Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 10

Sarkin Ya Tsabtace Ibadar Mutanensa

Sarkin Ya Tsabtace Ibadar Mutanensa

MANUFAR WANNAN BABIN

Dalili da kuma yadda Yesu ya tsabtace ibadar mabiyansa

1-3. Mene ne Yesu ya yi sa’ad da ya tarar cewa ana gurɓata haikalin?

 YESU yana daraja haikalin da ke Urushalima sosai don ya san abin da haikalin yake wakilta. Tun da daɗewa, haikalin ne cibiyar ibada ta gaskiya a duniya. Amma wajibi ne wannan ibadar, wato ibada ga Jehobah Allah mai tsarki ta kasance da tsarki. Ka yi tunanin yadda Yesu ya ji sa’ad da ya shiga cikin haikalin a ranar 10 ga watan Nisan, shekara ta 33 a zamaninmu kuma ya tarar ana gurɓata haikalin. Mene ne ake yi a ciki?—Karanta Matta 21:12, 13.

2 ’Yan kasuwa da masu musanyar kuɗi a Farfajiyar ’yan Al’ummai suna cutar da mutanen da suka je haikalin don su ba da hadaya ga Jehobah. a Sai Yesu ya “fitar da dukan masu-sayarwa da masu-saye cikin haikali, ya jirkitar da tebura na masu-musanyar kuɗi.” (Ka gwada Nehemiya 13:7-9.) Ya yi tir da waɗannan mutane masu son zuciya don sun mai da gidan Ubansa “kogon mafasa.” Ta hakan, Yesu ya daraja haikalin da kuma abin da take wakilta. Wajibi ne ibada ga Allah ta kasance da tsarki!

3 Shekaru aru-aru bayan haka, sa’ad da aka naɗa shi Sarki, Yesu ya sake tsabtace wani haikali wanda ya shafi dukan waɗanda suke so su bauta wa Jehobah a hanyar da ta dace a yau. Wane haikali ne ya tsabtace?

An Tsarkake “’Ya’yan Levi”

4, 5. (a) Ta yaya aka tsabtace mabiyan Yesu shafaffu daga shekara ta 1914 zuwa farkon 1919? (b) Shin wannan ne tsabtacewa na ƙarshe da aka yi wa mutanen Allah? Ka bayyana.

4 Kamar yadda muka tattauna a Babi na 2 na wannan littafin, bayan da aka naɗa Yesu Sarki a shekara ta 1914, shi da Ubansa sun zo don su bincika haikali na alama, wato ƙungiyar Allah da ke duniya. b Sa’ad da ya yi wannan binciken, Sarkin ya ga cewa “’ya’yan Levi,” wato Kiristoci shafaffu, suna bukatar tsabtacewa. (Mal. 3:1-3) Daga shekara ta 1914 zuwa farkon 1919, Jehobah wanda shi ne ‘Mai-tsarkakewa,’ ya ƙyale mutane su fuskanci gwaji da mawuyacin hali kuma hakan ya tsabtace su. Abin farin ciki shi ne bayan wannan gwaji mai tsanani, sun kasance masu tsarki kuma a shirye don su tallafa wa Sarki Almasihu!

5 Shin wannan shi ne ƙarshen tsabtacewar da aka yi wa mutanen Allah? A’a. A cikin kwanaki na ƙarshe, Jehobah ya ci gaba da yin amfani da Sarki Almasihu wajen taimaka wa mabiyansa su kasance da tsabta don su ci gaba da zama cikin haikali na alama. A babobi biyu da ke gaba, za mu ga yadda ya tsabtace ɗabi’arsu da kuma ƙungiyar da suke ciki. Amma yanzu za mu tattauna tsabtacewa da ta shafi ibadarsu. Za mu tattauna abubuwan da Yesu ya yi don ya tsabtace ibadar mabiyansa. Hakan ya ƙunshi abubuwan da ya yi da ake gani da waɗanda da ba sa ganuwa kuma hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu.

‘Ku Tsarkake’ Kanku

6. Ta yaya umurnin Jehobah ga Yahudawa da ke bauta a Babila ya taimaka mana mu fahimci abin da ibada mai tsabta ta ƙunsa?

6 Mece ce tsabtacewa ta ibada take nufi? Don mu sami amsar, bari mu bincika annabcin da Jehobah ya yi game da lokacin da Yahudawa da suke bauta a Babila za su bar ƙasar a ƙarni na shida kafin zamaninmu. (Karanta Ishaya 52:11.) Waɗannan Yahudawa suna dawowa Urushalima ne don su sake gina haikalin kuma su maido da bauta ta gaskiya. (Ezra 1:2-4) Jehobah yana so mutanensa su bar duk wani abu da ke da alaƙa da addinin Babila. Ka lura cewa ya ba su umurni ɗaya bayan ɗaya, ya ce: “Kada ku taɓa wani abu mai-ƙazamta,” “ku fita daga cikin tsakiyarta,” da kuma ‘ku tsarkake’ kanku. Wajibi ne su guji gurɓata bautar Jehobah da bautar ƙarya. Mene ne hakan ya ƙunsa? Ibada mai tsabta ta ƙunshi ware kanmu daga koyarwa da ayyukan bauta ta ƙarya.

7. Wane rukuni ne Yesu ya yi amfani da shi wajen taimaka wa mabiyansa su tsabtace ibadarsu?

7 Jim kaɗan bayan an naɗa shi Sarki, Yesu ya kafa rukunin bawa mai aminci mai hikima a shekara ta 1919. Wannan rukunin ne zai taimaka wa mabiyansa su tsabtace ibadarsu kuma bai yi wuya a gane wannan rukunin ba. (Mat. 24:45) Kafin wannan shekarar, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun riga sun tsabtace kansu daga koyarwar addinin ƙarya da yawa. Duk da haka, sun bukaci a ƙara tsabtace su. Kristi ya yi amfani da bawa mai aminci don ya ilimantar da mabiyansa game da wasu bukukuwa da ayyuka da suke bukata su daina yi. (Mis. 4:18) Bari mu tattauna wasu daga cikinsu.

Ya Kamata Kiristoci Su Yi Bikin Kirsimati Ne?

8. Mene Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka gano da daɗewa game da Kirsimati, kuma mene ne ba su ga amfanin yi ba?

8 Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun daɗe da sanin cewa Kirsimati ya samo tushe ne daga koyarwar arna kuma ba a haifi Yesu a ranar 25 ga Disamba ba. Mujallar Zion’s Watch Tower [Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona] ta watan Disamba, 1881, ta ce: “Miliyoyin mutane sun shiga coci ne daga addinan Arna. Amma canjin a suna ne kawai, wato an canja limaman addinan arna zuwa limaman coci, kuma an ba wa bukukuwan arna sunayen kirista, Kirsimati ɗaya ne daga cikin irin waɗannan bukukuwan.” A shekara ta 1883, wani talifin Hasumiyar Tsaro mai jigo “When Was Jesus Born?” (Yaushe Ne Aka Haifi Yesu?), ya bayyana cewa an haifi Yesu a farkon watan Oktoba ne. c Duk da haka, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba su ga amfanin daina yin bikin Kirsimati ba. Har ma waɗanda suke hidima a Bethel da ke Brooklyn sun ci gaba da yin bikin. Amma bayan shekara ta 1926, abubuwa sun soma canjawa. Me ya sa?

9. Mene ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka gano game da bikin Kirsimati?

9 Bayan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka bincika batun cikin natsuwa, sun gano cewa tushen bikin Kirsimati da kuma harkokin da ke tattare da bikin ba sa girmama Allah. Mujallar The Golden Age ta 14 ga Disamba, 1927, mai jigo: “The Origin of Christmas,” (Tushen Kirsimati) ta ce Kirsimati bikin arna ne da ya mai da hankali ga annashuwa da kuma bautar gumaka. Mujallar ta bayyana cewa Kristi bai umurta a yi bikin ba kuma ya kammala da wannan bayanin: “Hakika, tun da yake duniyar nan da Shaiɗan suna ɗaukaka wannan bikin kuma yana gamsar da sha’awar jiki . . . hakan ya nuna cewa bai dace waɗanda suka ware kansu don su bauta wa Jehobah su yi bikin ba.” Wannan dalilin ne ya sa iyalin Bethel ba su yi bikin Kirsimati a watan Disamba na shekarar ba, kuma ba su ƙara yin bikin ba!

10. (a) Wane jawabi ne aka bayar a watan Disamba 1928 da ya fallasa Kirsimati? (Ka kuma duba akwatin nan, “ Tushen Bikin Kirsimati da Kuma Manufarsa.”) (b) Ta yaya aka daɗa buɗe wa bayin Allah ido game da wasu bukukuwan arna? (Ka duba akwatin nan, “ Yadda Aka Fallasa Tushen Wasu Bukukuwa.”)

10 A shekara ta gaba, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun sami wani bayanin da ya ƙara fallasa bikin Kirsimati. A ranar 12 ga Disamba, 1928, Ɗan’uwa Richard H. Barber, wanda ke hidima a hedkwata, ya ba da wani jawabi da aka ɗauka a rediyo da ya fallasa tushen wannan bikin. Wane mataki ne ’yan’uwa suka ɗauka bayan sun sami wannan ja-gorar da hedkwata ta bayar? Ɗan’uwa Charles Brandlein, wanda shi da iyalinsa suka daina yin bikin Kirsimati, ya ce: “Bai yi mana wuya mu daina bukukuwan arna ba. Don yin hakan yana kamar tuɓe riga mai datti ne a yar.” Hakazalika, Ɗan’uwa Henry A. Cantwell, wanda daga baya ya yi hidima a matsayin mai kula mai ziyara, ya ce: “Mun yi farin cikin daina yin bikin don mu nuna cewa muna ƙaunar Jehobah.” Mabiyan Kristi masu aminci sun yi canji da son rai kuma sun ƙudura su cire hannu daga dukan bukukuwan da ke da alaƙa da ibada marar tsarki. dYoh. 15:19; 17:14.

11. Ta yaya za mu nuna cewa muna goyon bayan Sarki Almasihu?

11 Hakika, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun kafa mana misali mai kyau! Zai dace mu yi tunani sosai a kan misalinsu, kuma mu yi wa kanmu waɗannan tambayoyin: ‘Mene ne ra’ayina game da ja-gorar da bawa mai aminci yake bayarwa? Shin ina bin ja-gorar da zuciya ɗaya?’ Idan muka yi biyayya, hakan zai nuna cewa muna goyon bayan Sarki Almasihu, wanda yake amfani da bawa mai aminci wajen tanadar da koyarwar Allah.—A. M. 16:4, 5.

Ya Kamata Kiristoci Su Yi Amfani da Alamar Gicciye Ne?

Alamar gicciye-da-kambi (Ka duba sakin layi na 12 da 13)

12. Ta yaya Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke ɗaukan gicciye a dā?

12 A cikin shekaru da yawa, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna ɗaukan alamar gicciye a matsayin abu mai muhimmanci ga Kiristoci. Amma ba sa bauta wa gicciye, da yake sun san cewa bai da kyau a bauta wa gunki. (1 Kor. 10:14; 1 Yoh. 5:21) Tun daga shekara ta 1883, Hasumiyar Tsaro ta bayyana dalla-dalla cewa “Allah ya tsani bautar gumaka.” Amma, da farko, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki ba su ga ƙwararan dalilai da suka nuna cewa yin amfani da gicciye bai da kyau ba. Alal misali, suna alfaharin saka bajo da ke ɗauke da zanen gicciye-da-kambi a matsayin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. Suna gani kamar wannan giciye-da-kambi alama ce da ke nuna cewa idan suka kasance da aminci har mutuwa, za su sami kambin rai na har abada. A shekara ta 1891 ne aka soma fitar da Hasumiyar Tsaro da ke ɗauke da hoton gicciye-da-kambi.

13. Wane ƙarin haske ne mabiyan Kristi suka samu game da amfani da gicciye? (Ka kuma duba akwatin nan “ An Sami Ƙarin Haske da Sannu-sannu Game da Amfani da Gicciye.”)

13 Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna son alamar gicciye-da-kambi sosai a dā. Amma tun daga ƙarshen shekara ta 1920, an ci gaba da wayar da kan mabiyan Kristi game da yin amfani da gicciye. Sa’ad da Ɗan’uwa Grant Suiter, wanda daga baya ya zama memban Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah yake magana game da babban taron da aka yi a shekara ta 1928 a Detroit da ke jihar Michigan, a Amirka, ya ce: “A babban taron an nuna mana cewa alamar gicciye-da-kambi haramun ce kuma ba ta da amfani.” A cikin ’yan shekaru bayan hakan, an daɗa samun ƙarin haske. A bayyane yake cewa bai dace a yin amfani da gicciye a ibada ga Allah ba.

14. Wane mataki ne mutanen Allah suka ɗauka sa’ad da suka sami ƙarin haske game da gicciye?

14 Wane mataki ne bayin Allah suka ɗauka game da wannan ƙarin haske da suka samu game da yin amfani da gicciye a ibadarsu? Shin sun ci gaba da yin amfani da wannan gicciye-da-kambi da suka ɗauka da muhimmanci kuwa? Wani Ɗan’uwa da ya daɗe yana bauta wa Jehobah, mai suna Lela Roberts, ya ce: “Mun daina amfani da shi sa’ad da muka fahimci abin da yake wakilta.” Furucin wata amintacciyar ’yar’uwa mai suna Ursula Serenco, ya bayyana ra’ayin mutane da yawa. Ta ce: “Mun fahimci cewa tushen wannan abin da muke ɗaukakawa a matsayin alamar mutuwar Ubangijinmu kuma muke amfani da shi a ibada ainihi daga arna ne. Bisa ga abin da aka fada a littafin Misalai 4:18, muna farin ciki cewa mun sami wannan ƙarin haske.” Mabiyan Kristi masu aminci suna so su tabbata cewa sun rabu da duk wata koyarwar addinin ƙarya!

15, 16. Ta yaya za mu nuna cewa mun ƙuduri niyya mu sa ƙungiyar Jehobah ta kasance da tsabta?

15 Mu ma ƙudurinmu ke nan a yau. Mun fahimci cewa Jehobah yana amfani da bawa mai aminci mai hikima don ya taimaka wa bayinsa su yi masa ibada a hanyar da ta dace. Saboda haka, idan aka ba mu ƙarin haske game da wasu bukukuwa da ayyuka da kuma al’adun da suka samo asali daga addinin ƙarya, ya kamata mu ɗauki mataki nan da nan. Mun ƙuduri niyyar sa ƙungiyar Jehobah ta kasance da tsabta kamar yadda ’yan’uwan da suka rayu a lokacin bayyanuwar Kristi suka yi.

16 A waɗannan kwanaki na ƙarshe, Yesu yana aiki tuƙuru don ya kāre ikilisiyoyin bayin Allah daga mutanen da suke so su gurɓata su da koyarwar ƙarya. Ta yaya yake yin hakan? Bari mu bincika.

Ware “Miyagu Daga Cikin Masu Adalci”

17, 18. A kwatancin taru, mene ne ma’anar (a) jefa tarun cikin teku, (b) “tattara . . . kowane irin kifi,” (c) tattara kifi masu kyau cikin kurtuna da kuma (d) zubar da ‘munanan’ kifi?

17 Sarkinmu Yesu Kristi yana kula da ƙungiyar mutanen Allah a faɗin duniya sosai. Shi da mala’ikunsa suna aiki tuƙuru wajen ware tumaki daga awaki ko da yake ba ma ganinsu da idanunmu. Yesu ya bayyana wannan aikin a kwatancin da ya yi na taru. (Karanta Matta 13:47-50.) Mene ne wannan kwatancin yake nufi?

Tarun yana wakiltar wa’azin Mulkin Allah da ake yi dukan duniya (Ka duba sakin layi na 18)

18 Jefa “tarun . . . cikin teku.” Tarun yana wakiltar wa’azin Mulki da ake yi a dukan duniya. “Tattara . . . kowane irin kifi.” Bisharar tana jawo mutane dabam-dabam, wato waɗanda suka ɗauki matakin zama Kiristoci na gaske da waɗanda suka nuna suna son saƙon amma ba su ɗauki matakin bauta wa Jehobah ba. e “Suka tattara masu-kyau, suka zuba cikin kurtuna.” An tattara mutane masu kirki zuwa ikilisiyoyin da ke kama da kurtuna domin su bauta wa Jehobah a hanyar da ta dace. Suka zubar da ‘munanan’ kifi. A waɗannan kwanaki na ƙarshe, Kristi da mala’ikunsa suna aiki tuƙuru don su “rarraba miyagu daga cikin masu adalci.” f A sakamakon haka, ba a barin waɗanda suka ƙi canja halayensu ko kuma suka yi watsi da koyarwar ƙarya su gurɓata ikilisiyoyin. g

19. Yaya kake ji game da abin da Kristi yake yi don ya tsabtace ibadar mutanen Allah?

19 Sanin cewa Sarkinmu, Yesu Kristi, yana kāre mutanensa abin farin ciki ne. Shin ba abin ban ƙarfafa ba ne mu san cewa Yesu yana nuna ƙwazo wajen tsabtacce mabiyansa da kuma ibada ta gaskiya a yau kamar yadda ya yi a ƙarni na farko? Muna godiya cewa Kristi ya ci gaba da tsabtacce mutanensa da kuma ibada ta gaskiya! Bari mu nuna cewa muna goyon bayan Sarkin da kuma Mulkinsa ta wajen daina kowane irin sha’ani da addinin ƙarya.

a Yahudawa da suka zo daga wasu wurare suna zuwa da irin kuɗi da ba a amfani da shi a Urushalima. Saboda haka, don su samu su biya harajin haikali da ake biya shekara-shekara, sukan biya masu canja kuɗi don su canja musu kuɗin. Ƙari ga haka, wataƙila waɗannan Yahudawa da suka ziyarci haikalin sun bukaci su sayi dabbobi don ba da hadaya. Yesu ya kira waɗannan ’yan kasuwan “mafasa” mai yiwuwa don suna sayar da abubuwa da tsada ko kuma suna karɓan kuɗi mai yawa daga wajen Yahudawan.

b Bayin Jehobah a duniya suna bauta masa a farfajiyar haikali na alama da ke duniya.

c Wannan talifin ya nuna cewa lokacin sanyi da aka ce an haifi Yesu “bai jitu da bayanin da aka yi game da makiyaya cewa suna kula da dabbobinsu a waje ba.”—Luk 2:8.

d Ɗan’uwa Frederick W. Franz ya bayyana a cikin wata wasiƙa da ya rubuta a ranar 14 ga Nuwamba, 1927, cewa: “Ba za mu yi bikin Kirsimati wannan shekarar ba. Iyalin Bethel sun yarda cewa ba za su ƙara yin bikin Kirsimati ba.” Bayan wasu ’yan watanni, Ɗan’uwa Franz ya rubuta wata wasiƙa a ranar 6 ga Fabrairu, 1928, ya ce: “Da sannu a hankali, Ubangiji yana tsarkake mu daga koyarwar Shaiɗan da kuma Addinan ƙarya.”

e Alal misali, a shekara ta 2013, adadin masu shela 7,965,954 ne, kuma mutane 19,241,252 ne suka halarci taron Tunawa da Mutuwar Yesu.

f Ware kifaye masu kyau daga munana ba ɗaya ba ne da ware tumaki daga awaki. (Mat. 25:31-46) Za a yi wannan warewar ko kuma shari’a ta ƙarshe da ta shafi tumaki da awaki a lokacin ƙunci mai girma. Kafin wannan lokacin, waɗanda suke kamar munanan kifi za su iya komawa ga Jehobah da kuma ikilisiyoyi da ke kamar kurtuna.—Mal. 3:7.

g Daga baya, za a jefa munanan kifayen a cikin wuta mai ruruwa, wato za a halaka su.