Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA ƊAYA

Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Wahala?

Me Ya Sa Allah Ya Ƙyale Wahala?
  • Allah ne ya haddasa wahalar duniya?

  • Wane batu ne ya taso a gonar Adnin?

  • Ta yaya Allah zai magance wahalar ’yan adam?

1, 2. Wace irin wahala mutane suke sha a yau, kuma waɗanne tambayoyi take sa mutane su yi?

BAYAN wani ƙazamin faɗa da aka yi a wata ƙasa da ake yaƙi, aka kashe dubban mutane farar hula, mata da yara aka binne su a kabari guda aka saka alama. Alamar tana ɗauke da wannan rubutu: “Me ya sa?” Wani lokaci wannan ita ce tambaya mafi ƙuna. Mutane suna yin ta da baƙin ciki sa’ad da yaƙi, annoba, cuta, ko kuma wani abu makamancin haka ya halaka wani da suke ƙauna, ko ya halaka gidajensu, ko kuma ya jawo musu wahala a hanyoyi dabam dabam. Suna so su san abin da ya sa irin wannan masifa ta faɗa musu.

2 Me ya sa Allah ya ƙyale wahala? Idan Jehobah Allah ya fi kowa iko, yana da ƙauna, yana da hikima, yana da adalci, me ya sa duniya take cike da ƙiyayya da rashin adalci? Ka taɓa yin irin waɗannan tambayoyin da kanka?

3, 4. (a) Me ya nuna cewa ba laifi ba ne a tambayi dalilin da ya sa Allah ya ƙyale wahala? (b) Yaya Jehobah yake ji game da mugunta da kuma wahala?

3 Ba daidai ba ne a tambayi abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala? Wasu suna damuwa cewa yin irin wannan tambayar yana nufin cewa ba su da cikakkiyar bangaskiya ko kuma sun rena Allah. Amma sa’ad da kake karatun Littafi Mai Tsarki, za ka ga cewa mutane masu tsoron Allah masu aminci, sun yi irin waɗannan tambayoyin. Alal misali, annabi Habakkuk ya tambayi Jehobah: “Don me ka ke nuna mini saɓo, ka sa ni in duba shiririta kuma? Gama ɓarna da mugunta suna gabana; akwai husuma, jayayya kuma ta taso.”—Habakkuk 1:3.

Jehobah zai kawo ƙarshen dukan wahala

4 Shin Jehobah ya tsawata wa annabi Habakuk mai aminci ne domin ya yi waɗannan tambayoyi? A’a. Maimakon haka, Allah ya saka kalmomin Habakuk a cikin Littafi Mai Tsarki. Allah ya taimake shi ya fahimci batun sosai kuma ya kasance da bangaskiya mai ƙarfi. Jehobah yana so kai ma ka kasance haka. Ka tuna cewa Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa “yana kula da” kai. (1 Bitrus 5:7) Allah yana ƙin mugunta da kuma wahala fiye da dukan wani mutum. (Ishaya 55:8, 9) To, me ya sa ake wahala haka da yawa a duniya?

ME YA SA WAHALA TA YI YAWA?

5. Waɗanne bayanai aka yi wa wasu game da dalilin wahala, amma menene Littafi Mai Tsarki yake koyarwa?

5 Mutanen addinai dabam dabam sun je ga shugabannin addinansu da malamansu sun yi tambaya me ya sa ake wahala haka da yawa. Sau da yawa, amsar da ake bayarwa ita ce wahala nufin Allah ne, ya riga ya ƙaddara dukan abin da zai faru tun dā har da masifu. An kuma faɗa wa mutane da yawa cewa al’amuran Allah ba a fahimtarsu ko kuma shi yake haddasa mutuwar mutane—har da ta yara—saboda su kasance tare da shi a sama. Amma kamar yadda ka koya, Jehobah Allah ba ya yin mugun abu. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Daɗai Allah shi yi mugunta! Mai-iko duka shi yi aikin saɓo!”—Ayuba 34:10.

6. Me ya sa mutane suke yin kuskuren ɗora wa Allah alhakin wahalar duniya?

6 Ka san abin da ya sa mutane suke yin kuskuren ɗora wa Allah alhakin dukan wahalar duniya? Yawanci, suna ɗora wa Allah Mai Iko Duka laifi ne domin suna zaton shi ne ke mulkin wannan duniyar. Ba su san wata gaskiya mai sauƙi amma mai muhimmanci da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa ba. Ka koyi wannan gaskiyar a Babi na 3 na wannan littafi. Ainihin mai mulkin wannan duniyar Shaiɗan Iblis ne.

7, 8. (a) Ta yaya duniya take nuna halin wanda yake sarautarta? (b) Ta yaya ajizancin mutane da kuma “sa’a, da tsautsayi” suka ba da gudummawa wajen jawo wahala?

7 Littafi Mai Tsarki ya faɗa a fili cewa: “Duniya duka kuwa tana kwance cikin Shaiɗan.” (1 Yohanna 5:19) Sa’ad da ka yi tunani a kansa, wannan ba gaskiya ba ne? Wannan duniyar tana nuna irin hali ne na halittar ruhu marar ganuwa “mai-ruɗin dukan duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 12:9) Shaiɗan maƙiyi ne, mayaudari, maƙetacci. Shi ya sa duniyar da take ƙarƙashin ikonsa take cike da ƙiyayya, yaudara, da ƙeta. Wannan dalili ne guda na abin da ya sa ake wahala haka mai yawa.

8 Dalili na biyu game da abin da ya sa ake wahala shi ne kamar yadda aka tattauna a Babi na 3, mutane ajizai ne kuma masu zunubi tun daga lokacin tawaye a gonar Adnin. Mutane masu zunubi suna kokawa domin iko, kuma haka yana jawo yaƙe-yaƙe, zalunci, da wahala. (Mai-Wa’azi 4:1; 8:9) Dalilin wahala na uku shi ne cewa ‘sa’a, da tsautsayi, sukan sami kowannenmu.’ (Mai-Wa’azi 9:11 Littafi Mai Tsarki) A duniya da ba Jehobah ba ne Sarkinta mai kāre ta, mutane za su wahala domin sun kasance a wuri a lokacin da bai dace ba.

9. Me ya sa za mu tabbata cewa Jehobah yana da kyakkyawan dalili na ƙyale wahala ta ci gaba?

9 Abin farin ciki ne a gare mu mu fahimci cewa Allah ba ya jawo wahala. Ba shi ke da alhakin yaƙe-yaƙe, yin laifi, da kuma zalunci, har ma da annoba da suka haddasa wahala ga mutane ba. Duk da haka, muna bukatar mu san, Me ya sa Jehobah ya ƙyale wahala? Idan shi Mai Iko Duka ne, yana da ikon kawar da ita. To, me ya sa ya ƙyale ta? Allah mai ƙauna da muka zo ga fahimta dole ne ya kasance yana da kyakkyawan dalili.—1 Yohanna 4:8.

AN TA DA BATU MAI MUHIMMANCI

10. Menene Shaiɗan ya ƙalubalanta, kuma ta yaya?

10 Domin mu fahimci abin da ya sa Allah ya ƙyale wahala, muna bukatar mu tuna lokacin da wahala ta fara. Sa’ad da Shaiɗan ya rinjayi Adamu da Hauwa’u su yi wa Jehobah rashin biyayya, wata tambaya mai muhimmanci ta taso. Shaiɗan bai ƙalubalanci ikon Jehobah ba. Shaiɗan kansa ya sani cewa ikon Jehobah ba shi da iyaka. Maimakon haka, Shaiɗan ya ƙalubalanci dacewar sarautar Jehobah. Ta wajen cewa Allah maƙaryaci ne wanda yake hana bayinsa abin da ke mai kyau, Shaiɗan ya yi zargin cewa Jehobah mugun sarki ne. (Farawa 3:2-5) Shaiɗan yana cewa ne mutane za su fi jin daɗi ba tare da Allah yana sarauta a kansu ba. Wannan hari ne ga ikon mallaka na Jehobah, dacewar sarautarsa.

11. Me ya sa Jehobah bai halaka ’yan tawayen ba kawai a Adnin?

11 Adamu da Hauwa’u sun yi wa Jehobah tawaye. Wato, cewa suka yi: “Ba ma son Jehobah ya yi Sarauta a kanmu. Za mu shawarta wa kanmu abin da ke nagarta da abin da ke mugunta.” Ta yaya Jehobah zai magance wannan batu? Ta yaya Jehobah zai koya wa dukan halittu masu tunani cewa waɗannan ’yan tawaye sun yi kuskure, tafarkinsa shi ne daidai? Wasu za su ce da Allah ya halaka waɗannan ’yan tawaye kawai ya sake yin wasu. Amma Jehobah ya riga ya faɗi nufinsa na cika duniya da ’ya’yan Adamu da Hauwa’u, yana so su zauna a cikin aljanna a duniya. (Farawa 1:28) Jehobah ko a yaushe yana cika nufinsa. (Ishaya 55:10, 11) Ban da haka ma, halaka ’yan tawayen a Adnin ba zai warware batu da ta taso ba game da dacewar sarautar Jehobah.

12, 13. Ka kwatanta abin da ya sa Jehobah ya ƙyale Shaiɗan ya zama masaraucin wannan duniyar da kuma abin da ya sa Allah ya ƙyale mutane su mallaki kansu.

12 Bari mu dubi wani kwatanci. Alal misali, malami yana koya wa ɗalibansa yadda za su magance wata matsala. Wani ɗalibi mai basira amma ɗan tawaye ya yi da’awar cewa yadda malamin yake magance matsalar ba daidai ba ne. Wato, yana nufi ne cewa malamin bai ƙware ba, wannan ɗan tawayen ya dage cewa ya san hanyar da ta fi kyau wajen magance matsalar. Wasu ɗalibai suka gaskata abin da ya ce, sai su ma suka yi tawaye. Menene malamin zai yi? Idan ya kori ’yan tawayen daga aji, yaya hakan zai shafi wasu ɗalibai? Ba za su yi tunanin cewa ɗalibin da waɗanda suka ba shi goyon baya suna da gaskiya ba? Dukan sauran ɗalibai a ajin za su rena malamin, domin za su ce yana tsoron a fallasa shi. Amma idan malamin ya ƙyale ɗan tawayen ya nuna wa ajin yadda shi zai magance matsalar fa?

Ɗalibin ya fi malamin ƙwarewa ne?

13 Jehobah ya yi abin da ya kamanci abin da malamin ya yi. Ka tuna cewa ’yan tawayen a Adnin ba su kaɗai ba ne. Wasu mala’iku miliyoyi suna kallo. (Ayuba 38:7; Daniel 7:10) Yadda Jehobah ya magance wannan tawayen a ƙarshe zai shafi dukan mala’iku da kuma halittu masu tunani. To, menene Jehobah ya yi? Ya ƙyale Shaiɗan ya nuna yadda shi zai mallaki mutane. Allah kuma ya ƙyale mutane su mallaki kansu a ƙarƙashin rinjayar Shaiɗan.

14. Wane amfani ne zai zo daga shawarar Jehobah ya ƙyale mutane su mallaki kansu?

14 Malamin kwatancinmu ya sani cewa ɗan tawayen da kuma ɗaliban da suka ba shi goyon baya sun yi kuskure. Kuma ya sani cewa ba su lokaci su yi ƙoƙari su tabbatar da batunsu zai amfani dukan ajin. Sa’ad da ’yan tawayen suka gaza, dukan ɗaliban za su ga cewa malamin ne kaɗai ya ƙware ya koyar da ajin. Za su fahimci dalilin da ya sa malamin ya kori duk wani ɗan tawaye daga ajin. Hakazalika, Jehobah ya sani cewa dukan mutane masu zuciyar kirki da kuma mala’iku za su amfana da ganin cewa Shaiɗan da ’yan tawaye masu goya masa baya sun gaza kuma mutane ba za su iya mallakar kansu ba. Kamar yadda Irmiya na zamanin dā ya ce, za su fahimci wannan gaskiyar: “Ya Ubangiji, na tabbata hanyar mutum ba cikin nasa hannu ta ke ba; mutum kuwa ba shi da iko shi shirya tafiyarsa.”—Irmiya 10:23.

ME YA SA TA DAƊE HAKA?

15, 16. (a) Me ya sa Jehobah ya ƙyale wahala ta daɗe haka? (b) Me ya sa Jehobah bai hana munanan laifuffuka faruwa ba?

15 Me ya sa Jehobah, ya ƙyale wahala ta daɗe haka? Me ya sa bai hana miyagun abubuwa daga faruwa ba? Ka yi la’akari da abubuwa biyu da malami na kwantancinmu ba zai yi ba. Da farko, ba zai hana ɗan tawayen ya ba da tabbacinsa ba. Na biyu, malamin ba zai taimaki ɗan tawayen ya gabatar da tabbacinsa ba. Hakazalika, ka yi la’akari da abubuwa biyu da Jehobah ya ƙuduri aniyar ba zai yi ba. Na farko, bai hana Shaiɗan da waɗanda suka ba shi goyon baya daga ƙoƙarin su tabbatar da cewa suna da gaskiya ba. Ba da lokaci ya wajaba. A shekaru dubbai na tarihin ’yan adam, ’yan adam sun taɓa salon sarauta dabam dabam, ko kuma gwamnatin mutane. ’Yan adam sun sami ci gaba a kimiyya da kuma wasu fannonin ilimi, amma rashin adalci, talauci, yin laifi, da kuma yaƙi sun munanta. A yanzu an nuna cewa sarautar mutane ta gaza.

16 Na biyu, Jehobah bai taimaki Shaiɗan ya yi mulkin wannan duniyar ba. Alal misali, idan Allah ya hana munanan laifuffuka, hakan ba zai taimaka wa ’yan tawayen ba ne su tabbatar da batunsu? Ta haka Allah ba zai sa mutane su yi tunanin cewa wataƙila ’yan adam za su iya mallakar kansu ba tare da sakamako mai haɗari ba? Idan Jehobah ya yi haka, zai kasance yana tarayya da maƙaryata. Amma “ba shi yiwuwa Allah ya yi ƙarya.”—Ibraniyawa 6:18.

17, 18. Menene Jehobah zai yi game da dukan lahani da suka samu daga sarautar mutane da kuma rinjayar Shaiɗan?

17 To, yaya game da dukan lahanin da aka yi a wannan dogon lokaci na tawaye ga Allah? Ya kamata mu tuna cewa Jehobah shi ne Mai Iko Duka. Saboda haka, zai iya kuma zai kawar da sakamakon wahalar ’yan adam. Kamar yadda muka riga muka koya, za a gyara dukan wani lahani da aka yi wa duniyarmu sa’ad da aka mai da ita Aljanna. Za a kawar da sakamakon zunubi ta wajen ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Yesu, kuma sakamakon mutuwa ta wajen tashin matattu. Ta haka Allah zai yi amfani da Yesu “halaka ayyukan Shaiɗan.” (1 Yohanna 3:8) Jehobah zai yi dukan waɗannan a lokacin da ya dace. Ya kamata mu yi godiya da bai yi waɗannan da wuri ba, domin haƙurinsa ya ba mu zarafin mu fahimci gaskiya kuma mu bauta masa. (2 Bitrus 3:9, 10) A yanzu, Allah yana neman waɗanda suke so su bauta masa da gaske, kuma yana taimakonsu su jimre dukan wata wahala da za ta same su a wannan duniya ta wahala.—Yohanna 4:23; 1 Korinthiyawa 10:13.

18 Wasu za su yi tunani, da ba a hana dukan waɗannan wahaloli faruwa ba, da Allah ya halicci Adamu da Hauwa’u yadda ba za su iya yin tawaye ba? Domin mu amsa wannan tambayar, kana bukatar ka tuna wata kyauta mai tamani da Allah ya ba ka.

YAYA ZA KA YI AMFANI DA KYAUTA DA ALLAH YA YI?

Allah zai taimake ka ka jimre wa wahala

19. Wace kyauta ce mai muhimmanci Jehobah ya ba mu, kuma me ya sa za mu ɗauke shi da muhimmanci?

19 Kamar yadda muka gani a Babi na 5, an halicci ’yan adam da ’yancin zaɓe. Ka fahimci muhimmancin wannan kyautar? Allah ya yi dabbobi marasa iyaka, kuma waɗannan da ilhami suke amfani. (Misalai 30:24) Mutane sun ƙera ’yar tsana da suka tsara ta bi dukan umurni. Da za mu yi farin ciki da Allah ya halicce mu haka? A’a, muna farin ciki da muke da ’yancin zaɓan irin mutane da muke so mu zama, da kuma irin tafarkin rayuwa da za mu bi, irin abota da za mu ƙulla, da dai sauransu. Muna ƙaunar mu kasance da ’yanci, kuma abin da Allah yake so mu mora ke nan.

20, 21. Ta yaya za mu yi amfani da kyautar ’yancin zaɓe a hanyar da ta dace, kuma me ya sa za mu so mu yi haka?

20 Jehobah ba ya son bauta da aka yi don dole. (2 Korinthiyawa 9:7) Alal misali: Menene zai faranta wa iyaye rai ƙwarai—yaro ya ce “na gode” domin an gaya masa ya faɗi haka, ko kuma wadda ya faɗa don kansa daga zuciyarsa? To, tambayar ita ce, ta yaya za ka yi amfani da ’yancin zaɓin da Jehobah ya ba ka? Shaiɗan da kuma Adamu da Hauwa’u sun yi mummunan amfani da shi. Suka ƙi Jehobah Allah. Menene za ka yi?

21 Ka nemi zarafi ka yi amfani da ’yancinka na zaɓe a hanyar da take da kyau. Za ka iya shiga tsakanin mutane miliyoyi da suke goyon bayan Jehobah. Suna sa Allah ya yi farin ciki domin suna tabbatar da cewa Shaiɗan maƙaryaci ne, wanda ya gaza wajen sarauta. (Misalai 27:11) Kai ma za ka iya yin haka ta wajen zaɓan tafarki mai kyau na rayuwa. Za a yi bayani game da wannan a babi na gaba.