BABI NA 1
“Kaunar Allah Ke Nan”
“Gama ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.”—1 YOHANNA 5:3.
1, 2. Menene ya motsa ka ka ƙaunaci Jehobah Allah?
KANA ƙaunar Allah? Idan ka keɓe kanka ga Jehobah Allah, hakika amsarka za ta zama E ce, kuma hakan daidai ne! Babu wata abin da tafi mu ƙaunaci Jehobah. Muna ƙaunar Allah ne domin yana ƙaunarmu. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Muna ƙauna, domin shi ne ya fara ƙaunarmu.’—1 Yohanna 4:19.
2 Jehobah ya nemi zarafin ya nuna ƙaunarsa a gare mu. Ya yi mana tanadin duniya kyakkyawa ta kasance gidanmu. Yana kuma kula da bukatunmu na zahiri. (Matta 5:43-48) Mafi muhimmanci ma, yana kula da bukatunmu na ruhaniya. Ya ba mu Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Ƙari ga haka, ya gayyace mu mu yi addu’a zuwa gare shi da tabbacin cewa zai saurare mu ya kuma ba mu ruhunsa domin ya taimake mu. (Zabura 65:2; Luka 11:13) Mafi muhimmanci, ya aiko da Ɗansa mafi tamani ya fanshe mu domin a kuɓutar da mu daga zunubi da kuma mutuwa. Hakika, Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunarmu sosai!—Karanta Yohanna 3:16; Romawa 5:8.
3. (a) Domin mu kasance cikin ƙaunar Allah, menene ake bukata a gare mu? (b) Wace tambaya ce mai muhimmanci muke bukatar mu yi la’akari da ita, kuma a ina za a sami amsarta?
3 Jehobah yana so mu amfana daga ƙaunarsa har abada. Ko za mu amfana ko ba za mu amfana ba, wannan ya Yahuda 21) Furcin nan “ku tsare kanku,” yana nuna cewa idan muna son mu kasance cikin ƙaunar Allah, muna bukatar mu ɗauki mataki. Muna bukatar mu nuna cewa muna ƙaunarsa ta ƙwaƙƙwarar hanyoyi. Saboda haka, wata tambaya mai muhimmanci da muke bukatar mu yi la’akari da ita, ita ce, ‘Ta yaya zan nuna ƙauna ta ga Allah?’ An sami amsar a hurarrun kalmomin manzo Yohanna: “Ƙaunar Allah ke nan, mu kiyaye dokokinsa: dokokinsa fa ba su da ban ciwo ba.” (1 Yohanna 5:3) Muna bukatar mu bincika ma’anar waɗannan kalmomi a hankali, domin muna son mu nuna wa Allah yawan ƙaunar da muke yi masa.
dangana ne a gare mu. Kalmar Allah ta ce mana: “Ku tsare kanku cikin ƙaunar Allah, . . . zuwa rai na har abada.” (“ƘAUNAR ALLAH KE NAN”
4, 5. (a) Ga menene wannan furci “ƙaunar Allah” yake nuni? (b) Ka kwatanta yadda ƙaunar Jehobah ta fara ƙarfi a zuciyarka.
4 “Ƙaunar Allah,” menene manzo Yohanna yake nufi sa’ad da ya rubuta waɗannan kalmomin? Wannan furcin yana magana ne, ba a kan ƙaunar da Allah yake yi mana ba, amma a kan ƙaunar da muke yi masa. Za ka iya tuna lokacin da ƙaunar Jehobah ta fara ƙarfi a zuciyarka?
5 Ka tuna lokacin da ka koyi gaskiya game da Jehobah da kuma nufe nufensa kuma ka fara ba da gaskiya. Ka zo ka fahimci cewa ko da yake an haife ka mai zunubi bare ga Allah, Jehobah ta wurin Kristi ya buɗe hanya domin ka sami kamilta da Adamu ya yi hasara da kuma rai madawwami. (Matta 20:28; Romawa 5:12, 18) Ka fara fahimtar irin sadaukarwar da Jehobah ya yi wajen aiko Ɗansa da ya fi ƙauna don ya mutu dominka. Hakan ya motsa zuciyarka, kuma ka fara ƙaunar Allahn da ya nuna maka irin wannan ƙauna mai girma.—Karanta 1 Yohanna 4:9, 10.
6. Ta yaya ake nuna ƙauna ta gaskiya, kuma menene ƙaunar Allah ta motsa ka ka yi?
6 Amma wannan, mafari ne kawai na ƙauna ta gaskiya da kake yi wa Jehobah. Ƙaunar ba kawai yadda mutum yake ji ba ne; ba kuma kawai batun kalmomi ba ne. Ƙauna ta gaskiya ga Allah ta fi kawai mutum ya ce, “Ina ƙaunar Jehobah.” Kamar bangaskiya, ƙauna ta gaskiya tana bayyana ne ta wajen irin ayyuka da ta motsa mutum ya yi. (Yaƙub 2:26) Musamman, ƙauna tana nuna kanta ta wajen yin ayyukan da suke faranta wa wanda muke ƙauna rai. Saboda haka, sa’ad da ƙaunar Jehobah ta yi ƙarfi a zuciyarka, hakan ya motsa ka ka so yin rayuwa a hanyar da za ta faranta wa Ubangijinka na samaniya rai. Kai Mashaidi ne da ya yi baftisma? Idan haka ne, wannan ƙaunar da kuma bauta sun motsa ka ka yanke shawara mafi muhimmanci a rayuwarka. Ka keɓe kanka ga Jehobah domin ka yi nufinsa, kuma ka nuna alamar keɓe kanka ta wajen yin baftisma. (Karanta Romawa 14:7, 8) Cika wannan alkawarin naka ga Jehobah ya ƙunshi abin da manzo Yohanna ya faɗa a gaba.
“MU KIYAYE DOKOKINSA”
7. Menene wasu dokokin Allah, kuma menene kiyaye waɗannan ya ƙunsa?
7 Yohanna ya yi bayani game da abin da ƙaunar Allah take nufi: “Mu kiyaye dokokinsa.” Menene dokokin Allah? Jehobah ya ba mu wasu takamammun dokoki a cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Alal misali, ya hana irin halayen nan kamarsu yin maye, fasikanci, bautar gumaka, sata, da kuma ƙarya. (1 Korintiyawa 5:11; 6:18; 10:14; Afisawa 4:28; Kolossiyawa 3:9) Kiyaye dokokin Allah sun ƙunshi yin rayuwar da ta jitu da mizanan ɗabi’a na Littafi Mai Tsarki.
8, 9. Ta yaya za mu fahimci abin da ke faranta wa Jehobah rai har a yanayin da babu wata doka takamaimai daga Littafi Mai Tsarki da ta yi magana a kan batun? Ka ba da misali.
8 Domin mu faranta wa Jehobah rai, muna bukatar mu yi fiye da kiyaye dokokinsa na kai tsaye kawai. Jehobah bai taƙure mu ba da dokokin da suke yi mana ja-gora a dukan fannonin rayuwarmu ta yau da kullum. Saboda haka, a rayuwarmu ta kullum, za mu iya fuskantar yanayi masu yawa da babu takamaiman doka da ta shafe su daga Littafi Mai Tsarki. A irin waɗannan yanayi, ta yaya za mu san abin da zai faranta wa Jehobah rai? Littafi Mai Tsarki ya ƙunshi bayanan da suka nuna yadda Allah yake tunani. Sa’ad da muke nazarin Littafi Mai Tsarki, muna koyan abin da Jehobah yake ƙauna da kuma abin da yake ƙyama. (Karanta Zabura 97:10; Misalai 6:16-19) Mun fahimci irin halaye da ayyukan da yake so. Yayin da muke ƙara koyon halayen Jehobah da kuma hanyoyinsa, hakan zai ƙara motsa mu mu ƙyale tunaninsa ya mulmula shawarwarinmu ya kuma rinjayi ayyukanmu. Ta haka, har a yanayi ma da babu takamaiman doka daga Littafi Mai Tsarki, za mu iya fahimtar “nufin Ubangiji.”—Afisawa 5:17.
9 Alal misali, babu takamaiman doka a cikin Littafi Mai Tsarki da ta ce kada mu kalli finafinai ko kuma wasanni a talabijin da suka ƙunshi nuna ƙarfi ko lalata. Amma lalle ne muna bukatar takamaiman doka game da kallon irin waɗannan abubuwa? Mun san yadda Jehobah yake ɗaukan irin waɗannan batutuwan. Kalmarsa ta gaya mana cewa: “Mai-mugunta da mai-son zalunci [ran Jehobah] yana ƙinsu.” (Zabura 11:5) Ya kuma ce: “Da fasikai da mazinata Allah za shi shar’anta.” (Ibraniyawa 13:4) Ta wajen mai da hankali ga waɗannan kalmomin da aka hure, za mu fahimci nufin Jehobah sosai. Saboda haka, za mu ƙi kallon ayyukan da Allahnmu yake ƙyama. Mun san cewa za mu faranta wa Jehobah rai idan muka guji mugun ɗabi’a na salon wasanni da wannan duniyar take sayarwa don ta ruɗi mutane. *
10, 11. Me ya sa muka zaɓi tafarkin biyayya ga Jehobah, kuma wace irin biyayya ce muke yi masa?
10 Menene ainihin dalilin da ya sa muke kiyaye dokokin Allah? Me ya sa a kullum za mu so mu yi abin da muka san cewa Allah yana so? Ba wai muna bin irin wannan tafarkin ba ne ba kawai domin mu guji hukunci ko kuma miyagun sakamakon da waɗanda suka ƙi yin nufin Allah suke fuskanta. (Galatiyawa 6:7) Maimakon haka, muna ɗaukan biyayya ga Jehobah a matsayin zarafi ne na nuna cewa muna ƙaunarsa. Kamar yaron da yake ɗokin samun yardan babansa, haka muke so mu sami yardan Jehobah. (Zabura 5:12) Shi Ubanmu ne, kuma muna ƙaunarsa. Babu wani abin da zai faranta mana rai ko kuma ya gamsar da mu fiye da sanin cewa muna rayuwa a hanyar da ta “sami tagomashi a wurin Ubangiji.”—Misalai 12:2.
11 Saboda haka, biyayyarmu ba ta dole ba ce; ko kuma sai mun ga dama. * Ba ma zaɓan mu yi biyayya a lokacin da muka ga yana da sauƙi ko kuma sa’ad da yin hakan ba zai kasance da wani ƙalubale ba. Akasin haka, muna ‘biyayya da zuciya ɗaya.’ (Romawa 6:17) Muna ji kamar mai zabura na Littafi Mai Tsarki wanda ya rubuta: “Zan yi daula kuma da dokokinka, waɗanda na ƙaunace su.” (Zabura 119:47) Hakika, muna ƙaunar mu yi wa Jehobah biyayya. Mun fahimci cewa, ya cancanci kuma yana bukatar cikakken biyayya daga gare mu. (Kubawar Shari’a 12:32) Muna so Jehobah ya ce mana abin da Kalmarsa ta ce game da Nuhu. Game da wannan uban iyali mai aminci, wanda ya nuna ƙauna ga Allah ta wajen yin biyayya na shekaru masu yawa, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hakanan kuwa Nuhu ya yi; bisa ga abin da Allah ya umurce shi duka, haka ya yi.”—Farawa 6:22.
12. A wane lokaci ne biyayyarmu take faranta wa Jehobah rai?
12 Yaya Jehobah yake ji game da biyayyar da muke yi da son rai? Kalmarsa ta ce muna sa shi “farin ciki.” (Misalai 27:11) Da gaske ne biyayyarmu tana faranta wa Mai Iko duka rai? Hakika, tana faranta masa rai, kuma yana da dalilin yin haka! Jehobah ya halicce mu da ’yancin zaɓe. Wannan ya nuna cewa za mu iya zaɓan mu yi wa Allah biyayya ko kuma mu ƙi yi masa biyayya. (Kubawar Shari’a 30:15, 16, 19, 20) Idan muka zaɓi yi wa Jehobah biyayya da son rai, kuma idan dalilin yin hakan shi ne ƙaunar Allah da ke zuciyarmu, za mu sa Ubanmu na samaniya farin ciki ƙwarai. (Misalai 11:20) Da haka kuma mun zaɓi hanyar rayuwa mafi kyau ke nan.
“DOKOKINSA FA BA SU DA BAN CIWO”
13, 14. Me ya sa za a ce ‘dokokin Allah fa ba su da ban ciwo,’ kuma ta yaya za mu kwatanta wannan?
13 Manzo Yohanna ya gaya mana wani abu mai ban ƙarfafa game da bukatun Jehobah: “Dokokinsa fa ba su da ban ciwo.” Kalmar Helenanci da aka fassara “ban ciwo” a 1 Yohanna 5:3 a zahiri tana nufin “nauyi.” * Wata fassarar Littafi Mai Tsarki a nan ta ce: “Dokokinsa ba sa yi mana nauyi.” (New English Translation) Dokokin Jehobah ba na rashin hankali ba ne ko kuma masu ban ciwo. Dokokinsa ba su fi ƙarfin ’yan adam ba.
14 Za mu iya kwatanta batun kamar haka. Wani aboki na kud da kud ya ce ka taimake shi ya ƙaura zuwa wani gida. Da akwatuna masu yawa da za a kwashe. Wasu ba su da nauyi sosai, mutum ɗaya zai iya ɗaukansu, amma wasu suna da nauyi ƙwarai kuma suna bukatar mutane biyu su ɗauka. Abokinka ya zaɓi waɗanda yake so ka taya shi ɗauka. Kana ganin zai ce ka ɗauki akwatuna ne da ya san cewa ba za ka iya ɗauka ba? A’a. Ba zai so ka ji wa kanka rauni ba ta wajen ɗaukan su kai kaɗai. Hakazalika, Allahnmu mai ƙauna mai alheri, ba zai bukaci mu kiyaye dokokin da suke da wuyar kiyaye wa Kubawar Shari’a 30:11-14) Ba zai taɓa cewa mu ɗauki irin wannan nauyin ba. Jehobah ya san abin da ba za mu iya yi ba, domin “ya san tabi’ammu; Ya kan tuna mu turɓaya ne.”—Zabura 103:14.
ba. (15. Me ya sa za mu yarda cewa dokokin Jehobah domin amfaninmu ne?
15 Dokokin Jehobah ba su da ban ciwo; an yi su ne domin amfaninmu. (Karanta Ishaya 48:17) Saboda haka Musa ya gaya wa Isra’ila ta dā: ‘Ubangiji kuma ya umurce mu mu yi dukan waɗannan farillai, mu ji tsoron Ubangiji Allahnmu, domin anfanin kanmu kullum, domin shi wanzadda mu kamar rana ta yau.’ (Kubawar Shari’a 6:24) Mu ma za mu iya tabbata cewa domin dokokinsa da ya ba mu, Jehobah yana so mu amfana dindindin. Hakika, ba zai yi abin da zai cutar da mu ba. Jehobah Allah ne mai hikima marar iyaka. (Romawa 11:33) Saboda haka, ya san abin da ya fi kyau a gare mu. Jehobah kuma shi ne tushen ƙauna. (1 Yohanna 4:8) Ƙauna, wadda ita ce yanayinsa, tana rinjayar dukan abin da yake yi. Itace tushen dukan dokokin da ya ba bayinsa.
16. Duk da rinjaya na wannan malalaciyar duniya da kuma ta ajizancinmu, me ya sa za mu iya bin tafarkin biyayya?
16 Wannan ba ya nufin cewa yi wa Allah biyayya yana da sauƙi. Dole ne mu yaƙi rinjaya ta wannan malalaciyar duniya, wadda take “kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Dole ne kuma mu yi jayayya da ajizancinmu, wanda yake tura mu ga ƙeta dokokin Allah. (Romawa 7:21-25) Amma ƙaunarmu ga Allah za ta yi nasara. Jehobah yana yi wa waɗanda suke son su nuna ƙaunarsu a gare shi ta wajen biyayyarsu albarka. Yana ba da ruhunsa mai tsarki “ga waɗanda su ke biyayya gareshi.” (Ayukan Manzanni 5:32) Ruhun yana ba da ɗiya mai kyau a gare mu, wato, halaye masu kyau da za su taimake mu mu bi tafarkin biyayya.—Galatiyawa 5:22, 23.
17, 18. (a) Menene za mu bincika a cikin wannan littafin, kuma sa’ilin da muke haka, me ya kamata mu tuna da shi? (b) Menene za a tattauna a babi na gaba?
17 A wannan littafin, za mu bincika mizanan Jehobah da ɗabi’ar da ya kafa da kuma wasu abubuwa da za su nuna mana nufinsa. Sa’ad da muka ci gaba, muna bukatar mu tuna da abubuwa da yawa. Bari mu tuna cewa Jehobah ba ya tilasta mana mu kiyaye dokokinsa da mizanansa; yana bukatar biyayya da ta fito daga zuciyarmu. Kada kuma mu manta cewa Jehobah yana so ne mu rayu a hanyar da za ta kawo albarka mai yawa a yanzu da kuma rai madawwami a nan gaba. Kuma mu tuna cewa biyayyarmu da zuciya ɗaya, zarafi ne na nuna wa Jehobah cewa muna ƙaunarsa sosai.
18 Domin ya taimake mu mu fahimci abin da ke mai kyau da marar kyau, Jehobah cikin ƙaunarsa ya ba mu lamiri. Duk da haka, domin ja-gorarsa ya kasance abin dogara, muna bukatar mu koyar da lamirinmu, kamar yadda babi na gaba zai nuna.
^ sakin layi na 9 Ka dubi Babi na 6 na wannan littafin domin bayani game da yadda za ka zaɓi wasanni masu kyau.
^ sakin layi na 11 Har miyagun ruhohi ma suna biyayya da rashin son rai. Sa’ad da Yesu ya umurci aljannu su fita daga wasu mutanen da suka kama, an tilasta wa aljannun su fahimci ikonsa kuma sun yi biyayya, ko da yake ba sa son su yi haka.—Markus 1:27; 5:7-13.
^ sakin layi na 13 A Matta 23:4, an yi amfani da wannan kalmar wajen kwatanta “kaya masu-nauyi,” wato, yawan dokoki da kuma al’adun mutane da marubuta da Farisiyawa suka ɗaura a kan mutane. Wannan kalmar kuma an fassara ta “zafin hali” a Ayukan Manzanni 20:29, 30 kuma tana nuni ne ga ’yan ridda masu zafin hali waɗanda za su yi “karkatattun zantattuka” domin su yaudari mutane.