BABI NA 4
Jehobah “Mai Girma Ne”
1, 2. Waɗanne abubuwa masu ban-mamaki ne Iliya ya gani a rayuwarsa, amma waɗanne abubuwa mafi ban-mamaki ne ya gani daga kogo a Dutsen Horeb?
ILIYA ya ga abubuwa masu ban mamaki da yawa a dā. A lokacin da yake ɓoye, ya ga hankaka ta kawo masa abinci sau biyu a rana. Ya ga tukunya ba ta rasa gari ba da kuma tulun māi ba ta bushe ba a lokacin da aka yi wani fari mai tsanani sosai a ƙasar. Ya ma ga an amsa addu’ar da ya yi cewa wuta ta faɗo daga sama. (1 Sarakuna, surori 17, 18) Duk da haka, Iliya bai taɓa ganin wani abu irin wannan ba.
2 Da ya durƙusa a bakin kogo a Dutsen Horeb, ya ga abubuwa masu ban mamaki bi-da-bi. Ta farko iska ce. Wataƙila ta yi ƙara, ta yi gurnani da ƙarfi, domin tana da ƙarfi sosai, ta tsaga dutse kuma ta wargaza tuddai. Na gaba kuma girgizar ƙasa ce, da ƙarfi mai yawa da ke rufe can cikin ƙasa. Sai wuta ta biyo baya. Ta share yankin, wataƙila Iliya ya ji zafin ƙunarta.—1 Sarakuna 19:8-12.
3. Iliya ya ga tabbacin wane hali ne na Allah, kuma a ina ne za mu ga tabbacin irin wannan halin?
3 Dukan waɗannan abubuwa dabam-dabam da Iliya ya gani suna da abu iri ɗaya, sun nuna iko mai girma na Jehobah. Hakika, ba ma bukatar ganin mu’ujiza don mu fahimci cewa Allah yana da iko. Wannan a bayyane yake. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa halitta tana bayyana “halin Allahntaka na Allah da kuma ikonsa.’ (Romawa 1:20) Ka yi tunanin haske mai kashe ido na walƙiya da ƙarar tsawa da ruwan da ke saukowa daga tudu, da kuma yawan taurari da ke sama! Babu shakka, abubuwan nan sun nuna cewa Allah yana da iko. Duk da haka, mutane kaɗan ne kawai a yau suka yarda da ikon Allah. Har ila, mutane ƙalilan ne suka ɗauke shi yadda ya dace. Amma fahimtar wannan hali na Allah tana ba mu dalilai na kusantar Jehobah. A wannan sashen, za mu yi nazarin ikon Jehobah da babu kamarsa.
“Sai [Jehobah] ya wuce ta wurin”
Hali Mai Muhimmanci na Jehobah
4, 5. (a) Ta yaya aka kwatanta sunan Jehobah? (b) Me ya sa ya dace da Jehobah ya zaɓi bijimi ya kwatanta ikonsa?
4 Jehobah ya fi kowa iko. Irmiya 10:6 ta ce: “Ya Yahweh, babu wani kamarka! Kai mai girma ne, sunanka mai girma ne da iko sosai.” Ka lura cewa ayar ta ce sunan Jehobah yana da girma da kuma iko sosai. Ka tuna cewa, sunansa yana nufin “Yakan Sa Ya Kasance.” Me yake sa Jehobah ya sa kansa ya kasance dukan abin da ya zaɓa? Abu ɗaya shi ne iko. Hakika, iyawar Jehobah ya aikata abu, ya cika nufinsa, ba shi da iyaka. Irin wannan ikon yana ɗaya daga cikin halayensa masu muhimmanci.
5 Domin ba za mu iya samun cikakkiyar fahimtar ikonsa ba, Jehobah ya yi amfani da kwatanci domin ya taimake mu. Kamar yadda muka gani, ya yi amfani da bijimi ya kwatanta ikonsa. (Ezekiyel 1:4-10) Kwatancin nan ya dace, domin bijimi na gida ma yana da girma kuma dabba ne mai ƙarfi. Da ƙyar mutanen Palasɗinu na zamanin Littafi Mai Tsarki suke saduwa da abin da ya fi shi ƙarfi. Amma sun san wani bijimi mafi ban tsoro, wato wani irin bijimin daji, ko kuma ɓauna, waɗanda sun ƙare da jimawa. (Ayuba 39:9-12) Yuliyas Kaisar, shugaban Roma ya ce waɗannan bijimai da kaɗan giwa ta ɗara su. Ya ce: “Ƙarfinsu da yawa yake, kuma suna da gudu sosai.” Ka yi tunanin yadda za ka ƙanƙance kuma yadda za ka kasala idan kana tsaye kusa da irin wannan dabbar!
6. Me ya sa Jehobah ne kaɗai ake kira “Mai-iko duka”?
6 Hakazalika, mutum ajizi ne marar ƙarfi idan aka gwada shi da Jehobah, Allah mai iko. A gare shi, al’ummai masu girma ma kamar ƙura mai laushi a bisa mizani suke. (Ishaya 40:15) Ba kamar kowacce halitta ba, ikon Jehobah babu iyaka, domin shi kaɗai ake kira “Mai-iko duka.” a (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 15:3) Jehobah yana da “yawan ƙarfi” da kuma “girman iko.” (Ishaya 40:26) Shi ne Tushen iko marar ƙarewa. Bai dogara ba ga wani tushen ƙarfi daga waje, domin “iko na Allah ne.” (Zabura 62:11) Amma ta wace hanya ce Jehobah yake nuna ikonsa?
Yadda Jehobah Yake Nuna Ikonsa
7. Mene ne ruhu mai tsarki na Jehobah, kuma mece ce kalma ta asali ta harshen take nufi da aka yi amfani da ita a cikin Littafi Mai Tsarki?
7 Jehobah yakan zubo da ruhu mai tsarki babu iyaka. Ikon Allah ne cikin aiki. Hakika, a Farawa 1:2, NW, Littafi Mai Tsarki ya ambace shi da cewa “ikon aiki” na Allah. A kalma ta asalin Ibrananci da kuma Helenanci da aka fassara “ruhu” a wasu wurare, za a iya fassara ta “iska,” “numfashi,” da kuma “guguwa.” In ji mawallafan ƙamus, kalma ta asali ta yaren tana nufin iko da ba a gani amma yana aiki. Kamar iska, ruhun Allah ba ya ganuwa ga idanunmu, amma ana gani kuma ana fahimtar ayyukansa.
8. A cikin Littafi Mai Tsarki, mene ne aka kira ruhu mai tsarki a alamance, kuma me ya sa waɗannan kwatanci sun dace?
8 Ruhu mai tsarki na Allah mai canzawa ne. Jehobah yana yin amfani da shi ya cika dukan nufin da yake da shi a zuci. Saboda haka ne a cikin Littafi Mai Tsarki aka kira ruhun Allah a alamance “yatsu,” ko kuma “hannunsa mai iko.” (Luka 11:20; Maimaitawar Shari’a 5:15; Zabura 8:3) Kamar yadda mutum zai yi amfani da hannunsa wajen yin ayyuka dabam dabam da suke bukatar ƙarfi da ya bambanta, haka ma Allah yana iya amfani da ruhunsa ya cika kowanne nufinsa, kamar su halittar atam ɗan mitsitsi ko kuma tsaga Jar Teku ko kuma sa Kiristoci na farko su yi magana a wasu harsuna.
9. Yaya yawan ikon sarauta na Jehobah yake?
9 Jehobah kuma yana nuna ikonsa ta wajen ikonsa na Mamallakin Dukan Halitta. Za ka iya tunanin kana da bayi miliyoyi bisa miliyoyi masu basira da suke a shirye su bi umurninka? Jehobah yana da irin wannan ikon sarauta. Yana da bayi mutane, a cikin Nassosi sau da yawa an kwatanta su da runduna. (Zabura 68:11; 110:3) Mutum halitta ne marar ƙarfi, idan aka gwada shi da mala’ika. Shi ya sa, sa’ad da rundunar Assuriyawa suka kai wa mutanen Allah farmaki, mala’ika guda ya kashe sojoji 185,000 a dare ɗaya! (2 Sarakuna 19:35) Mala’ikun Allah “masu ƙarfi da iko” ne.—Zabura 103:19, 20.
10. (a) Me ya sa aka kira Mai Iko Duka, Jehobah mai runduna? (b) Wane ne ne mafi girma a dukan halittar Jehobah?
10 Mala’iku nawa ne ake da su? Annabi Daniel ya ga wahayin sama, a ciki ya ga mala’iku fiye da miliyan 100 a gaban kursiyin Jehobah, amma babu alamar cewa ya ga dukan mala’ikun. (Daniyel 7:10) Saboda haka, wataƙila da akwai mala’iku ɗarurruwan miliyoyi. Saboda haka ake kiran Jehobah mai runduna. Wannan laƙabi yana kwatanta matsayinsa mai girma na Kwamandan babbar ƙungiya ta mala’iku masu iko. A kan dukan waɗannan ruhohi, ya ɗora shugaba, Ɗansa wanda yake ƙauna, “ɗan fari ne gaban dukan halitta.” (Kolossiyawa 1:15) Tun da shi ne babban mala’ika, shugaban dukan mala’iku, seraf da kerub, Yesu shi ne mafi girma a dukan halittar Jehobah.
11, 12. (a) A waɗanne hanyoyi ne maganar Allah take iko? (b) Ta yaya Yesu ya yi shaidar yawan ikon Jehobah?
11 Jehobah har yanzu yana da wata hanyar nuna iko. Ibraniyawa 4:12 ta ce: “Kalmar Allah tana da rai, tana da ƙarfin aiki kuma.” Ka lura da ƙarfin kalmar Allah bisa hankali ko kuma saƙo da ruhu ya hure, da aka adana yanzu cikin Littafi Mai Tsarki? Zai iya ƙarfafa mu, ya gina bangaskiyarmu, kuma su taimake mu mu yi gyara sosai a rayuwarmu. Manzo Bulus ya gargaɗi ’yan’uwa masu bi game da mutane da suke duƙufa cikin salon rayuwa ta lalata. Sai ya daɗa cewa: “Haka waɗansunku ma suke dā.” (1 Korintiyawa 6:9-11) Hakika, “Kalmar Allah” ta yi iko a kansu kuma ta taimake su suka gyaru.
12 Ikon Jehobah da girma yake kuma hanyar nuna shi tana da ƙarfi sosai da babu wanda zai iya hana shi. Yesu ya ce: “Ga Allah kowane abu mai yiwuwa ne.” (Matiyu 19:26) Ga waɗanne nufe-nufe ne Jehobah yake amfani da ikonsa?
Iko da Ƙuduri Ke Ja-Gora
13, 14. (a) Me ya sa za mu iya cewa Jehobah ba tushe ba ne kawai marar rai na ƙarfi? (b) A waɗanne hanyoyi ne Jehobah yake amfani da ikonsa?
13 Ruhun Jehobah ya fi dukan wani ƙarfi na zahiri; kuma Jehobah ba ƙarfi ba ne da ba shi da rai, ko kuma kawai wani tushen ƙarfi. Shi Allah ne mai rai wanda yake iko da ƙarfinsa. Amma, me yake motsa shi ya yi amfani da ikonsa?
14 Kamar yadda za mu gani, Allah yana amfani da iko ya halitta, ya halaka, ya kāre, kuma ya yi gyara, wato, ya yi dukan abin da ya dace da kamiltaccen nufe-nufensa. (Ishaya 46:10) A wasu lokatai, Jehobah yana amfani da ikonsa ya bayyana muhimman fannin mutuntakarsa da kuma mizanai. Mafi muhimmanci ma, yana amfani da ikonsa ya cika nufinsa, wato ya tsarkake sunansa mai tsarki ta wajen Mulkin Almasihu kuma ya nuna cewa sarautarsa ce ta fi. Babu abin da zai iya taka wannan nufin.
15. Jehobah ya yi amfani da ikonsa domin wane nufi ne da ke haɗe da bayinsa, kuma yaya aka kwatanta wannan a batun Iliya?
15 Jehobah yana amfani da ikonsa ya amfane kowannenmu. Ka lura da abin da 2 Labarbaru 16:9 ta ce: “Idanun Yahweh suna kai da kawowa ko’ina a duniya domin ya ƙarfafa waɗanda suka dogara gare shi da zuciya ɗaya.” Wani misali shi ne abin da Iliya ya fuskanta, da aka ambata da farko. Me ya sa Jehobah ya nuna masa wannan iko? Muguwar sarauniya Jezebel ta rantse cewa sai ta sa an kashe Iliya. Annabin ya yi gudun ransa. Ya ji ya kaɗaita, ya tsorata, kuma ya kasala, kamar dukan aikinsa da ƙwazo ya zama banza. Don ya ƙarfafa mutumin da yake wahala, Jehobah ya tuna wa Iliya ikonsa. Iskar, da girgizar ƙasa, da wuta sun nuna cewa Mafi ƙarfi a dukan sararin sama yana tare da Iliya. Me zai tsorata daga Jezebel da yake Allah mai iko duka yana tare da shi?—1 Sarakuna 19:1-12. b
16. Me ya sa za mu ƙarfafa ta wajen bimbini bisa iko mai girma na Jehobah?
16 Ko da yake yanzu ba lokacinsa ba ne na yin mu’ujiza, Jehobah bai canja ba tun daga zamanin Iliya. (1 Korintiyawa 13:8) A yau, yana ɗokin ya yi amfani da ikonsa domin waɗanda suke ƙaunarsa. Hakika, yana mazaunin ruhu, amma ba shi da nisa daga gare mu. Ikonsa ba shi da iyaka, saboda haka, nisa ba wani abu ba ne. Maimakon haka, “Yahweh yana kurkusa ga masu kira gare shi.” (Zabura 145:18) Wani lokaci da annabi Daniyel ya kira bisa Jehobah domin taimako, mala’ika ya bayyana kafin ma ya gama addu’arsa! (Daniyel 9:20-23) Babu abin da zai hana Jehobah taimakon waɗanda yake ƙauna kuma ya ƙarfafa su.—Zabura 118:6.
Ikon Allah Ya Sa Ba Za A Iya Kusantarsa Ba Ne?
17. A wace hanya ce ikon Jehobah yake sa mu tsoro, amma wane irin tsoro ne ba ya kawowa?
17 Ikon Jehobah ya kamata ya sa mu tsorace shi ne? Dole ne mu amsa e, da kuma a’a. E, saboda wannan halin ya ba mu isashen dalilai domin tsoro na ibada, girmamawa da kuma darajawa da muka tattauna a babi na baya. Irin wannan tsoron, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa “mafarin hikima ne.” (Zabura 111:10) Za mu kuma ce a’a, domin ikon Allah bai ba mu dalilin razana ba dominsa ko kuma mu guji matsowa kusa da shi.
18. (a) Me ya sa mutane da yawa ba su yarda da mutane masu iko ba? (b) Ta yaya muka sani cewa ikon Jehobah ba zai lalata shi ba?
18 “Iko yana lalatarwa; cikakken iko yana lalatarwa gabaki ɗaya.” Haka ɗan tarihin Ingilishi Lord Acton ya rubuta a shekara ta 1887. Wannan furucin nasa an maimaita shi sau da yawa, wataƙila domin mutane da yawa suna ganin gaskiya ce da ba za a yi jayayya da ita ba. Mutane ajizai sau da yawa suna ɓarna da iko, kamar yadda tarihi ya nuna a kai a kai. (Mai-Wa’azi 4:1; 8:9) Domin wannan, mutane da yawa ba sa yarda da masu iko kuma suna janyewa daga gare su. Amma, Jehobah yana da cikakken iko. Akwai hanya ce da ya lalata shi? Hakika babu! Kamar yadda muka gani, mai tsarki ne, ba shi da lalata ko ɗis. Jehobah ba kamar mutane ajizai ba ne masu iko a wannan lalatacciyar duniya. Bai taɓa cin zali ba, kuma ba zai taɓa cin zali ba.
19, 20. (a) Cikin jituwa da waɗanne halaye ne Jehobah koyaushe yake nuna ikonsa, kuma me ya sa wannan yana da ban tabbaci? (b) Ta yaya za mu kwatanta kamewa na Jehobah, kuma me ya sa wannan yake da kyau a gare ka?
19 Ka tuna cewa, iko ba shi ne kaɗai ba halin Jehobah. Har yanzu ba mu yi nazarin shari’arsa ba, hikimarsa, da kuma ƙaunarsa. Amma bai kamata mu yi tsammanin cewa halayen Jehobah suna bayyana ne kawai ɗaɗɗaya ba, kamar dai a ce ɗaya zai bayyana a lokaci guda. Akasarin haka, za mu gani a babi na gaba cewa koyaushe Jehobah yana nuna ikonsa ne cikin jituwa da shari’arsa, hikimarsa, da kuma ƙaunarsa. Ka yi tunanin wani hali da Allah yake da shi, wanda ba a samu wurin sarakunan duniya, wato kamewa.
20 Ka yi tunanin ka sadu da mutum mai ƙiba kuma ga ƙarfi har ya tsorata ka. Amma, daga baya ka lura cewa yana da kirki. Koyaushe a shirye yake ya yi amfani da ƙarfinsa ya kāre mutane, musamman waɗanda ba su da mai kāre su da kuma marasa ƙarfi. Bai taɓa cin zali ba. Ana zaginsa babu dalili, duk da haka halinsa ga mutane a kafe yake yana kama kai, da daraja, har ma da kirki. Kana mamaki idan za ka iya nuna irin kirki da kuma kamewar nan, musamman ma idan kana da ƙarfinsa! Yayin da ka san wannan mutumin ba za ka fara matsowa kusa da shi ba? Muna da dalili mafi girma na kusantar Jehobah mai iko duka. Ka lura da cikakkiyar jimla da ta ba da jigon wannan babin: Jehobah “ba mai saurin fushi ba ne, amma mai iko ne shi.” (Nahum 1:3) Jehobah ba ya saurin yin amfani da ikonsa gaba da mutane, har ma miyagu. Mai jinkirin fushi ne kuma mai kirki. Ya tabbatar da cewa shi “ba mai saurin fushi ba ne” duk da yawan tsokana da ake yi masa.—Zabura 78:37-41.
21. Me ya sa Jehobah yake kame kansa daga tilasta wa mutane su yi nufinsa, kuma mene ne wannan ya nuna mana game da shi?
21 Ka lura da kamewa na Jehobah a wata hanya dabam. Idan kana da iko babu iyaka, a wasu lokatai, kana tsammanin za ka so ka sa mutane su yi abubuwa yadda kake so? Jehobah, da dukan ikonsa, ba ya tilasta wa mutane su bauta masa. Ko da yake bauta wa Allah shi ne kawai hanyar rai madawwami, Jehobah bai tilasta mana ba mu yi wannan bautar. Maimakon haka, ya daraja kowa da ’yancin zaɓe. Ya yi gargaɗi game da sakamakon mummunan zaɓe kuma ya faɗi ladar kyakkyawan zaɓe. Amma, ya bar mu mu yi zaɓen kanmu. (Maimaitawar Shari’a 30:19, 20) Jehobah ba ya son a bauta masa dole ko kuma cikin tsoron ikonsa mai ban tsoro. Yana neman waɗanda za su bauta masa da son rai, cikin ƙauna.—2 Korintiyawa 9:7.
22, 23. (a) Me ya nuna cewa Jehobah yana farin ciki ya ba wasu iko? (b) Mene ne za mu bincika a babi na gaba?
22 Bari mu ga dalili na ƙarshe da ya sa bai kamata mu rayu cikin razanar Allah Mai Iko Duka ba. Mutane masu iko suna tsoron ba wa wasu iko. Amma, Jehobah yana farin cikin ba wa amintattun bayinsa iko. Yana ba wasu iko da ya dace, kamar Ɗansa. (Matiyu 28:18) Jehobah kuma yana ba wa bayinsa iko a wata hanya. Littafi Mai Tsarki ya yi bayani: “Ya Yahweh, girma da iko naka ne! Ɗaukaka da kuma daraja da nasara naka ne gama kome a sama da ƙasa naka ne. . . . A hannunka ne ƙarfi da iko suke, ikon girmama mutum da ikon ƙarfafa shi.”—1 Tarihi 29:11, 12.
23 Hakika, Jehobah zai yi farin ciki ya ba ka ƙarfi. Yana bayar da “cikakken ikon da ya fi duka” ga waɗanda suke so su bauta masa. (2 Korintiyawa 4:7) Ba ka ji kana so ka matso kusa da wannan Allah mai ƙarfi ba, wanda yake yin amfani da ikonsa a wannan hanya ta kirki da kuma ƙa’ida? A babi na gaba, za mu mai da hankali ga yadda Jehobah yake amfani da ikonsa ya yi halitta.
a Kalmar Helenanci da aka fassara “Mai-iko duka” a zahiri tana nufin “Mai Iko Bisa Kowa; Wanda Yake da Dukan Iko.”
b Littafi Mai Tsarki ya ce Jehobah “ba ya cikin iskar . . . , rawar ƙasar . . . da wutar.” Ba kamar masu bauta wa allolin ƙage ba, bayin Jehobah ba sa nemansa cikin ikon halitta. Ya fi ƙarfin a neme shi cikin dukan wani abin da ya halitta.—1 Sarakuna 8:27.