba. Amma Allah ya gaya wa Adamu da Hauwa’u sa’ad da suke a lambun Adnin su haifi ’ya’ya su cika duniya. Amma sun kasa yin haka. Allah sai ya ga nufinsa na cika duniya da mutanen kirki ya tabbata.—Farawa 1:28; Ishaya 45:18; 55:11.

Ka yi tunanin yadda zai zama abin farin ciki a zauna a Aljanna! Dukan duniya za ta zama lambu. Za ta cika da tsuntsaye da dabbobi masu kyau da kuma itatuwa da furanni iri iri. Babu wanda zai sha azaba domin yana ciwo, kuma babu wanda zai mutu. Kowa zai zama abokin kowa. Idan mu ma muna so mu zauna a cikin Aljanna har abada, yanzu ne lokacin da ya kamata mu yi shiri.

Ka ƙara karatu game da nufin Allah domin duniya, a Misalai 2:21, 22; Mai-Wa’azi 1:4; Ishaya 2:4; 11:6-9; 35:5, 6; da kuma 65:21-24.