Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 16

Ka Yi Tsayayya da Shaidan da Kissoshinsa

Ka Yi Tsayayya da Shaidan da Kissoshinsa

“Ku yi tsayayya da Shaiɗan.”—YAƘUB 4:7.

1, 2. Su wanene ke farin ciki a lokacin baftisma?

IDAN ka riga ka soma bauta wa Jehobah tun da daɗewa, wataƙila ka ji jawabai masu yawa na baftisma a taronmu ƙanana da manya. Duk da haka, ko da sau nawa ne ka taɓa shaida irin wannan lokacin, a duk lokacin da ka ga waɗanda suke zaune a kujerun gaba suka tashi su gabatar da kansu don baftisma, hakan na taɓa zuciyarka sosai. A daidai wannan lokacin, dukan masu sauraro suna cika da farin ciki, kuma ko’ina na cika da tafi. Idanunka na iya cika da hawaye yayin da kake kallon wasu rukunin mutanen da suka zaɓi su bi Jehobah. Wannan lokacin na sa mu farin ciki!

2 Wataƙila a inda muke da zama, ba ma yawan shaida baftisma sosai a shekara, amma mala’iku suna da gatan ganin baftisma sosai fiye da mu. Za ka iya tunanin irin ‘murnar’ da ake yi a cikin sama, sa’ad da suka ga dubban mutane a dukan duniya da suke shiga sashen ƙungiyar Jehobah da ke duniya a kowane mako? (Luka 15:7, 10) Babu shakka, mala’iku suna farin cikin ganin wannan ƙaruwar!—Haggai 2:7.

IBLIS “KAMAR ZAKI MAI-RURI, YANA YAWO”

3. Me ya sa Shaiɗan yake yawo “kamar zaki mai-ruri,” kuma me yake son ya yi?

3 Amma fa, akwai wasu halittun ruhu da ke kallon baftisma da fushi. Ga Shaiɗan da aljanu, suna mugun jin haushin ganin dubbai da ke juya wa wannan lalatacciyar duniyar baya. Dole ne Shaiɗan ya yi fushi, domin ya riga ya yi kuri cewa babu mutumin da ke bauta wa Jehobah cikin ƙauna ta gaskiya kuma babu wanda zai kasance da aminci a lokacin gwaji mai tsanani. (Karanta Ayuba 2:4, 5.) A duk lokacin da mutum ya yanke shawarar keɓe kansa ga Jehobah, hakan na nuna cewa Shaiɗan maƙaryaci ne. Kamar dai Shaiɗan yana shan mari marar iyaka ne a kowane mako a shekara. Babu shakka, shi ya sa “kamar zaki mai-ruri, yana yawo, yana neman wanda za ya cinye.” (1 Bitrus 5:8) Wannan ‘zakin’ yana ɗokin cinye mu a ruhaniyance, don mu ɓata dangantakarmu da Allah.—Zabura 7:1, 2; 2 Timothawus 3:12.

A duk lokacin da mutum ya keɓe rayuwarsa ga Jehobah kuma ya yi baftisma, yana mai da Shaiɗan maƙaryaci

4, 5. (a) Ta waɗanne hanyoyi biyu ne Jehobah ya ƙayyade tasirin Shaiɗan? (b) Wane tabbaci ne Kirista na gaskiya yake da shi?

4 Ko da yake muna fuskantar mugun maƙiyi, ba mu da wani dalilin jin tsoro. Me ya sa? Domin Jehobah ya rage ƙarfin wannan “zaki mai-ruri” a hanyoyi masu muhimmanci guda biyu. Waɗanne ke nan? Na farko, Jehobah ya annabta cewa “taro mai-girma” na Kiristoci na gaskiya za su tsira daga “babban tsanani” mai zuwa. (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14) Annabce-annabcen Jehobah ba sa kasawa! Saboda haka, ko Shaiɗan da kansa ya san cewa ba zai iya kama mutanen Allah gabaki ɗaya ba.

5 Za mu iya samun dalili na biyu a cikin wata gaskiyar da ɗaya daga cikin bayin Allah na dā ya faɗa. Annabi Azariah ya gaya wa Sarki Asa: “Ubangiji yana tare da ku, muddar kuna tare da shi.” (2 Labarbaru 15:2; karanta 1 Korintiyawa 10:13) Misalai masu yawa da aka rubuta sun nuna cewa a dā, Shaiɗan ya kasa cinye dukan bayin Allah da suka kusaci Allah. (Ibraniyawa 11:4-40) A yau, duk Kirista da ya kusaci Allah zai iya yin tsayayya da Iblis kuma ya yi nasara a kansa. Hakika, Kalmar Allah ta ba mu tabbaci: “Ku yi tsayayya da Shaiɗan, za ya fa guje muku.”—Yaƙub 4:7.

MUNA “KOKUWA . . . DA RUNDUNAI MASU-RUHANIYA NA MUGUNTA”

6. Ta yaya ne Shaiɗan yake yaƙi da Kiristoci ɗaɗɗaya?

6 Shaiɗan ba zai iya yin nasara a wannan yaƙin na alama ba, amma yana iya cinye mu ɗaɗɗaya idan muka yi sakaci. Shaiɗan ya san cewa zai iya cinye mu idan ya raunana abotarmu da Jehobah. Ta yaya Shaiɗan yake ƙoƙarin cim ma hakan? Ta wajen kai wa kowannenmu mugun hari, kuma cikin dabara. Bari mu tattauna waɗannan kissoshi na Shaiɗan.

7. Me ya sa Shaiɗan yake kai wa mutanen Jehobah mugun hari?

7 Mugun hari. Manzo Yohanna ya ce: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Waɗannan kalmomin sun ƙunshi gargaɗi ga dukan Kiristoci na gaskiya. Tun da yake Shaiɗan ya riga ya cinye dukan mugayen mutanen da ke wannan duniyar, ya mai da hankalinsa ne ga waɗanda a yanzu sun riga sun tsira daga hannunsa, wato, mutanen Jehobah, kuma yana kai musu mugun hari. (Mikah 4:1; Yohanna 15:19; Ru’ya ta Yohanna 12:12, 17) Yana mugun fushi domin ya san cewa ba shi da isashen lokaci. Hakan ya sa ya ƙara yawan matsin. A yau, muna fuskantar mugun ƙoƙarin da yake yi na ɓata dangantakarmu da Allah. Saboda haka, fiye da kowane lokaci, muna bukatar mu “gane zamani [mu] san abin da ya kamata [mu] yi.”—1 Labarbaru 12:32.

8. Menene manzo Bulus yake nufi sa’ad da ya ce muna “kokuwa” da mugayen ruhohi?

8 Yin kokuwa da kanmu. Manzo Bulus ya gargaɗi ’yan’uwa Kiristoci: “Kokuwarmu . . . da rundunai masu-ruhaniya na mugunta cikin sammai [ne].” (Afisawa 6:12) Me ya sa Bulus ya yi amfani da kalmar nan “kokuwa”? Domin hakan na nufin yin amfani da hannu da ƙarfi da kuma haɗa jiki. Da haka, ta wajen yin amfani da kalmar nan, Bulus ya nanata cewa kowannenmu yana da kokawar da zai yi da mugayen ruhohi. Ko da muna zaune ne a ƙasar da aka gaskata da mugayen ruhohi ko a’a, kada mu taɓa manta cewa sa’ad da muka keɓe kanmu ga Jehobah, mun shiga filin kokuwa ne a alamance. Tun lokacin da muka keɓe kanmu, kowanne Kirista ya shiga filin kokuwa. Hakan ya sa Bulus ya ga muhimmancin ariritar Kiristocin da ke Afisa sau uku su “tsaya fa.”—Afisawa 6:11, 13, 14.

9. (a) Me ya sa Shaiɗan da aljanu suke amfani da “dabaru”? (b) Me ya sa Shaiɗan yake ƙoƙarin ɓata tunaninmu, kuma ta yaya za mu iya yin tsayayya da ƙoƙarce-ƙoƙarcensa? (Duba akwatin nan da ke  shafi na 192-193.) (c) Wace dabara ce za mu tattauna yanzu?

9 Mugun dabaru. Bulus ya aririci Kiristoci su yi tsayin daka da “dabarun Shaiɗan.” (Afisawa 6:11) Idan ka lura za ka ga cewa Bulus ya yi amfani ne da jam’i. Mugayen ruhohi suna amfani ne da hanyoyin dabaru masu yawa, kuma suna hakan ne da ƙwaƙƙwaran dalili. A kwana a tashi, wasu masu bi da suka yi tsayayya da wani gwaji, suna iya faɗuwa sa’ad da suka fuskanci wani irin gwajin dabam. Saboda haka, Iblis da aljanu sun mai da hankalinsu a kan kowannenmu don su ga kasawarmu. Bayan haka, suna iya amfani da kasawa ta ruhaniya da muke da ita. Abin farin ciki shi ne, za mu iya sanin yawancin hanyoyin Iblis, domin Littafi Mai Tsarki ya bayyana mana su. (2 Korintiyawa 2:11) A farkon wannan littafin, mun tattauna irin waɗannan dabarun kamar su neman abin duniya, mugun tarayya, da kuma lalata. Bari yanzu mu tattauna wata dabarar da Shaiɗan yake amfani da ita, wato, sihiri.

YIN SIHIRI HANYA CE TA YAUDARA

10. (a) Menene sihiri? (b) Yaya Jehobah yake ɗaukan sihiri, kuma yaya kake ɗaukan shi?

10 Ta wajen yin sihiri, mutum yana saduwa ne kai tsaye da mugayen ruhohi. Duba, maita, sammu, da kuma tuntuɓar matattu suna cikin sihiri. Kamar yadda muka sani, Jehobah yana ɗaukan sihiri a matsayin “abin ƙyama.” (Kubawar Shari’a 18:10-12; Ru’ya ta Yohanna 21:8) Tun da yake dole ne mu “yi ƙyamar abin da ke mugu,” wauta ce mu yi tarayya da mugayen ruhohi. (Romawa 12:9) Kuma yin hakan na nufin cewa mun yaudari Jehobah, Ubanmu na samaniya!

11. Me ya sa Shaiɗan zai yi nasara sosai idan ya ruɗe mu mu saka hannu cikin sihiri? Ka kwatanta.

11 Domin ya san cewa saka hannu a sihiri muguwar yaudara ce ga Jehobah, Shaiɗan ya ƙuduri aniyar sa wasunmu a ciki. A duk lokacin da ya ruɗi Kirista ya saka hannu a sihiri, Shaiɗan ya yi nasara sosai. Me ya sa? Yi la’akari da wannan kwatancin: Idan aka rinjayi soja ya yi watsi da ’yan’uwansa sojoji kuma ya yaudare su sa’an nan ya je ya shiga cikin rundunar maƙiya, shugaban maƙiyan zai yi farin ciki sosai. Yana ma iya nuna wannan maci amana a matsayin ganimar yaƙi, don ya ba shugabansa na dā haushi. Hakazalika, idan Kirista ya saka hannu a cikin sihiri, da sane kuma da son rai zai yi watsi da Jehobah kuma ya koma ƙarƙashin ikon Shaiɗan. Ka yi tunanin irin farin cikin da Shaiɗan zai yi sa’ad da yake nuna wannan maci amana a matsayin ganimar yaƙi! Akwai wani a cikinmu da zai so Iblis ya yi irin wannan nasarar? Ko kaɗan! Mu ba maci amana ba ne.

YIN AMFANI DA TAMBAYOYI DON JAWO SHAKKA

12. Wace dabara ce Shaiɗan yake amfani da ita don rinjayar ra’ayinmu game da sihiri?

12 Idan muka ci gaba da ƙin sihiri, Shaiɗan ba zai yi nasara a kanmu ba idan ya yi amfani da shi. Saboda haka, ya fahimci cewa dole ne ya canja tunaninmu. Ta yaya? Ya nemi hanyoyi don ya ruɗar da Kiristoci har wasu su yarda cewa “mugunta nagarta [ce]; nagarta kuma mugunta . . . ce.” (Ishaya 5:20) Don ya cim ma hakan, Shaiɗan ya koma ga yin amfani da wata tsohuwar dabararsa, yana ta da tambayoyi da suke jawo shakka.

13. Ta yaya ne Shaiɗan ya yi amfani da dabarar ta da tambayoyi don ya jawo shakka?

13 Ka yi la’akari da yadda Shaiɗan ya yi amfani da dabara a dā. A Adnin ya tambayi Hauwa’u: ‘Ashe, ko Allah ya ce, ba za ku ci daga dukan itatuwa na gona ba?’ A lokacin Ayuba, sa’ad da mala’iku suke taro a sama, Shaiɗan ya ta da wannan tambayar: ‘A banza ne Ayuba ya ke tsoron Allah?’ Kuma a farkon hidimar Yesu a duniya, Shaiɗan ya ƙalubalanci Kristi ta wajen cewa: ‘Idan kai Ɗan Allah ne, ka umurci waɗannan duwatsu su zama gurasa.’ A nan, Shaiɗan yana kwaikwayon ainihin kalmomin da Jehobah da kansa ya faɗa makonni shida da suka wuce kafin wannan aukuwar: ‘Wannan Ɗana ne, ƙaunatacena, wanda raina ya ji daɗinsa sarai.’—Farawa 3:1; Ayuba 1:9; Matta 3:17; 4:3.

14. (a) Ta yaya ne Shaiɗan yake amfani da dabararsa wajen sa shakka game da sihiri? (b) Menene za mu tattauna a yanzu?

14 A yau, Iblis yana amfani da irin wannan dabarar don mutane su yi shakkar muguntar da ke tattare da sihiri. Abin baƙin ciki, ya yi nasara wajen saka shakka cikin zukatan wasu masu bi. Sun soma yin shakka ko wasu irin sihiri ba su da kyau. Da haka, suna tunani, ‘Ko haka ne?’ (2 Korintiyawa 11:3) Ta yaya za mu iya taimaka wa irin waɗannan su daidaita tunaninsu? Ta yaya za mu tabbata cewa dabarar Shaiɗan ba ta yi tasiri a kanmu ba? Don mu amsa, bari mu tattauna hanyoyin rayuwa guda biyu da Shaiɗan cikin dabarunsa ya ɓata da sihiri. Su ne nishaɗi da kula da lafiyar jiki.

YIN AMFANI DA SHA’AWARMU DA BUKATUNMU

15. (a) Yaya ne yawancin mutane da ke Yammacin duniya suke ɗaukan sihiri? (b) Ta yaya ne ra’ayin duniya game da sihiri ya shafi wasu Kiristoci?

15 Musamman a ƙasashen da ke Yammacin duniya, mutane da yawa suna ɗaukan rukunin asiri, maita, da sauran fasalolin sihiri abu mai kyau. Wasannin bidiyo, littattafai, tsarin wasannin TV, da kuma wasan kwamfuta suna ci gaba da gabatar da ayyukan aljanu a matsayin abin wasa, wayo, kuma marar lahani. Wasu wasannin bidiyo da littattafai da suke nuna rukunin asiri sun zama sanannu sosai har waɗanda suke son wasannin suka kafa rukunonin magoya baya. Babu shakka, aljanu sun yi nasara wajen ƙasƙantar da haɗarurrukan da ke tattare da ƙungiyar asiri. Irin wannan ra’ayin game da sihiri ya shafi Kiristoci kuwa? Ƙwarai kuwa! Ya shafi tunanin wasu. Ta wace hanya? Ga misali, bayan wani Kirista ya kalli bidiyon da ke nuna ƙungiyar asiri, ya ce, “Na kalli bidiyon ne kawai, amma ban saka hannu a sihiri ba.” Me ya sa irin wannan tunanin yake da haɗari?

16. Me ya sa zaɓan nishaɗin da ke nuna ƙungiyar asiri yake da haɗari?

16 Ko da yake akwai bambancin saka hannu a sihiri da kuma kallonsa, amma hakan ba ya nufin cewa kallon ayyukan ƙungiyar asiri ba shi da haɗari. Me ya sa? Yi la’akari da wannan: Kalmar Allah ta nuna cewa Shaiɗan da aljanunsa ba za su iya karanta zuciyarmu ba. * Da haka, kamar yadda aka ambata a baya, don su san abin da muke tunani da duk wata kasawar da muke da ita a ruhaniya, mugayen ruhohi suna bukatar su kalli ayyukanmu sosai, har da irin nishaɗin da muke yi. Sa’ad da halin Kirista ya nuna cewa yana jin daɗin wasannin bidiyo ko littattafan da suke gabatar da duba, dabo, da kuma wasannin da aljanu suke shiga jikin mutum, ko kuwa batutuwan da suka shafi aljanu, to, yana aika saƙo ga aljanu ke nan. Da haka, yana nuna musu kasawarsa! A sakamakon haka, aljanun za su iya tsananta kokawar da suke yi da wannan Kirista ta wajen yin amfani da kasawar da ya nuna musu har sai sun kada shi. Hakika, wasu da suka soma marmarin sihiri sun yi hakan ne ta wajen kallon wasannin da ke gabatar da ƙungiyar asiri, kuma daga baya suka tsoma hannunsu cikin sihiri.—Karanta Galatiyawa 6:7.

Ka amfana daga taimakon Jehobah a lokacin rashin lafiya

17. Wace dabara ce Shaiɗan zai iya yin amfani da ita don ya cinye marar lafiya?

17 Shaiɗan yana ƙoƙarin ya yi amfani da nishaɗin da muke sha’awa da kuma neman lafiya da muke yi. Ta yaya? Kirista da lafiyarsa ta ci gaba da taɓarɓarewa duk da ƙoƙarce-ƙoƙarcen da yake yi na neman lafiya zai iya soma baƙin ciki. (Markus 5:25, 26) Shaiɗan da aljanunsa suna iya yin amfani da wannan daman. Sun san cewa Kalmar Allah ta yi gargaɗi a kan neman “taimakon masu-aika saɓo.” (Ishaya 31:2) Don su sa Kirista ya ƙi bin wannan gargaɗin, aljanu suna iya jarraba marar lafiya ya soma neman magani ko kuma ya bi wasu hanyoyin da suka ƙunshi yin amfani da “tsafi,” ko sihiri, abin da zai iya jawo mugun lahani. (Ishaya 1:13, NW) Idan waɗannan aljanun suka yi nasara ta wajen yin amfani da wannan dabarar, hakan zai iya shafan dangantakar marar lafiyar da Allah. Ta wace hanya?

18. Waɗanne abubuwa ne Kirista zai guje wa, kuma me ya sa?

18 Jehobah ya gargaɗi Isra’ilawan da suka juya ga yin “mugunta”: “Sa’anda ku ke buɗen hannuwanku, zan ɓoye maku idanuna: i, sa’anda ku ke yi mani yawan addu’oi, ba ni ji ba.” (Ishaya 1:15) Hakika, muna son mu guji duk wani abin da zai hana Jehobah jin addu’o’inmu da kuma samun taimakonsa, musamman a lokacin rashin lafiya. (Zabura 41:3) Saboda haka, idan akwai alamun cewa wasu hanyoyin binciko rashin lafiya ko magance rashin lafiya da rauni sun ƙunshi sihiri, dole ne Kirista na gaskiya ya guje su. * (Matta 6:13) Da haka, Jehobah zai ci gaba da tallafa masa.—Duba akwatin nan “ Wannan Sihiri ne Kuwa?” a shafi na 194.

SA’AD DA LABARAI GAME DA ALJANU SUKA YI YAWA

19. (a) Menene Iblis ya yaudari mutane da yawa su gaskata game da ikonsa? (b) Waɗanne labarai ne Kiristoci na gaskiya za su guje wa?

19 Yayin da mutane da yawa da suke zaune a Yammacin duniya ba sa damuwa da haɗarin da ke tattare da ikon Shaiɗan, akasin hakan ne ke faruwa a sauran ɓangarorin duniya. A waɗannan wuraren, Iblis ya ruɗi mutane masu yawa su gaskata cewa yana da iko sosai. Wasu mutane suna harkokinsu na dukan rayuwa cike da tsoron mugayen ruhohi. Labarai game da manyan ayyukan aljanu sun cika ko’ina. A yawancin lokaci ana ba da irin waɗannan labaran ne cike da annashuwa, kuma mutane suna jin daɗinsu. Ya kamata mu ma mu saka hannu wajen yaɗa irin waɗannan labaran? A’a, bayin Allah na gaskiya suna guje wa yin hakan domin dalilai biyu masu muhimmanci.

20. Ta yaya mutum ba tare da sani ba, zai yaɗa ƙarairayin Shaiɗan?

20 Na farko, ta wajen yaɗa labarai game da abubuwan da aljanu suka cim ma, muna gabatar da abubuwan da Shaiɗan yake so. Kamar yaya? Kalmar Allah ta ce Shaiɗan zai iya yin manyan ayyuka, amma ta gargaɗe mu cewa yana yin amfani da “al’ajabai na ƙarya” da ‘ruɗani.’ (2 Tassalunikawa 2:9, 10) Tun da yake Shaiɗan ne shugaban mayaudara, ya san yadda zai rinjayi zuciyar waɗanda suke son sihiri ya kuma sa su gaskata abubuwan da ba gaskiya ba ce. Irin waɗannan mutanen suna iya gaskata cewa sun ga kuma sun ji wasu abubuwa, kuma suna iya gaya wa mutane cewa abubuwan da suka shaida gaskiya ce. Da sannu sannu, za a ci gaba da ƙara wa labarin gishiri ta wajen sake faɗinsu. Idan Kirista ya yaɗa irin waɗannan labaran, yana yin nufin Iblis ke nan, “uban ƙarya.” Kuma zai ci gaba da yaɗa ƙarairayin Shaiɗan.—Yohanna 8:44; 2 Timothawus 2:16.

21. A kan menene ya kamata hirarmu ta kasance?

21 Na biyu, ko da Kirista ya haɗu da mugayen ruhohi a dā, zai guji tattauna irin waɗannan labaran da ’yan’uwa masu bi. Me ya sa? An aririce mu: “[Mu] zuba ido ga Yesu shugaban bangaskiyarmu da mai-cikanta.” (Ibraniyawa 12:2) Hakika, muna bukatar mu mai da hankalinmu ga Kristi, ba Shaiɗan ba. Ya kamata mu tuna cewa sa’ad da yake duniya, Yesu bai zaunar da mabiyansa ya cika su da tatsuniyar mugayen ruhohi ba, ko da yake ya gaya musu abin da Shaiɗan zai iya yi da wanda ba zai iya ba. Maimakon haka, Yesu ya mai da hankali ne a kan saƙon Mulki. Saboda haka, ta yin koyi da Yesu da manzanninsa, muna son hirarmu ta kasance a kan “ayyuka masu-girma na Allah.”—Ayukan Manzanni 2:11; Luka 8:1; Romawa 1:11, 12.

22. Menene za mu yi da zai sa a ci gaba da yin “murna cikin sama”?

22 Hakika, Shaiɗan yana amfani da dabaru masu yawa, har da sihiri, don ya ɓata dangantakarmu da Jehobah. Amma, idan muka guji mugun abu kuma muka manne wa abin da ke da kyau, ba za mu ba Iblis dama ya raunana ƙudurin da muka yi na guje wa kowane irin sihiri ba. (Karanta Afisawa 4:27) Ka yi tunanin irin ‘murna da za a yi cikin sama’ idan muka ci gaba da yin “tsayayya da dabarun Shaiɗan” har lokacin da aka halaka shi.—Afisawa 6:11.

^ sakin layi na 16 Sunayen kwatanci da aka ba Shaiɗan (Ɗan hamayya, Mai tsegumi, Mai ruɗi, Mai gwaji, Maƙaryaci) ba sa nufin cewa zai iya sanin abubuwan da ke zukatanmu. Akasin haka, an kira Jehobah mai “auna zukata,” kuma Yesu, wanda ke “bimbinin ciki da zukata.”—Misalai 17:3; Ru’ya ta Yohanna 2:23.

^ sakin layi na 18 Don ƙarin bayani, ka duba talifin nan “A Health Test for You?” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Disamba, 1994, shafi na 19-22 a Turanci, da kuma talifin nan “The Bible’s Viewpoint: Your Choice of Medical Treatment—Does It Matter?” da ke Awake! fitowar 8 ga Janairu, 2001.