ƘARIN BAYANI NA 2
Zai Dace Ka Daina Tattaunawar?
Idan wani ya yi mana tambaya kuma da gaske yana so ya san amsar, muna jin daɗin yi masa bayani. Muna son tattaunawa da masu “zuciya ta samun rai na har abada.”—A. M. 13:48, New World Translation.
Amma idan mutumin yana fushi, ko yana so ya yi gardama, ko kuma ba ya so ya yi magana da kai fa? Cikin basira, ka daina tattaunawar da shi. (K. Mag. 17:14) Ku rabu lafiya don ya yarda ya sake tattaunawa da mu a nan gaba.—1 Bit. 2:12.