ALMAJIRTARWA
DARASI NA 12
Ka Gaya Masa Gaskiya
Ƙaꞌida: “Turare da man ƙanshi sukan farantar da rai, amma farin cikin abokantaka daga shawara mai kyau ne.”—K. Mag. 27:9.
Abin da Yesu Ya Yi
1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Markus 10:17-22. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:
Mene ne Abin da Yesu Ya Yi Ya Koya Mana?
2. Ya kamata mu nuna wa ɗalibanmu ƙauna, amma mu riƙa gaya musu gaskiya idan muna so su sami ci gaba.
Ka Yi Koyi da Yesu
3. Ka taimaki ɗalibinka ya kafa maƙasudi kuma ya cika su.
-
Ka yi amfani da sashen “Maƙasudi” da ke kowane darasi a littafin Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!
-
Ka taimaki ɗalibin ya san abin da zai yi don ya iya cika ƙananan maƙasudansa da kuma manyan.
4. Ka san abubuwan da ke hana ɗalibin samun ci gaba kuma ka taimaka masa ya magance su.
-
-
‘Idan ɗalibina ba ya yin abubuwan da za su sa ya cancanci yin baftisma, mene ne yake hana shi?’
-
‘Me zan iya yi don in taimaka masa?’
-
-
Ka yi adduꞌa don ka sami ƙarfin gaya wa ɗalibin abin da yake bukatar ya yi, kuma ka yi hakan cikin ƙauna.
5. Idan ɗalibin ba ya samun ci gaba, ka daina nazari da shi.
-
Don ka san ko ɗalibin yana samun ci gaba, ka tambayi kanka cewa:
-
‘Ɗalibina yana bin abin da yake koya?’
-
‘Yana zuwa taro kuma yana gaya ma wasu abubuwan da yake koya?’
-
‘Idan kun daɗe kuna nazari, shin yana so ya zama Mashaidin Jehobah kuwa?’
-
-
Idan ka ga cewa ɗalibin ba ya so ya samu ci gaba:
-
Ka ce masa ya yi tunani a kan abin da yake hana shi.
-
Cikin ƙauna, ka bayyana masa abin da ya sa za ka daina nazari da shi.
-
Ka gaya masa abin da yake bukatar ya yi idan yana so ku ci gaba da nazarin wata rana.
-
KA KUMA KARANTA
Zab. 141:5; K. Mag. 25:12; 27:6; 1 Kor. 9:26; Kol. 4:5, 6