Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 18

Hikima Cikin “Maganar Allah”

Hikima Cikin “Maganar Allah”

1, 2. Wace “wasiƙa” ce Jehobah ya rubuto mana, kuma me ya sa?

 KA TUNA sa’ad da ka samu wasiƙa daga wanda kake ƙauna da ke da zama da nesa? Abubuwa kaɗan ne suke ba mu farin ciki kamar wasiƙa daga wajen wanda muke ƙauna. Muna farin ciki mu san yadda yake, abin da ya fuskanta da kuma abin da yake shirin yi. Irin wannan sadarwa tana kawo ƙaunatattu kusa da juna, ko suna nesa da juna a zahiri.

2 To, mene ne zai kawo mana farin ciki fiye da samun rubutaccen saƙo daga Allahn da muke ƙauna? Watau, kamar Jehobah ya rubuto mana wasiƙa ne—Maganarsa, Littafi Mai Tsarki. A ciki ya gaya mana wanda yake, abin da ya yi, abin da yake da niyyar yi, da kuma abubuwa da yawa. Jehobah ya ba mu Kalmarsa domin yana so mu kusace shi. Allahnmu mafi hikima ya zaɓi hanya da ta fi kyau ya yi magana da mu. Da hikima marar iyaka a hanyar da aka rubuta Littafi Mai Tsarki da kuma abin da ya ƙunsa.

Me Ya Sa Rubutacciyar Kalma?

3. Ta wace hanya ce Jehobah ya bayar da Doka ga Musa?

3 Wasu suna iya mamaki, ‘Me ya sa Jehobah bai yi amfani da hanya mafi ban al’ajabi ba—kamar a ce, murya daga sama—ta yi magana da mutane?’ Hakika, a wasu lokatai Jehobah ya yi magana daga sama ta wajen wakilansa mala’iku. Alal misali ya yi hakan, sa’ad da yake ba da Doka ga Isra’ila. (Galatiyawa 3:19) Muryar daga sama tana da ban tsoro—saboda haka Isra’ilawa da suka razana suka roƙi Jehobah kada ya yi magana da su ta wannan hanyar amma ya yi hakan ta wajen Musa. (Fitowa 20:18-20) Saboda haka, aka bai wa Musa Doka da take ɗauke da umurnai 600, baki da baki.

4. Ka bayyana abin da ya sa sanarwa ta maganar baki ba za ta kasance hanya ba ce matabbaciya ta bi da dokokin Allah.

4 To, inda ba a rubuta Dokar ba fa? Da Musa zai iya tuna daidai kalmomin dokar kuma ya gaya wa sauran al’ummar ba tare da kuskure ba? Tsara da suke zuwa a nan gaba fa? Da dole ne su dogara gabaki ɗaya a kan maganar baka? Da wannan ba za ta kasance hanya ce matabbaciya ta bi da dokokin Allah ba. Ka yi tunanin abin da zai faru idan an sanar da labari ga dogon layin mutane a gaya wa mutum na farko sai shi kuma ya gaya wa na biye da shi a bi haka har ƙarshen layin. Abin da mutumin da yake ƙarshen layin zai ji wataƙila zai bambanta ƙwarai da na farkon. Kalmomin Dokar Allah, a nan ba ta cikin irin wannan haɗarin.

5, 6. Mene ne Jehobah ya umurci Musa ya yi da Maganarsa, kuma me ya sa albarka ce a gare mu mu samu rubutacciyar Kalmar Jehobah?

5 Cikin hikima Jehobah ya zaɓi a rubuta maganarsa. Ya umurci Musa: “Ka rubuta dukan waɗannan kalmomi. Bisa ga waɗannan kalmomi ne, na ɗaura yarjejeniya da kai da kuma jama’ar Isra’ila.” (Fitowa 34:27) Haka zamanin rubuta Littafi Mai Tsarki ya fara, a shekara ta 1513 K.Z. A cikin shekaru 1,610 da suka biyo baya, Jehobah ya yi “magana ta hanyoyi iri-iri da kuma a lokatai dabam-dabam,” da marubuta 40 waɗanda suka rubuta Littafi Mai Tsarki. (Ibraniyawa 1:1) Daga baya, marubuta da suka ba da kai suka mai da hankali suka rubuta wasu domin su adana Nassosin.—Ezra 7:6; Zabura 45:1.

6 Babu shakka Jehobah ya albarkace mu da ya yi magana da mu ta rubutu. Ka taɓa samun wasiƙar da kake ƙaunarta ƙwarai—wataƙila domin tana da ban ƙarfafa—da ka adana kana karatunta sau da yawa? Haka “wasiƙar” Jehobah take a gare mu. Domin Jehobah ya sa an rubuta maganarsa, muna iya karatunta a kai a kai kuma mu yi bimbini bisa abin da ta ce. (Zabura 1:2) Za mu iya samun “ƙarfafawa” daga Nassosi a duk lokacin da muke bukatar ta.—Romawa 15:4.

Me Ya Sa Marubuta Mutane Ne?

7. Ta yaya aka ga hikimar Jehobah a wajen yin amfani da marubuta mutane?

7 Cikin hikimarsa, Jehobah ya yi amfani da mutane su rubuta Kalmarsa. Ka yi la’akari da wannan: Da Jehobah ya yi amfani da mala’iku su rubuta Littafi Mai Tsarki, da zai kasance iri ɗaya ne? Hakika, da mala’iku za su iya kwatanta Jehobah a nasu mizanai masu girma, su furta nasu ibada a gare shi, kuma su rubuta labari game da bayin Allah masu aminci. Da kuwa za mu iya fahimtar ra’ayin waɗannan kamiltattun halittu na ruhu, waɗanda iliminsu, fahimi, da kuma ikonsu sun ɗara namu?—Ibraniyawa 2:6, 7.

8. A wace hanya ce aka ƙyale marubutan Littafi Mai Tsarki su yi amfani da na su fahimi? (Duba hasiya.)

8 Ta wajen amfani da marubuta mutane, Jehobah ya ba mu daidai abin da muke bukata, wato Maganarsa “hurarre,” kuma tana ratsa zukatanmu. (2 Timoti 3:16) Ta yaya ya cim ma wannan? A bayyane yake cewa ya ƙyale marubutan su yi amfani da nasu fahimi wajen zaɓan kalmomi “masu daɗin ji,” da kuma “kalmomin gaskiya.” (Mai Wa’azi 12:10, 11) Wannan ya ba da dalilin salo iri-iri na Littafi Mai Tsarki; rubutun ya bayyana tarbiyya da kuma mutuntakar kowanne marubuci. a Duk da haka, “ruhun Allah ne ya shiga zukatan mutane ya sa su su faɗa abin da suka karɓa daga wurin Allah.” (2 Bitrus 1:21) Saboda haka, abu da aka samu a ƙarshe da gaske “kalmar Allah” ce.—1 Tasalonikawa 2:13.

“Duk Rubutacciyar Maganar Allah hurarre ce daga wurinsa”

9, 10. Me ya sa yin amfani da marubuta mutane ya ƙara armashi ga Littafi Mai Tsarki?

9 Yin amfani da marubuta mutane ya bai wa Littafi Mai Tsarki armashi ƙwarai. Marubutansa mutane ne masu motsin zuciya kamar namu. Tun da ajizai ne, sun fuskanci gwaji da kuma matsi kamar namu. A wasu lokatai, ruhun Jehobah yana hure su su rubuta game da tasu motsawar zuciya da kuma kokawa. (2 Korintiyawa 12:7-10) Saboda haka sun yi rubutu na mai maganar, kalmomi da babu mala’ikan da zai iya furta su.

10 Ka ɗauki Sarki Dauda na Isra’ila ga misali. Bayan ya yi zunubi mai tsanani, Dauda ya rubuta zabura da a ciki ya furta zuciyarsa, yana roƙon gafarar Allah. Ya rubuta: “Ka tsabtace ni daga zunubaina! Gama ina sane da zunuban gangancina, zunubaina suna a gabana kullum. Lallai mai laifi ne ni tun daga ranar da aka haife ni, mai zunubi ne ni tun mamata ta ɗauki cikina. Kada ka kore ni daga gabanka, kada ka ɗauke mini ruhunka mai tsarki. Ya Allah, hadaya ta gaske a wurinka, ita ce halin sauƙin kai, halin sauƙin kai da zuciya mai tuba ba za ka ƙi ba, ya Allah.” (Zabura 51:2, 3, 5, 11, 17) Ka ga baƙin cikin marubucin? Waye in ba mutum ajizi ba zai iya furta irin wannan sosuwar zuci?

Me Ya Sa Littafi Ne Game da Mutane?

11. Waɗanne misalai ne na rayuwa ta gaskiya aka haɗa cikin Littafi Mai Tsarki ‘domin koyonmu’?

11 Har ila da wani abu kuma da ya ƙara ga armashin Littafi Mai Tsarki. Galibi, littafi ne game da mutane—mutane na zahiri—waɗanda suke bauta wa Allah da kuma waɗanda ba sa bauta masa. Mun karanta game da abubuwa da suka fuskanta, wahalarsu, da kuma farin ciki. Mun ga sakamakon abin da suka zaɓa a rayuwa. An rubuta irin waɗannan labaran “domin a koyar da mu.” (Romawa 15:4) Ta wajen wannan misali na rayuwa ta gaskiya, Jehobah ya koyar a hanyoyi da suke taɓa zukatanmu. Ga wasu misalai.

12. Tarihin Littafi Mai Tsarki game da mutane marasa aminci ya taimake mu a wace hanya?

12 Littafi Mai Tsarki ya faɗi game da mutane marasa aminci, har ma miyagu, da kuma abin da ya faru da su. A cikin waɗannan tarihin, ayyukan sun nuna halaye da ba a so, sun kasance da sauƙi mu fahimci hakan. Alal misali, wace doka ce game da rashin aminci za ta fi wannan nunin halin Yahuda wanda ya shirya ya ci amanar Yesu? (Matiyu 26:14-16, 46-50; 27:3-10) Irin wannan tarihin yana taɓa zuciyarmu ƙwarai, yana taimakonmu mu fahimci kuma mu ƙi ƙazaman halaye.

13. A waɗanne hanyoyi ne Littafi Mai Tsarki ya taimake mu mu fahimci halaye masu kyau?

13 Littafi Mai Tsarki kuma ya kwatanta bayin Allah da yawa masu aminci. Mun karanta game da ibadarsu da kuma aminci. Mun ga misalan halayen da ya kamata mu koya domin mu kusaci Allah. Ka ɗauki bangaskiya ga misali. Littafi Mai Tsarki ya bayyana ma’anar bangaskiya kuma ya gaya mana yadda take da muhimmanci idan muna so mu faranta wa Allah rai. (Ibraniyawa 11:1, 6) Amma kuma Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da misalai na bangaskiya ƙwarai. Ka yi tunanin bangaskiya da Ibrahim ya nuna sa’ad da ya yi ƙoƙarin ya miƙa Ishaƙu. (Farawa, sura 22; Ibraniyawa 11:17-19) Ta wajen irin wannan tarihi, kalmar nan “bangaskiya” tana ba da bayani kuma takan kasance da sauƙin fahimta. Kai, hikima ce da Jehobah ba kawai ya shawarce mu mu koyi halaye masu kyau ba, amma kuma ya yi tanadin misalai game da su!

14, 15. Mene ne Littafi Mai Tsarki ya gaya mana game da wata mace da ta zo haikali, kuma mene ne muka koya game da Jehobah daga wannan labarin?

14 Tarihin rayuwa ta gaske da suke cikin Littafi Mai Tsarki sau da yawa suna koya mana wani abu game da yadda Jehobah yake. Ka yi la’akari da abin da muka karanta game da matar da Yesu ya lura da ita a cikin haikali. Yayin da yake zaune kusa da ma’aji, Yesu yana kallo sa’ad da mutane suke jefa kyautarsu. Mutane masu arziki da yawa suka zo, suna ta zubawa daga “yawan abin da suke da shi.” Amma Yesu ya kafa wa wata gwauruwa matalauciya ido. Ta ba da “dukan abin da take dogara da shi.” b Shi ne iyakar kuɗi da take da su. Yesu, wanda yake nuna irin ra’ayin Jehobah game da batutuwa ya ce: “Baikon da matalauciyar nan ta sa, ya fi na sauran [mutanen] duka.” Bisa ga waɗannan kalmomi, ta zuba fiye da dukan abin da suka zuba idan aka haɗa.—Markus 12:41-44; Luka 21:1-4; Yohanna 8:28.

15 Ba shi da muhimmanci ne cewa a cikin dukan mutane da suka zo haikalin a wannan ranar, aka ware wannan gwauruwar kuma aka ambace ta a cikin Littafi Mai Tsarki? Ta wajen wannan misalin, Jehobah ya koya mana cewa shi Allah ne mai godiya. Yana farin ciki ya karɓi kyautarmu ta zuciya ɗaya, ko yaya suke idan aka gwada su da abin da wasu suka bayar. Jehobah ya yi amfani da hanya mafi kyau ya koyar da mu wannan gaskiya mai taɓa zuciya!

Abin da Ba Ya Cikin Littafi Mai Tsarki

16, 17. Ta yaya ake ganin hikimar Jehobah har a cikin abin da ya zaɓi ba zai haɗa cikin Kalmarsa ba?

16 Idan ka rubuta wasiƙa ga wadda kake ƙauna, wasiƙar za ta kasance tana da iyaka. Saboda haka, za ka zaɓi abin da za ka rubuta. Hakanan, Jehobah ya zaɓi ya faɗi game da wasu mutane da kuma wasu aukuwa cikin Kalmarsa. Amma a waɗannan labaran na kwatanci, Littafi Mai Tsarki bai faɗi kome dalla-dalla ba. (Yohanna 21:25) Alal misali, sa’ad da Littafi Mai Tsarki ya faɗi game da zartar da hukuncin Allah, bayanin ba zai amsa dukan tambayoyinmu ba. Hikimar Jehobah ta bayyana har a cikin abin da ya zaɓa ba zai haɗa cikin Kalmarsa ba. Ta yaya?

17 Hanyar da aka rubuta Littafi Mai Tsarki tana gwada abin da yake zuciyarmu. Ibraniyawa 4:12 ta ce: “Kalmar Allah [ko kuma, saƙo] tana da rai, tana da ƙarfin aiki kuma. Kaifinta ya fi na kowane takobi mai baki biyu. Tana sara har ciki-cikin mutum, ta raba ruhu da rai . . . . Har ma tana gane duk tunani da nufin da suke cikin zuciya.” Saƙon Littafi Mai Tsarki yana hudawa da zurfi, yana bayyana tunaninmu na gaske da kuma nufe-nufenmu. Waɗanda suke karatunsa da ra’ayin sukā sau da yawa suna tuntuɓe domin labaran da ba sa ɗauke da cikakken bayani ba za su gamsar da su ba. Irin waɗannan mutanen har suna tambaya ko Jehobah da gaske yana da ƙauna, da hikima, kuma mai gaskiya.

18, 19. (a) Me ya sa bai kamata mu damu ba idan wani labari na Littafi Mai Tsarki ya jawo tambayoyi da ba za mu iya samun amsarsu nan take ba? (b) Me ake bukata domin a fahimci Kalmar Allah, kuma ta yaya wannan tabbaci ne na hikima mai girma ta Jehobah?

18 Akasarin haka, sa’ad da muka yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kyau da zuciyar kirki, za mu koya game da Jehobah a matani da Littafi Mai Tsarki gaba ɗayansa ya bayyana shi. Saboda haka, ba ya ta da mana hankali idan a wani labari ya jawo tambayoyi da ba za mu iya samun amsarsu ba a take. Alal misali: Sa’ad da muke wasan wasa ƙwaƙwalwa, wataƙila da farko ba mu ga wani ɓangare ba ko kuma ba mu fahimci yadda wani ɓangare yake da nasaba da wasu ba. Duk da haka, wataƙila mun tare ɓangarori da suka isa mu fahimci yadda hoton gabaki ɗayansa yake. Hakazalika, sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki, da kaɗan kaɗan za mu koyi game da irin Allah da Jehobah yake, sai cikakken hoton ya bayyana. Ko idan da farko ba mu fahimci wasu labarai ba ko kuma mu ga yadda ya jitu da mutuntakar Allah, nazarinmu na Littafi Mai Tsarki ya riga ya koya mana ƙwarai game da Jehobah da zai iya sa mu ga cewa shi babu shakka mai ƙauna ne, Allah mai gaskiya.

19 To, domin mu fahimci Kalmar Allah, dole ne mu karanta kuma mu yi nazarinsa da zuciyar kirki da kuma rashin son zuciya. Wannan ba tabbaci ba ne na hikima mai girma na Jehobah? Mutane masu basira suna iya rubuta littafi da sai “masu hikima da masu ilimi” za su iya fahimta. Amma a rubuta littafi da sai masu zuciyar kirki za su fahimta—yana bukatar hikima ta Allah!—Matiyu 11:25.

Littafi Mai Ɗauke da “Ainihin Hikima”

20. Me ya sa Jehobah ne kaɗai zai gaya mana hanya mafi kyau na rayuwa, kuma mene ne Littafi Mai Tsarki ya ƙunsa da zai taimake mu?

20 A cikin Kalmarsa, Jehobah ya gaya mana hanya mafi kyau da za mu rayu. Tun da Mahaliccinmu ne, ya san abin da muke bukata fiye da yadda muka sani. Bukatun mutane—haɗe da muradin ƙauna, farin ciki, da kuma nasara wajen nasaba—ya kasance duk ɗaya. Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da arziki na “ainihin hikima” da za ta taimake mu mu yi rayuwa mai ma’ana. (Karin Magana 2:7) Kowanne sashe na wannan littafin nazari yana ɗauke da babi da yake nuna yadda za mu yi amfani da gargaɗi na hikima ta Littafi Mai Tsarki, amma bari mu bincika ɗaya kawai.

21-23. Wane gargaɗi na hikima zai taimake mu mu guje wa fushi da ƙiyayya?

21 Ka taɓa lura cewa mutane da suke da ƙiyayya da kuma gāba sau da yawa suna ji wa kansu ne? Gāba kaya ce mai nauyin ɗauka a rayuwa. Sa’ad da muke riƙe da ita, tana cika tunaninmu, tana ɗauke mana salama, kuma ta kashe mana farin ciki. Nazari na kimiyya ya nuna cewa yin gāba za ta iya ƙara mana haɗarin ciwon zuciya da kuma wasu cututtuka masu tsanani. Shekaru aru-aru kafin waɗannan nazarin kimiyya, Littafi Mai Tsarki da hikima ya ce: “Kada ka bar zuciya ta yi zafi, ko hankalinka ya tashi.” (Zabura 37:8) Amma ta yaya za mu yi wannan?

22 Kalmar Allah ta ba da wannan gargaɗi cikin hikima: “Hankali yakan sa mutum ya danne fushinsa, ƙyale laifin da aka yi masa, abu ne mai kawo masa daraja.” (Karin Magana 19:11) Fahimi iya hangar nesa ce, ganin fiye da zahiri. Fahimi yana ɗauke da fahimta, domin zai taimake mu mu fahimci abin da ya sa wani ya yi magana ko kuma ya yi abu a wata hanya. Da ƙoƙarin mu fahimci ainihin abin da ya motsa shi, yadda yake ji, da kuma yanayin zai iya taimakonmu wajen korar miyagun tunani da kuma zuci game da shi.

23 Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da wannan ƙarin shawarwari: “Ku yi ta haƙuri da juna kuna gafarta wa juna.” (Kolosiyawa 3:13, New World Translation) Furucin nan “ku yi ta haƙuri da juna” yana nufin jimiri da wasu, ƙyale halayensu da ba ma so. Irin wannan jimirin zai taimaka wajen guje wa ƙananan ƙiyayya. “Gafarta” tana ɗauke da ma’anar a ƙyale ƙiyayya ta wuce. Allah mai hikima ya sani cewa muna bukatar mu gafarta wa wasu sa’ad da akwai dalilin yin haka. Wannan ba domin a kyautata musu ba ne kawai amma kuma domin namu kwanciyar rai da kuma zuciya. (Luka 17:3, 4) Hikima tana ƙunshe cikin Kalmar Allah!

24. Me ke faruwa idan muka sa rayuwarmu ta jitu da hikima ta Allah?

24 Domin ƙaunarsa marar iyaka ta motsa shi, Jehobah yana so ya yi magana da mu. Ya zaɓi hanya mafi kyau—rubutacciyar “wasiƙa” da mutane suka rubuta sa’ilin da ruhu mai tsarki yake yi musu ja-gora. Domin haka, hikimar Jehobah ce take cikin shafuffukansa. Wannan hikimar ‘tabbatacciya’ ce. (Zabura 93:5) Sa’ad da muka sa rayuwarmu ta jitu da ita, da kuma sa’ad da muka gaya wa wasu, ta haka muna kusantar Allahnmu da ya fi hikima. A babi na gaba, za mu tattauna wani misali fitacce na hikima mai hangar nesa na Jehobah: iyawarsa ya faɗi abin da zai kasance a nan gaba kuma ya cika nufinsa.

a Alal misali, Dauda, wanda makiyayi ne, ya yi amfani da misalai daga rayuwar makiyayi. (Zabura ta 23) Matiyu, wanda dā mai karɓan haraji ne, ya yi magana sau da yawa bisa kuɗi da kuma muhimmancinsu. (Matiyu 17:27; 26:15; 27:3) Luka, wanda likita ne, ya yi amfani da kalmomi da suka nuna wannan.—Luka 4:38; 14:2; 16:20.

b Kowacce wannan saba drachma ɗari ce, mafi ƙanƙantar tsaba ta Yahudawa da ake amfani da shi a lokacin. Ɗari biyu sun yi daidai da kashi ɗaya cikin sattin da huɗu na kuɗin aikin yini. Waɗannan tsaba biyu ba za su iya ma su sayi gwara guda ba, tsuntsu mai araha da matalauta suke amfani da shi wajen abinci.