Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 15

Yesu “Ya Kafa Yin Gaskiya a Duniya”

Yesu “Ya Kafa Yin Gaskiya a Duniya”

1, 2. A wane lokaci ne Yesu ya fusata, kuma me ya sa?

 YESU ya fusata—da kyakkyawar hujja. Wataƙila ya yi maka wuya ka yi tunaninsa a wannan hanyar, domin mutum ne mai tawali’u. (Matiyu 21:5) Ya kasance da cikakken kame kai, domin fushinsa na adalci ne. a Amma mene ne ya sa wannan mutum mai son lumana ya fusata? Batun rashin adalci ne mai tsanani.

2 Yesu yana ƙaunar haikali da yake Urushalima a zuciyarsa. A dukan duniya shi ne kawai wuri mai tsarki da aka keɓe ga bautar Ubansa na sama. Yahudawa daga ƙasashe da yawa suna tafiya mai nisa su je bauta a wurin. Har mutane na Al’ummai masu tsoron Allah, suna zuwa farfajiyar haikalin da aka keɓe domin amfaninsu. Amma da farkon hidimarsa, Yesu ya shiga cikin filin haikalin ya ga abin da yake da ban ƙyama. Duba, wurin ya fi kama da kasuwa fiye da gidan bauta! Ya cika da dillalai da masu canja kuɗi. Amma, ina rashin adalci a nan? Ga waɗannan mutane, haikalin Allah wuri ne kawai na cutar mutane—har ma a yi musu fashi. Ta yaya?—Yohanna 2:14.

3, 4. Wace damfara ce ta haɗama take faruwa a gidan Jehobah, me Yesu ya yi ya gyara al’amura?

3 Shugabannan addini sun kafa doka cewa sai dai da wata irin saba za a biya harajin haikali. Baƙi dole su canja kuɗinsu domin su samu irin wannan saba. Saboda haka, masu canja kuɗin sun kafa teburansu har cikin haikali, suna karɓar la’ada daga kowane ciniki da aka yi. Wanda ma ya fi riba shi ne sayar da dabbobi. Baƙi waɗanda suke so su miƙa hadaya za su iya sayan dabba a cikin gari, amma ma’aikatan haikali za su iya ƙin hadayarsu cewa bai cancanta ba. Amma, abin hadaya da aka saya a nan cikin filin haikali tabbatacce ne za a karɓa. Tun da mutanen suna cikin hannunsu, wani lokaci ’yan kasuwan suna yin tsada. b Wannan ya wuce kasuwanci. Ya zama fashi!

4 Yesu ba zai ƙyale irin wannan rashin adalci ba. Wannan gidan Ubansa ne! Ya yi bulala ta igiya ya kori garken shanu da na tumaki daga haikalin. Sai ya tsallake zuwa wajen ’yan canja kuɗi ya jirkice teburansu. Ka yi tunanin tsaba suna watsewa a kan daɓen sassaƙaƙƙen duwatsu! Ya dokaci dillalan tantabaru: “Ku fitar da waɗannan daga nan!” (Yohanna 2:15, 16) Kamar dai babu wanda yake da gaba gaɗi ya yi adawa da wannan mutumin mai ƙarfin zuciya.

“Ku fitar da waɗannan daga nan!”

Ka Ga Ɗa, Ka Ga Uba

5-7. (a) Ta yaya rayuwar Yesu kafin ya zama mutum ya rinjayi yin shari’arsa, kuma mene ne za mu koya ta wajen nazarin misalansa? (b) Wane mataƙi ne Yesu ya ɗauka a kan rashin adalcin Shaiɗan, kuma ta yaya zai yi hakan a nan gaba?

5 Hakika, dillalan sun sake dawowa. Bayan kamar shekara uku, Yesu ya sake magance wannan matsalar ta rashin adalci, a wannan lokaci ya ɗauko kalmomin Jehobah yana la’anta waɗanda suka mayar da gidan Ubansa “wurin ɓuyan ’yan fashi.” (Irmiya 7:11; Matiyu 21:13) Hakika, sa’ad da Yesu ya ga damfara ta haɗama na mutanen da kuma ƙazantar da haikalin Allah, ya ji kamar dai yadda Ubansa ya yi. Kuma ba abin mamaki ba ne! Domin cikin shekaru miliyoyi marasa iyaka, Uba na sama ya koyar da Yesu. Saboda haka, ya cika da shari’a irin na Jehobah. Ya zama rayayyen misali na furucin nan, Ka ga ɗa, ka ga uba. Saboda haka, idan muna so mu fahimci halin Jehobah na shari’a, hanya mafi kyau ita ce mu yi bimbini bisa misalan Yesu Kristi.—Yohanna 14:9, 10.

6 Ɗan Allah makaɗaici yana wajen sa’ad da Shaiɗan ya kira Jehobah Allah maƙaryaci, kuma ya tuhumi adalcin Sarautarsa. Wannan jafa’i ne na kai tsaye! Ɗan kuma ya ji Shaiɗan ya ƙalubalanta cewa babu wanda zai bauta wa Jehobah ba tare da son kai ba, cikin ƙauna. Waɗannan tuhuma babu shakka sun ɓata wa Ɗan mai adalci rai. Babu shakka ya yi farin ciki da ya sani cewa shi yake da babban matsayi wajen gyara wannan al’amari! (2 Korintiyawa 1:20) Ta yaya zai yi wannan?

7 Kamar yadda muka koya a Babi na 14, Yesu Kristi ya bayar da amsa ta ƙarshe, cikakkiya ga tuhuma da take ɓata amincin halittun Jehobah. Ta hakan, Yesu ya kafa tushen wanke sunan Allah tsarkakke, wato Jehobah daga zargi, har daga ƙarya cewa bai iya mulki ba. Tun da Yesu ne Shugaba, zai kafa shari’a ta Allah a dukan sararin sama. (Ayyukan Manzanni 5:31) Rayuwarsa a duniya haka nan ta nuna shari’a ta Allah. Jehobah ya ce game da shi: “Zan cika shi da ruhuna, zai sanar wa al’ummai shari’ar gaskiya.” (Matiyu 12:18) Ta yaya Yesu ya cika waɗannan kalmomi?

Yesu Ya Bayyana ‘Abin da Shari’a Take Nufi’

8-10. (a) Ta yaya al’adar baka ta addinin Yahudawa ta ɗaukaka ƙyama ga waɗanda ba Yahudawa ba da kuma mata? (b) Ta yaya dokokin baka ta mai da dokar Asabarci na Jehobah ta zama kaya?

8 Yesu ya yi ƙaunar Dokar Jehobah kuma ya rayu daidai da ita. Amma shugabannin addini na zamaninsa sun jujjuya Dokar kuma ba su yi amfani da ita daidai ba. Yesu ya ce musu: “Kaitonku, malaman Koyarwar Musa da Farisiyawa, munafukai! . . . kun ƙyale abubuwan da suka fi muhimmanci a cikin dokoki, wato gaskiya, da jin ƙai, da aminci.” (Matiyu 23:23) Waɗannan malaman Dokar Allah ba sa bayyana ‘abin da shari’a take nufi.’ Maimakon haka, suna ɓata shari’a ta Allah. Ta yaya? Ka ga wasu misalai ’yan kaɗan.

9 Jehobah ya umurci mutanensa su ware daga al’umman arna da suka kewaye su. (1 Sarakuna 11:1, 2) Amma, wasu shugabannan addini masu wawan-bi suka ƙarfafa mutanen su yi ƙyamar dukan waɗanda ba Yahudawa ba. Mishnah yana ɗauke da wannan dokar: “Kada a bar sa a masaukin mutanen al’ummai tun da ana zaton suna jima’i da dabba.” Irin wannan ƙiyayya ga dukan waɗanda ba Yahudawa ba rashin adalci ne kuma bai jitu da ma’anar Dokar Musa ba. (Littafin Firistoci 19:34) Wasu dokokin mutane sun ƙasƙantar da mata. Dokar baka ta ce ya kamata mace ta bi mijinta a baya, kar ta yi tafiya kafaɗa da kafaɗa da shi ba. An gargaɗe namiji kada ya yi magana da mace a cikin jama’a ko idan matarsa ce! Kamar bayi, ba a ba mata damar su ba da shaida a kotu ba. Da akwai wata addu’a ma da maza suke yi wa Allah godiya domin cewa su ba mata ba ne!

10 Shugabannan addini sun binne Dokar Allah a ƙarƙashin dokoki da umurnan mutane. Alal misali, dokar Asabarci, ta hana aiki ne ranar Asabarci, ta keɓe wannan ranar domin bauta, wartsakewa ta ruhaniya, da kuma hutu. Farisawan sun sa dokar ta yi nauyi. Sun ɗauka wa kansu fassarar abin da “aiki” yake nufi. Sun ware abubuwa 39 cewa aiki ne, kamar su girbi ko kuma farauta. Waɗannan suna jawo tambayoyi marasa iyaka. Idan mutum ya kashe ƙuma a ranar Asabarci, yana farauta ne? Idan ya cika hannu da hatsi domin ya ci yayin da yake tafiya, yana girbi ne? Idan ya warkar da wanda yake ciwo, yana aiki ne? Waɗannan tambayoyin an amsa su da dokoki da yawa.

11, 12. Ta yaya Yesu ya nuna adawarsa ga al’adun Farisawa wanda ba daga Nassosi ba?

11 A irin wannan yanayi ta yaya Yesu zai taimaki mutane su fahimci abin da shari’a take nufi? A koyarwarsa da kuma hanyar rayuwarsa ya ƙarfafa wajen yin adawa da waɗannan shugabannan addini. Da farko ka ga wasu cikin koyarwarsa. Ya la’anci dubban dokokinsu na mutane, yana cewa: “Kuna mai da kalmar Allah wofi saboda al’adun da kuke koya wa yaranku.”—Markus 7:13.

12 Yesu ya koyar cikin iko cewa Farisawan sun ɓata game da dokar Asabarcin—cewa, ba su fahimci gaba ɗayan ma’anar dokar ba. Almasihu, ya yi bayani, shi ne ‘ubangijin asabarci,’ saboda haka yana da damar ya warkar da mutane a ranar Asabarci. (Matiyu 12:8) Domin ya nanata batun, ya yi warkarwa ta mu’ujiza a fili a ranar Asabarci. (Luka 6:7-10) Irin wannan warkarwa nuna abin da zai yi ne a dukan duniya a lokacin Sarautarsa ta Shekara Dubu. Alif ɗin za ta zama ranar Asabarci ce mai girma, lokacin da dukan mutane masu aminci a ƙarshe za su huta daga ƙarnuka na wahala cikin zunubi da mutuwa.

13. Wace doka ce ta kahu a sakamakon hidimar Kristi na duniya, kuma ta yaya ta bambanta da wadda take gaba da ita?

13 Yesu kuma ya bayyana sarai abin da shari’a take nufi da sabuwar doka ta kahu, “koyarwar Almasihu,” bayan ya kammala hidimarsa ta duniya. (Galatiyawa 6:2) Ba kamar ta gaba da ita ba, Dokar Musa, wannan sabuwar doka galibi tana dangane ne, ba bisa jerin rubutaccen dokoki ba, amma bisa mizanai. Ko da yake ta ƙunshi wasu dokoki kai tsaye. Ɗaya daga cikin waɗannan Yesu ya kira, “sabon umarni.” Yesu ya koyar da mabiyansa su yi ƙaunar juna kamar yadda ya yi ƙaunarsu. (Yohanna 13:34, 35) Hakika, ƙauna ta sadaukar da kai za ta zama halin dukan waɗanda suke rayuwa bisa ‘dokar Kristi.’

Rayayyen Misali na Shari’a

14, 15. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya fahimci iyakacin ikonsa, kuma me ya sa wannan yake da ban ƙarfafa?

14 Yesu ya yi fiye da koyarwa game da ƙauna. Ya rayu daidai da “koyarwar Almasihu.” An gani a tafarkin rayuwarsa. Ka ga hanyoyi uku da misalin Yesu ya bayyana sarai abin da shari’a take nufi.

15 Na farko, Yesu ya mai da hankali ya guji yin rashin adalci. Wataƙila ka lura cewa yawancin rashin adalci yana faruwa ne sa’ad da mutane ajizai suka zama masu taurin kai kuma suka zarce iyakar ikonsu. Yesu bai yi haka ba. A wani lokaci, wani mutum ya tunkari Yesu, kuma ya ce: “Malam, ka ce wa ɗan’uwana ya ba ni rabona na gadōn da babanmu ya mutu ya bar mana.” Yesu ya ce: “Kai! Wa ya mai da ni alƙali ko in zama mai raba muku kayan da babanku ya mutu ya bar muku?” (Luka 12:13, 14) Wannan ba abin mamaki ba ne? Fahimin Yesu, hukuncinsa, da kuma iyakar iko da Allah ya ba shi ya fi na kowane mutum a duniya; duk da haka, ya ƙi ya saka baki cikin wannan al’amari, tun da ba a ba shi ainihin ikon ya yi haka ba. Yesu ya san da iyakarsa ta wannan hanyar, har a cikin ƙarnuka na rayuwarsa kafin ya zama mutum. (Yahuda 9) Hali ne mai kyau na Yesu, cikin tawali’u ya dogara ga Jehobah ya tsara abin da yake adalci.

16, 17. (a) Ta yaya Yesu ya nuna shari’a wajen wa’azin bisharar Mulkin Allah? (b) Ta yaya Yesu ya nuna cewa shari’arsa tana da jinƙai?

16 Na biyu, Yesu ya nuna shari’a a hanyar da ya yi wa’azin bisharar Mulkin Allah. Bai nuna son zuciya ba. Maimakon haka, ya yi ƙoƙari ya isa wurin dukan ire-iren mutane, ko mai arziki ko matalauci. Akasin haka, Farisawan sun sallami matalauta, da kalma ta nuna ƙyama ʽam-ha·ʼaʹrets, ko “ ’yan iska.” Yesu da gaba gaɗi ya gyara wannan rashin adalci. Sa’ad da ya koya wa mutane bishara—ko kuma ma, idan ya ci abinci da mutanen, ko ciyar da su, ya warkar da su, ko kuma ya tashe su a matattu—ya ɗaukaka shari’ar Allahn da yake so a kai ga “dukan mutane.” c1 Timoti 2:4.

17 Na uku, shari’ar Yesu tana da jinƙai ƙwarai. Ya yi ƙoƙari ya taimake masu zunubi. (Matiyu 9:11-13) Ya taimaki mutane da ba su da ƙarfin kāre kansu. Alal misali, Yesu bai haɗa da shugabannan addini ba wajen ɗaukaka rashin yarda da dukan mutane na Al’ummai ba. Cikin jinƙai, ya taimaki kuma ya koyar da wasu cikin waɗannan, ko da yake ainihi an aiko shi ga Yahudawa ne. Ya yarda ya tafiyar da warkarwa na sojan Roma, yana cewa: “A cikin Isra’ila ban taɓa samun mai bangaskiya mai ƙarfi kamar wannan ba.”—Matiyu 8:5-13.

18, 19. (a) A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya ɗaukaka darajar mata? (b) Ta yaya misalin Yesu ya taimaka mana muka ga nasaba da ke tsakanin gaba gaɗi da shari’a?

18 Hakazalika, Yesu bai yarda da yadda ake ɗaukan mata ba. Maimakon haka, da gaba gaɗi ya yi abin da yake daidai. Matan Samariyawa an gaskata ba su da tsarki kamar matan mutane na Al’ummai. Duk da haka, Yesu bai yi wata wata ba wajen yi wa matar Basamariyar wa’azi a rijiyar Sukar. Hakika, ga wannan matar ne ma Yesu da farko ya bayyana kansa shi ne Almasihu da aka yi alkawarinsa. (Yohanna 4:6, 25, 26) Farisawan sun ce bai kamata a koya wa mata Dokar Allah ba, amma Yesu ya yi amfani da lokaci da kuzari wajen koyar da mata. (Luka 10:38-42) Kuma ko da yake al’ada ta gaskata cewa mata ba za a iya dogara cewa za su ba da tabbatacciyar shaida ba, Yesu ya ɗaukaka mata da yawa da gatar kasancewa na farko su gan shi bayan ya tashi daga matattu. Har ya gaya musu su je su gaya wa almajiransa maza game da wannan aukuwa mai muhimmanci!—Matiyu 28:1-10.

19 Hakika, Yesu ya bayyana sarai abin da shari’a take nufi. A yawancin lokatai, ya yi hakan cikin haɗari ga kansa. Misalin Yesu ya taimake mu mu ga cewa ɗaukaka shari’a ta gaskiya tana bukatar gaba gaɗi. Daidai fa, aka kira shi “Zakin nan daga zuriyar Yahuda.” (Ru’uyar da Aka Yi wa ta Yohanna 5:5) Ka tuna cewa zaki alama ne na shari’a, mai gaba gaɗi. A nan gaba kaɗan, Yesu zai kawo shari’a mafi girma. A cikar ta gabaki ɗaya zai kafa “yin gaskiya a duniya.”—Ishaya 42:4.

Almasihu Ya Kafa “Yin Gaskiya a Duniya”

20, 21. A zamaninmu, ta yaya Sarki Almasihu ya ɗaukaka shari’a a dukan duniya da kuma a cikin ikilisiyar Kirista?

20 Tun da ya zama Sarki Almasihu a shekara ta 1914, Yesu ya ɗaukaka shari’a a duniya. Ta yaya? Ya goyi bayan cikar annabcinsa da ke Matiyu 24:14. Mabiyan Yesu a duniya sun koyar da mutanen dukan ƙasashe gaskiya game da Mulkin Jehobah. Kamar Yesu, sun yi wa’azi ba tare da son zuciya ba kuma cikin adalci, suna ƙoƙarin su ba kowa—yara da manya, attajiri da matalauci, maza da mata—zarafi su san Jehobah, Allah na shari’a ta gaskiya.

21 Yesu kuma yana ɗaukaka shari’a a cikin ikilisiya ta Kirista, wanda shi ne Shugabanta. Kamar yadda aka annabta, ya yi tanadin “baiwa iri-iri,” dattawa Kiristoci masu aminci waɗanda suke ja-gora a cikin ikilisiya. (Afisawa 4:8-12) Wajen kiwon wannan garke mai tamani na Allah, irin waɗannan mutane suna bin misalin Yesu Kristi wajen ɗaukaka shari’a. Suna tunawa kullum cewa Yesu yana son a bi da tumakinsa cikin adalci—ko yaya matsayinsu, rinjaya, ko kuma arziki.

22. Yaya Jehobah yake ji game da rashin adalci mai yawa a duniya ta yau, kuma Mene ne ya naɗa Ɗansa ya yi game da shi?

22 A nan gaba kaɗan, Yesu zai kafa shari’a a duniya a babbar hanya. Rashin adalci ya yi yawa cikin wannan lalatacciyar duniya. Kowane yaro da ya mutu domin yunwa ya faɗa ne cikin hannun rashin adalci da ba ta da hujja, musamman idan muka yi tunani game da kuɗi da kuma lokaci da ake ɓatarwa wajen yin makaman yaƙi da kuma nishaɗi na son kai na maneman nishaɗi. Miliyoyin mutuwa marar iyaka kowacce shekara suna ɗaya ne cikin rashin adalci mai yawa, duka kuma suna ta da fushin Jehobah na adalci. Ya naɗa Ɗansa ya yi yaƙi na adalci da dukan wannan mugun zamani ya kawo ƙarshen dukan rashin adalci dindindin.—Ru’uyar da Aka Yi wa ta Yohanna 16:14, 16; 19:11-15.

23. Bayan Armageddon, ta yaya Kristi zai ɗaukaka shari’a cikin dukan fil’azal?

23 Amma dai, shari’ar Jehobah ta ƙunshi fiye da kawai halaka miyagu. Ya kuma naɗa Ɗansa ya yi sarauta a matsayin “Sarkin Salama.” Bayan yaƙin Armageddon, sarautar Yesu za ta kafa salama a dukan duniya, kuma zai yi sarauta cikin “adalci.” (Ishaya 9:6, 7) Sai Yesu ya yi farin ciki wajen kawar da dukan rashin adalci da ya kawo bala’i da wahala a duniya. A cikin dukan fil’azal, zai ɗaukaka cikakkiyar shari’a ta Jehobah da aminci. Saboda haka, yana da muhimmanci mu yi ƙoƙari mu yi koyi da shari’ar Jehobah a yanzu. Bari mu ga yadda za mu yi haka.

a Wajen nuna fushi na adalci, Yesu kama yake da Jehobah, wanda yake “fushi” da dukan mugunta. (Nahum 1:2) Alal misali, bayan Jehobah ya gaya wa mutanensa masu taurin kai cewa sun mai da gidansa “wurin ɓuyan ’yan fashi,” ya ce: “Zan zuba fushina da fushi mai zafi a kan wannan wuri.”—Irmiya 7:11, 20.

b In ji Mishnah, an taɓa zanga-zanga wasu shekaru daga baya domin tsadar tantabaru a haikalin. Aka rage kuɗin tantabarun nan da nan da kashi 99 kan ɗari! Wa suke amfana daga wannan kasuwanci mai riba? Wasu ’yan tarihi suka ce kasuwar haikalin, gidan Babban Firist Annas suke da ita, yana ba da yawancin arziki wa iyalin firist ɗin.—Yohanna 18:13.

c Farisawan sun yi imani da cewa matalauta, waɗanda ba su yi zurfi a Doka ba, “la’anannu ne.” (Yohanna 7:49) Sun ce kada mutum ya koyar da su ko ya yi kasuwanci da su ko kuma ma ya ci abinci da su ko kuma ya yi addu’a tare da su. Mutum ya ƙyale ’yarsa ta auri ɗayansu ya fi ya ba da ita ga mugun dabba. Sun yi tunanin cewa tashin matattu ban da waɗannan matalauta.