FARA MAGANA DA MUTANE
DARASI NA 2
Ka Yi Kamar Kuna Hira
Ƙaꞌida: “Abu mai kyau ne magana ta fita a daidai lokaci.”—K. Mag. 15:23.
Abin da Filibus Ya Yi
1. Ka kalli BIDIYON, ko ka karanta Ayyukan Manzanni 8:30, 31. Saꞌan nan ka yi tunani a kan tambayoyin nan:
Mene ne Abin da Filibus Ya Yi Ya Koya Mana?
2. Idan muka yi magana da mutum kamar muna hira, hakan zai sa shi ma ya saki jiki kuma ya so ya saurare mu.
Ka Yi Koyi da Filibus
3. Ka riƙa lura. Za ka iya gane abubuwa game da mutum idan ka lura da yadda yake yi da kuma yanayin fuskarsa. Shin mutumin yana a shirye ya saurare ka? Idan yana a shirye, za ka iya soma tattauna wani abu a Littafi Mai Tsarki da shi ta wajen yi masa tambayar nan, “Ka san cewa . . . ?” Idan mutum ba ya so ya tattauna da kai, kada ka sa shi dole.
4. Ka zama mai haƙuri. Ba dole ba ne ka soma magana game da Littafi Mai Tsarki nan da nan. Ka jira har sai ka sami lokacin da ya dace don ka yi hakan. A wasu lokuta, kana bukatar ka jira har sai ka sake haɗuwa da mutumin kafin ka iya tattauna game da Littafi Mai Tsarki.
5. Ka kasance a shirye don ka iya canja batun da kake so ka tattauna. Wanda kake tattaunawa da shi zai iya soma tattauna wani abu dabam. Don haka, ka kasance a shirye don ka iya gaya wa mutumin wani abu a cikin Littafi Mai Tsarki da zai so ya ji, ko da hakan ya yi dabam da abin da kake so ka tattauna.
KA KUMA KARANTA
M. Wa. 3:1, 7; 1 Kor. 9:22; 2 Kor. 2:17; Kol. 4:6