Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 11

Ka Yi Magana da Kuzari

Ka Yi Magana da Kuzari

Romawa 12:11

ABIN DA ZA KA YI: Ka ƙarfafa masu sauraronka ta wurin yin magana da himma.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Ka fahimci batun da kyau. A lokacin da kake shiri, ka yi tunani sosai a kan muhimmancin saƙon. Ka san batun sosai domin ka iya bayyana shi daga zuciyarka.

  • Ka yi tunani a kan masu sauraronka. Ka yi tunani a kan yadda masu sauraro za su amfana daga abin da za ka karanta ko kuma koyar. Ka yi tunani a kan hanyoyin da za ka gabatar da saƙon da kyau don masu sauraronka su amfana.

  • Ka sa jawabin ya yi daɗi. Ka yi magana da himma. Motsin hannayenka, da yanayin fuskarka su nuna yadda kake ji game da batun da kake tattaunawa.