BABI NA 22
“Hikima Mai-Fitowa Daga Bisa” Tana Aiki Kuwa A Rayuwarka?
1-3. (a) Ta yaya Sulemanu ya nuna hikima mai yawa wajen warware jayayyar mata game da jariri? (b) Me Jehobah ya yi alkawari zai ba mu, kuma waɗanne tambayoyi ne suka taso?
AL’AMARI ne mai wuya—mata biyu suna jayayya a kan jariri. Matan suna zama a gida ɗaya, kowacce ta haifi ɗa, kwanaki ne kawai suka raba su. Yaro ɗayan ya mutu, amma yanzu kowacce tana da’awar ita ce mamar yaron da yake raye. a Babu shaida game da abin da ya faru. Wataƙila an kai al’amarin gaban alƙali a ƙaramin kotu amma abin ya faskara. A ƙarshe, aka kai wannan al’amarin gaban Sulemanu, sarkin Isra’ila. Zai iya ya bayyana gaskiyar al’amarin kuwa?
2 Bayan ya saurara na ɗan lokaci sa’ad da matan suke jayayya, Sulemanu ya aika a kawo takobi. Sai, da tabbaci, ya ba da umurni a raba yaron gida biyu, a ba kowacce mace ɓari guda. A take, uwar ta ainihi ta roƙi sarki ya ba da yaron—ɗan da take ƙauna—ga mace ɗayar. Amma ɗayar macen ta nace a raba jaririn gida biyu. Sulemanu yanzu ya san gaskiyar. Ya san ƙaunar uwa ga ɗan cikinta, kuma ya yi amfani da wannan ilimin ya warware jayayyar. Ka yi tunanin kwanciyar ran uwar sa’ad da Sulemanu ya ba ta jaririn, ya ce: “Ita ce ainihin mamar.”—1 Sarakuna 3:16-27.
3 Hikima mai yawa, ko ba haka ba? Sa’ad da mutane suka ji yadda Sulemanu ya warware al’amarin, Sai suka cika da tsoro, “gama sun gane cewa Allah ya ba shi hikima.” Hakika, hikimar Sulemanu kyauta ce daga Allah. Jehobah ya ba shi “zuciya mai hikima da ganewa.” (1 Sarakuna 3:12, 28) To, mu kuma fa? Mu ma za mu iya samun hikima ta ibada? I, an hure Sulemanu ya rubuta: “Yahweh yana ba da hikima.” (Karin Magana 2:6) Jehobah ya yi alkawari ya ba da hikima—iya yin amfani ƙwarai da ilimi, fahimta, da fahimi—ga waɗanda suke nema da gaske. Ta yaya za mu samu hikima da take zuwa daga sama? Kuma ta yaya za mu yi amfani da ita a rayuwarmu?
‘Ka Sami Hikima’—Ta Yaya?
4-7. Waɗanne abubuwa huɗu ake bukata domin samun hikima?
4 Dole ne sai muna da fahimi ko kuma muna da ilimi mai yawa kafin mu samu hikima ta Allah? A’a. Jehobah yana shirye ya ba mu hikima ko daga ina muka fito kuma ko yaya iliminmu. (1 Korintiyawa 1:26-29) Amma dole ne mu ɗauki matakin samu, domin Littafi Mai Tsarki ya aririce mu mu ‘sami hikima.’ (Karin Magana 4:7) Ta yaya za mu yi haka?
5 Na farko, muna bukatar mu ji tsoron Allah. “Tsoron Yahweh shi ne mafarin hikima [“takun farko ga hikima,” The New English Bible],” in ji Karin Magana 9:10. Tsoron Allah shi ne tushen hikima ta gaskiya. Me ya sa? Ka tuna cewa hikima ta ƙunshi iya amfani da ilimi daidai. Tsoron Allah, ba a yi rawar jiki ba ne a gabansa domin razana, amma a yi sujjada a gabansa da ban girma, daraja, da kuma dogara. Irin wannan tsoron yana da kyau kuma yana motsawa. Yana motsa mu mu sa rayuwarmu ta jitu da ilimi na Allah da kuma hanyoyinsa. Babu wani tafarki da ya fi hikima da za mu bi, domin mizanan Jehobah koyaushe suna kawo amfani mafi girma ga dukan waɗanda suka bi su.
6 Na biyu, dole ne mu kasance da tawali’u da kuma filako. Hikimar Allah ba za ta kasance ba ba tare da tawali’u ba da kuma filako. (Karin Magana 11:2) Mene ne wannan? Idan muna da tawali’u da kuma filako, za mu yarda da son rai cewa ba mu san dukan abu ba, da cewa ra’ayinmu ba kullum ba ne yake daidai, saboda haka, muna bukatar mu san ra’ayin Jehobah bisa batun. Jehobah yana “ƙin mai girman kai,” amma yana farin ciki da kuma ba da hikima ga masu tawali’u a zuciya.—Yakub 4:6.
7 Abu na uku mai muhimmanci shi ne nazarin rubutacciyar Kalmar Allah. An bayyana hikimar Jehobah a cikin Kalmarsa. Domin mu sami wannan hikima, dole ne mu yi ƙoƙari mu neme ta. (Karin Magana 2:1-5) Farilla ta huɗu ita ce addu’a. Idan da gaske mun roƙi hikima daga wurin Allah, zai ba mu hannu sake. (Yakub 1:5) Addu’o’inmu domin taimakon ruhunsa ba zai faɗi banza ba. Kuma ruhunsa zai taimake mu mu samu arziki a cikin Kalmarsa da za ta taimake mu magance matsaloli, mu guje wa masifa, kuma mu yanke shawara cikin hikima.—Luka 11:13.
Domin mu samu hikima ta Allah, dole ne mu yi ƙoƙari mu neme ta
8. Idan da gaske mun samu hikima ta Allah, ta yaya za ta bayyana?
8 Kamar yadda aka lura a Babi na 17, hikimar Jehobah tana da amfani. Saboda haka, idan da gaske mun samu hikima ta Allah, za ta bayyana a halayenmu. Almajiri Yaƙub ya kwatanta ’ya’yan hikima ta Allah sa’ad da ya rubuta: “Hikimar da take daga wurin Allah, da farko dai mai tsarki ce, kuma mai kawo salama ce, mai hankali ce, mai sauƙin kai ce, mai yawan tausayi ce, mai yawan alheri ce. Ba ta nuna bambanci ko munafunci.” (Yakub 3:17) Yayin da muke tattauna kowanne cikin waɗannan ɓangarorin hikima ta Allah, za mu iya tambayar kanmu, ‘Shin hikima mai fitowa daga bisa tana aiki kuwa a rayuwata?’
“Mai Tsarki Ce . . . , Kuma Mai Kawo Salama Ce”
9. Mene ne yake nufi a kasance da tsarki, kuma me ya sa ya dace cewa kasancewa da tsarki shi ne hali na farko na hikima da aka rubuta?
9 “Da farko dai mai tsarki ce.” Kasancewa mai tsarki yana nufin kasancewa mai tsabta marar ƙazanta, ba kawai a waje ba amma a ciki. Littafi Mai Tsarki ya danganta hikima da zuciya, amma hikima mai zuwa daga bisa ba za ta shiga zuciyar da ta ƙazantu da mugun tunani, da sha’awa, da kuma nufi ba. (Karin Magana 2:10; Matiyu 15:19, 20) Amma, idan zuciyarmu tsatsarka ce—watau, iyakan yadda ta yiwu ga mutane ajizai—za mu “rabu da mugunta, [mu] yi kirki.” (Zabura 37:27; Karin Magana 3:7) Bai dace ba ne cewa kasancewa da tsarki shi ne hali na farko na hikima da aka rubuta? Ban da haka ma, idan ba mu da tsabta a ɗabi’a ko kuma a ruhaniya, ta yaya za mu nufi wasu halaye na hikima da take zuwa daga bisa?
10, 11. (a) Me ya sa yake da muhimmanci mu kasance masu neman salama? (b) Idan ka ji ka yi wa ɗan’uwa mai bi laifi, ta yaya za ka tabbatar da cewa kai mai yin salama ne? (Ka duba hasiya.)
10 “Kuma mai kawo salama ce.” Hikima ta Allah tana motsa mu mu nemi salama, wadda wani fanni ne na ꞌyar ruhun Allah ce. (Galatiyawa 5:22) Muna ƙoƙari mu guje wa ɓata “salama” da ta haɗa kan mutanen Jehobah. (Afisawa 4:3) Muna kuma iyakacin ƙoƙarinmu mu mai da salama sa’ad da an yi tashin hankali. Me ya sa wannan yake da muhimmanci? Littafi Mai Tsarki ya ce: Ku ci gaba da “zaman lafiya da juna. Ta haka Allah mai ƙauna da salama zai kasance tare da ku.” (2 Korintiyawa 13:11) Idan muka ci gaba da zama da salama, Allah na salama zai kasance tare da mu. Yadda muke bi da ’yan’uwa masu bi yana shafar dangantakarmu da Jehobah kai tsaye. Ta yaya za mu tabbatar da kanmu mu masu neman salama ne? Ga wani misali.
11 Mene ne za ka yi idan ka ji ka yi wa ɗan’uwa mai bi laifi? Yesu ya ce: “Idan kana cikin ba da baiko a kan bagaden hadaya, a nan ka tuna cewa ɗan’uwanka yana da wata damuwa game da kai, sai ka ajiye baikonka a gaban bagaden tukuna, ka je ka shirya da ɗan’uwanka. Sa’an nan ka zo ka ba da baikonka.” (Matiyu 5:23, 24) Za ka yi amfani da wannan gargaɗi ta wajen ɗaukan zarafi ka je wajen ɗan’uwanka. Da wane nufi? Don ka “shirya” da shi. b Domin ka yi haka, kana bukatar ka fahimci, kar ka musanci, fushinsa ba. Idan ka dumfare shi da nufin sulhuntawa kuma ka riƙe wannan hali, hakika dukan wani rashin fahimta za a warware shi, ba da haƙuri yadda ya dace, kuma a yi gafara. Sa’ad da ka ɗauki zarafin ka sulhunta, kana nuna cewa hikima ta Allah ce take ja-gorarka.
“Mai Hankali Ce, Mai Sauƙin Kai”
12, 13. (a) Mece ce ma’anar furucin da aka fassara “mai-hankali” a Yakub 3:17? (b) Ta yaya za mu nuna cewa muna nuna yin la’akari?
12 “Mai hankali ce.” Me yake nufi a mutum ya zama mai hankali? In ji wani manazarci, kalmar Helenanci ta asali da aka fassara ta, “mai hankali” a Yakub 3:17 tana da wuyar fassara. Kalmar tana iya nufin mutum ba ya nacewa da raꞌayinsa. Masu fassara sun yi amfani da kalmomi kamar su “mai kamewa,” “mai haƙuri,” da kuma “mai la’akari.” Ta yaya za mu nuna cewa wannan ɓangaren hikima daga bisa tana aiki a cikinmu?
13 “Ku kasance da halin haƙuri cikin dangantakarmu da kowa,” in ji Filibiyawa 4:5. Wata fassara ta ce: “Ku kasance a san ku da yin la’akari.” (The New Testament in Modern English, na J. B. Phillips) Ka lura cewa ba batun yaya muke ganin kanmu ba ne; amma batun yaya wasu suke ganinmu, da yadda aka san mu ne. Mutum mai la’akari ba ya nace wa kalmomin doka ko da yaushe ko kuma ga nasa ra’ayi. Maimakon haka, yana shirye ya saurari wasu, sa’ad da haka ta dace, ya yarda da muradinsu. Kuma yana da kamewa, ba mai tsanantawa ba, a sha’aninsa da wasu. Ko da yake wannan yana da muhimmanci ga dukan Kiristoci, yana da muhimmanci musamman ga dattawa. Kamewa yana jawo mutane, kuma ya sa dattawa su kasance a iya zuwa gare su. (1 Tasalonikawa 2:7, 8) Dukanmu ya kamata mu tambayi kanmu, ‘An san ni da yin la’akari, mai yarda, kuma mai kamewa kuwa?’
14. Ta yaya za mu nuna cewa mu ‘masu biyayya’ ne?
14 “Mai sauƙin kai.” Kalmar Helenanci da aka fassara “mai-sauƙin kai” ta bayyana a wani wuri a cikin Nassosin Helenanci na Kiristoci. In ji wani manazarci, wannan kalmar “sau da yawa ana amfani da ita a horon soja.” Tana ɗauke da ma’anar “sauƙin rinjaya” da kuma “miƙa kai.” Wanda hikima daga bisa take ja-gorarsa zai miƙa kai ga abin da Nassosi suka ce babu jayayya. Ba za a san shi ba cewa ba ya canja shawararsa ko gaskiya ta rinjaye shi. Maimako, zai yi canji da sauri sa’ad da aka nuna masa tabbaci daga Nassosi cewa ya yi kuskure ko kuma ya tsai da shawarar da ba daidai ba. Haka ne wasu suka san ka?
‘Mai Yawan Tausayi Ce, da Mai Yawan Alheri’
15. Mene ne tausayi, kuma me ya sa ya dace da aka yi amfani da “tausayi” da kuma “yawan alheri” tare a Yakub 3:17?
15 “Mai yawan tausayi ce, mai yawan alheri ce.” c Tausayi ɓangare ne mai muhimmanci na hikima daga bisa, domin iri wannan hikima an ce tana “yawan tausayi.” Ka lura cewa “tausayi” da “yawan alheri” an faɗe su tare. Wannan ya dace domin a Littafi Mai Tsarki, tausayi sau da yawa yana nufin damuwa da wasu, tausayi da yake ba da ’ya’ya da yawa na ayyukan kirki. Wani littafin neman bayani ya ba da ma’anar jinƙai da cewa “jin zafin mummunan yanayi na wani ne, kuma da yin ƙoƙari a yi wani abu a kai.” Saboda haka, hikima ta Allah ba marar daɗaɗa rai ba ce, marar tausayi, ko kuma cike kawai da ilimi. Maimakon haka, tana daɗaɗa rai, tana da tausayi, kuma tana da saurin damuwa. Ta yaya za mu nuna muna cike da jinƙai?
16, 17. (a) Ƙari ga ƙaunar Allah, mene ne yake motsa mu mu yi wa wasu wa’azi, kuma me ya sa? (b) A waɗanne hanyoyi ne za mu nuna cewa muna cike da jinƙai?
16 Hakika hanya mafi kyau ita ce ta wajen gaya wa wasu bisharar Mulkin Allah. Mene ne yake motsa mu mu yi wannan aiki? Ainihi, ƙaunar Allah ce. Jinƙai ko kuma tausayin wasu ma yakan motsa mu. (Matiyu 22:37-39) Da yawa a yau “suna shan wahala kuma ba mai taimako, kamar tumakin da ba su da makiyayi.” (Matiyu 9:36) Makiyaya na addinin ƙarya sun yasar da su kuma sun makantar da su a ruhaniya. Saboda haka, ba su da ja-gora ta hikima da take cikin Kalmar Allah ko kuma albarkar da Mulkin zai kawo ba da daɗewa. Sa’ad da muke yin bimbini bisa bukatu na ruhaniya na waɗanda suka kewaye mu, tausayinmu daga zuciya sai ya motsa mu mu yi dukan abin da za mu iya mu gaya musu game da nufi na ƙauna na Jehobah.
17 A waɗanne hanyoyi ne kuma za mu nuna cewa muna yawan tausayi? Ka tuna misali na Yesu na Basamariye wanda ya iske matafiyi yana kwance a gefen hanya, an yi masa fashi kuma an buge shi. Tausayi ta motsa shi, Basamariyen ya “ji tausayinsa,” ya ɗaɗɗaure raunuka na mutumin. (Luka 10:29-37) Wannan bai nuna cewa jinƙai ya ƙunshi ba da taimako ba, ga waɗanda suke da bukata? Littafi Mai Tsarki ya gaya mana “mu kyautata wa dukan mutane, musamman waɗanda suke ’yan’uwanmu cikin Almasihu.” (Galatiyawa 6:10) Ka bincika wasu yanayi masu yiwuwa. Wani ɗan’uwa da ya tsufa zai bukaci taimako na zuwa da dawowa daga taro na Kirista. Wataƙila gwauruwa a cikin ikilisiya za ta bukaci taimako na wasu gyara a gidanta. (Yakub 1:27) Wanda ya karaya zai bukaci ‘kalmar ƙarfafawa’ don ya wartsake shi. (Karin Magana 12:25) Sa’ad da muka nuna jinƙai a irin waɗannan hanyoyi, muna ba da tabbacin cewa hikima daga bisa tana aiki a cikinmu.
“Ba Ta Nuna Bambanci Ko Munafunci.”
18. Idan hikima daga bisa take yi mana ja-gora, mene ne dole mu kawar daga zuciyarmu, kuma me ya sa?
18 “Ba ta nuna bambanci.” Hikima ta Allah ta nuna bambanci da kuma fahariya ta ƙasa. Idan wannan hikima tana yi mana ja-gora, mu yi ƙoƙari mu kawar da son zuciya daga zuciyarmu. (Yakub 2:9) Ba za mu ɗaukaka wasu ba domin iliminsu, arzikinsu, ko kuma hakkinsu cikin ikilisiya; ko kuma mu raina wani cikin ’yan’uwanmu masu bi, ko yaya ƙasƙantar su ya kasance. Idan Jehobah ya ba waɗannan ƙaunarsa, ya kamata mu ga sun cancanci ƙaunarmu.
19, 20. (a) Mene ne tushen kalmar Helenanci na “munafuki”? (b) Ta yaya za mu nuna “ƙauna ta ainihi,” kuma me ya sa wannan yake da muhimmanci?
19 Ba ya nuna “munafunci.” Kalmar Helenanci ta “munafuki” tana iya nufin “mai wasan kwaikwayo wanda yake wasa.” A zamanin dā, masu wasan kwaikwayo na Helenawa da Romawa suna saka abin rufe fuska sa’an da suke wasa. Saboda haka, kalmar Helenanci “munafuki” ana amfani da ita ga wanda yake ayyukan ƙarya. Wannan ɓangaren hikima ta Allah ya kamata ya rinjayi ba kawai yadda za mu bi da ’yan’uwa masu bi ba amma kuma yadda muke ji game da su.
20 Manzo Bitrus ya lura cewa “yin biyayya ga gaskiya” ya kamata ta sa mu riƙa ‘ƙaunar ’yan’uwanmu da ƙauna ta ainih.’ (1 Bitrus 1:22) Hakika, ƙaunarmu ga ’yan’uwanmu dole ne ta kasance ba sama sama ba kawai. Kada mu zama abin rufe fuska ko kuma mu yi abubuwa kawai domin mu ruɗi wasu. Ƙaunarmu dole ta zama sahihiya, daga zuciya. Idan haka take, ’yan’uwanmu masu bi za su yarda da mu, domin sun sani cewa muna nan yadda muke. Irin wannan gaskiya tana shirya hanyar dangantaka ta gaskiya tsakanin Kiristoci kuma tana taimakawa wajen kawo yarda a cikin ikilisiya.
“Ka Riƙe hikima”
21, 22. (a) Ta yaya Sulemanu ya kasa riƙe hikima? (b) Ta yaya za mu riƙe hikima, kuma ta yaya za mu amfana daga yin haka?
21 Hikima ta Allah kyauta ce daga wajen Jehobah, wadda ya kamata mu kiyaye. Sulemanu ya ce: “Ɗana, . . . ka riƙe hikima da hankali kam-kam.” (Karin Magana 3:21) Abin baƙin ciki, Sulemanu kansa bai yi haka ba. Zai kasance mai hikima muddin ya ci gaba da zuciya mai biyayya. Amma a ƙarshe, matansa baƙi da yawa suka juya zuciyarsa daga bautar Jehobah. (1 Sarakuna 11:1-8) Ƙarshen Sulemanu ya nuna cewa ilimi amfaninsa kaɗan ne idan ba mu yi amfani da kyau da shi ba.
22 Ta yaya za mu riƙe hikima? Ba kawai ya kamata mu karanta Littafi Mai Tsarki ba a kai a kai da kuma littattafai na Littafi Mai Tsarki da “bawan nan mai-aminci, mai-hikima” yake tanadinsa, amma kuma dole ne mu yi ƙoƙarin yin amfani da abin da muka koya. (Matiyu 24:45) Muna da dalili da yawa na yin amfani da hikima ta Allah. Tana nufin rayuwa mafi kyau a yanzu. Tana taimakonmu mu “kafu cikin rai wanda shi ne ainihin rai”—rayuwa a sabuwar duniya ta Allah. (1 Timoti 6:19) Kuma mafi muhimmanci ma, koyon hikima da take fitowa daga bisa za ta matso da mu kusa da Tushen dukan hikima, Jehobah Allah.
a In ji 1 Sarakuna 3:16, mata biyun karuwai ne. Insight on the Scriptures ya ce: “Waɗannan matan karuwai ne, ba kamar kilakawa ba, amma mata ne da suka yi fasikanci, ko matan Yahudawa, ko kuma wataƙila, mata baƙi.”—Shaidun Jehobah ne suka buga.
b Furucin Helenanci da aka fassara “ka shirya” yana nufin “daina zama maƙiyin amma a ƙulla abuta; a sasanta matsaloli da sake soma yin abokantaka ko kuma yin abubuwa da haɗin kai.” Domin burinka ka kawo canji ne, ka cire, idan zai yiwu, fushi daga zuciyar da aka yi wa laifi.—Romawa 12:18.
c Wata fassara ta fassara waɗannan kalmomi “cike da jinƙai da kuma nagarin ayyuka.”—A Translation in the Language of the People, na Charles B. Williams.