Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 1

Wani Sirri da Muke Farin Cikin Sani

Wani Sirri da Muke Farin Cikin Sani

An taɓa gaya maka wani abu kai kaɗai amma ba a gaya ma kowa ba?— * Idan haka ne, abin da aka gaya maka asiri ne ko kuma sirri domin wasu mutane ba su sani ba. Littafi Mai Tsarki ya yi maganar wani babban ‘asiri’ daga wurin Allah. An kira shi sirri domin mutane ba su san shi ba. Mala’iku ma sun so su san wannan sirrin. Za ka so ka san wannan sirrin?—

Mene ne kake ganin mala’ikun nan suke so su sani?

Tun dā can, Allah ya halicci namiji da tamace na farko. Sunayensu Adamu da Hawwa’u. Allah ya saka su a wani wuri mai kyau da ake kira, lambun Adnin. Da a ce Adamu da Hawwa’u sun yi biyayya ga Allah, da su da ’ya’yansu sun mai da dukan duniya aljanna kamar wannan lambun. Ƙari ga haka, da sun rayu har abada a cikin wannan Aljannar. Amma ka tuna abin da Adamu da Hawwa’u suka yi?—

Adamu da Hawwa’u sun yi wa Allah rashin biyayya, shi ya sa ba ma cikin aljanna yanzu. Amma Allah ya ce zai mai da dukan duniya wuri mai kyau, inda mutane za su zauna har abada kuma su yi farin ciki. Yaya Allah zai yi hakan? Da daɗewa, mutane ba su sani ba, domin hakan sirri ne.

Sa’ad da Yesu ya zo duniya, ya koya wa mutane abubuwa da yawa game da wannan sirrin. Ya ce sirrin game da Mulkin Allah ne. Yesu ya gaya wa mutane su yi addu’a don wannan Mulkin ya zo. Mulkin zai mai da duniya aljanna.

Yaya kake ji yanzu da ka san wannan sirrin?— Ka tuna cewa waɗanda suke yi wa Jehobah biyayya ne kaɗai za su shiga Aljanna. Littafi Mai Tsarki ya gaya mana labarai da yawa game da maza da mata da suka yi wa Jehobah biyayya. Za ka so ka koya game da su?— Bari mu koya game da wasu daga cikinsu da kuma yadda za mu bi misalinsu.

KARANTA NASSOSIN NAN

  • Markus 4:11

  • 1 Bitrus 1:12

  • Farawa 1:26-28; 2:8, 9; 3:6, 23

  • Matta 6:9, 10

  • Zabura 37:11, 29

^ sakin layi na 3 A cikin kowane darasi, za ka ga wannan alamar (—) a bayan wasu tambayoyi. Hakan yana nuna cewa ya kamata ka dakata don yaronka ya ba da amsa.