Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 20

Kammalawa Mai Dadi

Kammalawa Mai Dadi

Mai-Wa’azi 12:​13, 14

ABIN DA ZA KA YI: Sa’ad da kake kammalawa, ka taimaka wa masu sauraronka su amince da abin da ka faɗa kuma su yi amfani da shi.

YADDA ZA KA YI HAKAN:

  • Kammalawarka ta yi daidai da jigon jawabinka. Ka sake maimaita muhimman batutuwan da ke jawabinka.

  • Ka ƙarfafa masu sauraronka. Ka nuna wa masu sauraronka abin da za su yi da kuma dalilin da ya sa za su yi hakan. Ka yi magana da tabbaci.

  • Kammalawarka ta zama mai sauƙi kuma gajere. Kada ka ƙara batutuwan da ba ka sa su cikin jawabinka ba. Ka kammala da kalamai kaɗan sa’ad da kake ƙarfafa masu sauraronka su yi amfani da abin da suka koya.