RATAYE
A Wane Lokaci Ne Ya Kamata a Rufe Kai, Kuma Me Ya Sa?
A wane lokaci ne ya kamata mace Kirista ta rufe kanta domin bauta, kuma me ya sa? Bari mu bincika bayanin da aka huri Manzo Bulus ya yi game da wannan batu. Ya ba da ja-gora da muke bukata domin mu yanke shawarar da ta dace, wadda za ta faranta wa Allah rai. (1 Korintiyawa 11:3-16) Bulus ya nuna abubuwa uku da za a kula da su: (1) ayyuka da za su bukaci mace ta rufe kanta, (2) yanayi da ya kamata mace ta rufe kanta, kuma na (3) dalilin da ya sa za ta yi amfani da wannan mizani.
Ayyuka. Bulus ya faɗi guda biyu: addu’a da annabci. (Ayoyi na 4, 5) Addu’a, babu shakka magana ce da Allah cikin bauta. A yau, annabci ya shafi dukan wani koyarwa na Littafi Mai Tsarki da Kiristoci masu hidima suke yi. Manzo Bulus yana cewa ne, ya kamata mace ta rufe kanta a dukan lokacin da take addu’a ko kuma take koyar da gaskiya ta Littafi Mai Tsarki? A’a. Yanayin da mace take addu’a
ko kuma take koyarwa zai nuna ko tana bukatar ta rufe kanta.Yanayi. Kalmomin Bulus sun yi magana ne a kan yanayi guda biyu, iyali da kuma ikilisiya. Ya ce: “Kan mace . . . namiji ne; . . . kowace mace da ta ke yin addu’a ko wa’azi, kanta ba luluɓi, tana yi ma kanta ƙanƙanci.” (Ayoyi na 3, 5) A tsarin iyali, namiji ne Jehobah ya bai wa ikon shugabanci. Idan ba ta nuna ta fahimci ikon mijinta ba, za ta ƙasƙantar da mijinta idan ta ɗauki hakkin da Jehobah ya ba shi. Alal misali, idan ya kasance za ta gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a gaban mijinta, za ta nuna ta fahimci ikonsa kuma ta rufe kanta. Za ta yi haka ko ya yi baftisma ko bai yi ba, tun da shi ne shugaban iyali. * Idan za ta yi addu’a ko za ta koyar a gaban ɗanta ƙarami da ya yi baftisma, za ta rufe kanta, ba domin shi ne shugaban iyali ba, amma domin iko da aka bai wa maza da suka yi baftisma cikin ikilisiya.
Bulus ya yi magana game da tsarin ikilisiya, ya ce: “Amma idan kowane mutum yana bayana halin gardama, ba mu da wannan irin alada ba, ko mu ko ekklesiyai na Allah.” (Aya ta 16) A cikin ikilisiyar Kirista ana bai wa maza da suka yi baftisma shugabanci. (1 Timothawus 2:11-14; Ibraniyawa 13:17) Maza ne kawai ake naɗawa dattawa ko kuma bayi masu hidima don hakkin da Allah ya ba su na kula da tumakinsa. (Ayukan Manzanni 20:28) A wasu lokatai, yanayi yana iya sa mace Kirista ta yi aikin da namiji Kirista da ya yi baftisma ne ya kamata ya yi. Alal misali, wataƙila tana bukatar ta gudanar da taron fita hidima domin babu namiji da ya ƙware da ya yi baftisma a wajen. Ko kuma ta gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a gaban namiji da ya yi baftisma. Domin waɗannan ayyukan sun shafi ikilisiyar Kirista, za ta rufe kanta ta nuna tana yin aikin da ainihi aikin maza ne.
Bugu da ƙari, a wasu wurare kuma na bauta ’yan’uwa mata ba sa bukatar su rufe kansu. Alal misali, ba ta bukatar ta rufe kanta sa’ad da take kalami a lokacin taro, sa’ad da take wa’azi gida gida tare da mijinta ko kuma wani ɗan’uwa da ya yi baftisma, ko kuma sa’ad da take nazari ko addu’a da ’ya’yanta maza da ba su yi baftisma ba. Hakika, wasu tambayoyi za su iya tasowa, idan ’yar’uwa ba ta da tabbaci game da wani batu, ta yi bincike. * Idan duk da haka ba ta tabbata ba, kuma lamirinta ya motsa ta ta rufe kanta, yin haka babu laifi, kamar yadda aka nuna a wannan hotun.
Dalili. A aya ta 10, mun ga dalilai biyu da suka sa mace Kirista za ta so ta cika wannan hakki: “Ya kamata mace ta kasance da shaidar hukumci bisa kanta, saboda mala’iku.” Na farko, ka lura da furcin nan, “shaidar hukumci.” Rufe kai hanya ce da mace za ta nuna cewa ta yarda da ikon da Jehobah ya bai wa maza a cikin ikilisiya. Saboda haka, tana nuna ƙaunarta da amincinta ga Jehobah Allah. An same dalili na biyu a cikin kalmomin nan, kuma “saboda da mala’iku.” Ta yaya mace take shafan waɗannan halittu masu ƙarfi ta wajen rufe kanta?
Mala’iku suna so su ga cewa an bi ikon Allah a dukan tsarin ƙungiyarsa, a sama da kuma a duniya. Su ma suna amfana da misalin ’yan adam ajizai a wannan batun. Dole ne su miƙa kai ga tsarin Jehobah, domin wasu a cikinsu Yahuda 6) Mala’iku za su ga lokatai da mace Kirista da take da fahimi, da ilimi da basira fiye da namijin da ya yi baftisma a ikilisiya; amma duk da haka, tana miƙa kai ga ikonsa. A wasu yanayi, macen, Kirista ce shafaffiya, wadda za ta yi sarauta tare da Kristi. Irin wannan macen za ta yi hidima daga baya a matsayi da ma ya fi na mala’iku kuma ta yi sarauta tare da Kristi a sama. Misali ne mai kyau ga mala’iku! Hakika, gata ce mai girma ’yan’uwa mata suke da ita na nuna biyayya ta wajen amincinsu da kuma halinsu na miƙa kai a gaban miliyoyin mala’iku!
sun kasa yin hakan a dā. (^ sakin layi na 1 Mace Kirista ba za ta ɗaga murya ta yi addu’a ba a gaban mijinta idan mai bi ne sai dai a wasu yanayi, kamar idan wani ciwo ya sa ya zama bebe.
^ sakin layi na 1 Domin ƙarin bayani, don Allah dubi Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu, 2015, shafi na 30 da ta 15 ga Yuli, 2002, shafuffuka na 26-27, da kuma 15 ga Fabrairu, 1977, shafuffuka na 125-128.