Abin da Allah Ya Nufa Ke Nan?
KA KARANTA kowace jarida. Ka kalli telibijin ko kuma ka saurari rediyo. A cike suke da labarai na yin laifi, yaƙi, da ta’addanci. Ka yi tunanin naka matsalolin. Wataƙila ciwo ko kuma mutuwar wanda kake ƙauna yana tada maka hankali. Za ka ji kamar yadda mutumin arziki Ayuba ya ji, wanda ya ce “ina baƙin ciki ƙwarai.”—Ayuba 10:15.
Ka tambayi kanka:
-
Abin da Allah ya nufa mini da sauran ’yan Adam ke nan?
-
A ina zan sami taimako domin in jimre wa matsalolina?
-
Da begen za mu taɓa samun salama kuwa a duniya?
Littafi Mai Tsarki ya ba da amsoshi masu gamsarwa ga waɗannan tambayoyi.
GA ABIN DA ALLAH YA NUFA ZAI YI GA DUNIYA KAMAR YADDA LITTAFI MAI TSARKI YA KOYAR.
“Za ya share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin zuciya, ko kuka, ko azaba.”—Ru’ya ta Yohanna
“Gurgu za ya yi ta tsalle kamar barewa.”—Ishaya 35:5, 6.
“Za a buɗe idanun makafi.—Ishaya 35:5.
Yohanna 5:28, 29.
“Dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su . . .fito.”—“Ba wanda zai . . . ƙara yin kukan yana ciwo.”—Ishaya 33:24.
“Za a yi albarkar hatsi a ƙasa.”—Zabura 72:16.
KA AMFANA DAGA ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE KOYARWA
Kada ka yi tunanin abin da aka gabatar a shafuffuka na baya kamar kyakkyawan zato ne kawai. Allah ya yi alkawarin zai yi waɗannan abubuwa, kuma Littafi Mai Tsarki ya yi bayani game da yadda zai yi hakan.
Bugu da ƙari, Littafi Mai Tsarki zai taimake mu a hanyoyi masu yawa. Mabuɗi ne na hanyar samun rayuwa mai gamsarwa da gaske har a yanzu. Ka ɗan yi tunani game da damuwanka da kuma matsalolinka. Wataƙila sun haɗa da matsalar kuɗi, matsala ta iyali, rashin lafiya, ko kuma rasuwar wanda kake ƙauna. Littafi Mai Tsarki zai iya taimakonka ka magance matsalolinka a yau, kuma zai iya kwantar maka da hankali ta wajen amsa tambayoyi irin su:
-
Me ya sa muke wahala?
-
Ta yaya za mu jimre wa damuwa na rayuwa?
-
Ta yaya za mu kyautata farin cikin iyalinmu?
-
Menene yake samun mu sa’ad da muka mutu?
-
Za mu sake ganin ’yan’uwanmu da suka rasu kuwa?
-
Ta yaya za mu tabbata cewa Allah zai cika waɗannan alkawuransa game da rayuwa ta nan gaba?
Ganin cewa kana karanta wannan littafin ya nuna cewa kana so ka fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Wannan littafin zai taimake ka. Ka kula cewa kowane sakin layi yana da nasa tambaya a ƙasan shafin. Miliyoyin mutane sun ji daɗin wannan salon nazari na tambayoyi da amsoshi wajen nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah. Muna fatan kai ma za ka ji daɗinsa. Allah ya yi maka albarka sa’ad da kake fahimtar abin da ainihi Littafi Mai Tsarki yake koyarwa!