Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 2

An Kafa Mulkin a Sama

An Kafa Mulkin a Sama

MANUFAR WANNAN BABIN

Yadda Allah ya shirya bayinsa kafin a kafa Mulkin

1, 2. Wace aukuwa mafi girma ce ta faru a tarihi, kuma me ya sa mutane ba su ga wannan aukuwar ba?

 KA TAƁA yin tunanin yadda rayuwa ta kasance sa’ad da aka yi wani gagarumin canji a tarihi? Mutane da yawa sun taɓa rayuwa a irin wannan lokacin. Amma ka yi la’akari da wannan: Da a ce ka rayu a wannan lokacin, za ka shaida abin da ya kai ga wannan canjin kuwa? Wataƙila a’a. Me ya sa? Domin wasu abubuwa da suke sa a yi juyin mulki ba sa faruwa a gaban jama’a. Yawancin canjin da ake yi a tarihi suna faruwa ne a ɓoye, wato a daƙuna ko gidajen sarauta da jam’iyoyi ko kuma ofisoshin gwamnati. Duk da haka, waɗannan canjin suna shafan rayuwar miliyoyin mutane.

2 Aukuwa mafi girma da ta taɓa faruwa tarihin duniya fa? Wannan aukuwar ta shafi rayuwar miliyoyin mutane. Wannan abin bai faru a duniya ba. Hakika, muna magana ne game da Mulkin Allah da aka kafa a sama, wato gwamnatin Almasihu da aka yi alkawarinta tun da daɗewa, wadda za ta kawo ƙarshen mugun yanayin da duniya take ciki. (Karanta Daniyel 2:34, 35, 44, 45.) Tun da yake ’yan Adam ba su ga lokacin da aka kafa wannan gwamnatin ba, shin hakan yana nufin cewa Jehobah ya hana ’yan Adam sanin abin da ya faru ne? Shin ya shirya amintattun bayinsa ne kafin lokacin? Bari mu bincika.

“Manzona . . . Za Ya kuwa Shirya Tafarki a Gabana”

3-5. (a) Wane ne “mala’ikan alkawari” da aka ambata a littafin Malakai 3:1? (b) Mene ne zai faru kafin zuwan “mala’ikan alkawari” haikali ta alama?

3 Tun dā can, nufin Jehobah shi ne ya shirya mutanensa don Mulkin Almasihu da za a kafa. Alal misali, ka yi la’akari da annabcin da ke littafin Malakai 3:1: “Duba, ina aike manzona, za ya kuwa shirya tafarki a gabana; Ubangiji ma, wanda ku ke biɗarsa, za ya zo a haikalinsa ba labari; mala’ikan alkawari kuma, wanda ku ke murna da shi.”

4 A cikar annabcin nan a zamaninmu, yaushe ne Jehobah, wato “Ubangiji” da aka ambata a annabcin nan, ya zo don ya bincika waɗanda suke yin hidima a haikali na alama a duniya? Annabcin ya ce Jehobah zai zo tare da “mala’ikan alkawari.” Waye ke nan? Babu shakka, Sarki Almasihu ne, wato Yesu Kristi! (Luk 1:68-73) A matsayin sabon Sarki, Yesu zai bincika bayin Allah da ke duniya, kuma ya yi musu gyara.—1 Bit. 4:17.

5 To, wane ne wannan ‘manzon’ da aka ambata da farko a littafin Malakai 3:1? Wannan da aka yi annabcinsa zai kasance kafin bayyanuwar Sarki Almasihu. A shekarun da suka gabaci 1914, shin akwai wanda ya “shirya tafarki” don Sarki Almasihu?

6. Wane ne ‘manzon’ da ya fara zuwa don ya shirya bayin Allah domin abubuwa da za su faru a nan gaba?

6 Za mu sami amsoshin waɗannan tambayoyin a cikin wannan littafin yayin da muke tattauna tarihi mai ƙayatarwa game da mutanen Jehobah a zamaninmu. Tarihin ya nuna cewa a ƙarshen ƙarni na sha tara, wani ƙaramin rukuni na amintattun mutane ya bayyana a matsayin rukunin Kiristoci na gaskiya a tsakanin jabun Kiristoci da yawa. Wannan rukunin shi ne ake kira Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a lokacin. Waɗanda suke musu ja-gora su ne Charles Taze Russell da abokan aikinsa. Hakika, kamar yadda aka ambata a annabcin ‘manzon,’ sun koya wa bayin Allah Littafi Mai Tsarki kuma sun shirya su don abubuwan da za su faru a nan gaba. To, bari mu tattauna hanyoyi huɗu da wannan ‘manzon’ ya yi hakan.

Yin Ibada Cikin Gaskiya

7, 8. (a) Su waye ne suka fallasa koyarwar kurwa marar mutuwa a shekara ta 1800 zuwa shekara ta1899? (b) Waɗanne koyarwa ne Ɗan’uwa Russell da abokansa suka fallasa cewa ƙarya ne?

7 Yayin da waɗannan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suke nazari, sun roƙi Jehobah ya yi musu ja-gora; sun kasance da fahimta guda, kuma suka wallafa gaskiyar Littafi Mai Tsarki da suka gano dalla-dalla. A ƙarnuka da yawa, Kiristendam sun kasance cikin duhun kai sosai game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki, domin tushen yawancin koyarwarta daga arna ne. Babban misali shi ne koyarwar nan cewa kurwa ba ta mutuwa. A tsakanin shekara ta 1800 da 1900, wasu masu nazarin Littafi Mai Tsarki sun bincika wannan koyarwar kuma sun gano cewa ba koyarwar Littafi Mai Tsarki ba ne. Henry Grew da George Stetson da kuma George Storrs sun yi rubuce-rubuce don bayyana wa mutane cewa wannan koyarwar ƙarya ce kuma sun yi jawabai kai tsaye game da hakan. a Wannan aikin da suka yi ya shafi rayuwar Charles Taze Russell da abokan aikinsa sosai.

8 Wannan ƙaramin rukuni na Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun gano daga baya cewa wasu koyarwa da suke da alaƙa da koyarwar kurwa ba ta mutuwa ƙarya ne kuma suna ruɗar da hankalin mutane. Alal misali, koyarwar nan cewa dukan mutane masu adalci za su je sama ko kuma Allah zai azabtar da mugaye a wutar jahannama. Russell da abokan aikinsa sun fallasa waɗannan ƙaryace-ƙaryace kai tsaye a talifofi da littattafai da ƙasidu da warƙoƙi da kuma jawabai da suka wallafa.

9. Ta yaya Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta nuna cewa koyarwar Allah-uku-cikin-daya ƙarya ce?

9 Har ila, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fallasa cewa koyarwa ta Allah-uku-cikin-ɗaya da ta yi tasiri ba daga Littafi Mai Tsarki ba ne. A shekara ta 1887, mujallar Zion’s Watch Tower (Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona) ta ce: “Nassosi sun yi bayani dalla-dalla game da dangantakar da ke tsakanin Jehobah da Ubangijinmu Yesu da kuma matsayin kowannensu.” Talifin ya sake bayyana wani abin ban mamaki, wato yadda “koyarwar Allah-uku-cikin-ɗaya da kuma Allah ɗaya cikin uku ya sami karɓa a wajen mutane da yawa. Amma hakan ya nuna cewa ’yan coci sun yi sakaci kuma sun ƙyale magabcin ya yaɗa koyarwar ƙarya.”

10. Ta yaya Hasumiyar Tsaro ta nuna cewa shekara ta 1914 tana da muhimmanci sosai?

10 Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta mai da hankali a kan annabci game da bayyanuwar Kristi, kamar yadda jigonta ta nuna. Amintattun shafaffun Kristi da suka saka hannu a rubuta wannan mujallar sun gane cewa annabcin Daniyel a kan ‘lokatai bakwai’ yana da alaƙa da lokacin da nufin Allah game da Mulkin Almasihu zai cika. Tun daga tsakanin shekara 1870 zuwa 1879, amintattun shafaffun sun nuna cewa shekara ta 1914 ce shekarar da lokatai bakwai za su zo ƙarshe. (Dan. 4:25; Luk 21:24) Ko da yake ’yan’uwanmu a lokacin ba su fahimci cewa wannan shekarar tana da muhimmanci sosai ba, duk da haka, sun yi ta wa’azin abubuwan da suka sani da ƙwazo, kuma aikinsu ya yi tasiri sosai.

11, 12. (a) Wane ne Ɗan’uwa Russell yake yaba wa don abubuwan da ya koyar? (b) Mene ne muhimmancin aikin da Ɗan’uwa Russell da abokansa suka yi kafin shekara ta 1914?

11 Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa masu aminci ba su yi da’awar cewa su ne suka gano gaskiyar Littafi Mai Tsarki ba. Russell ya yabi waɗanda suka gabace shi. Mafi muhimmanci, ya yabi Jehobah Allah wanda Shi ne yake koyar da mutanensa game da abubuwan da suke bukata su sani a lokacin da ya kamata. Hakika, Jehobah ya albarkaci ƙoƙarin Russell da abokansa a yadda suka tāce koyarwar gaskiya daga na ƙarya. Da shigewar shekaru, bambancin da ke tsakanin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da Kiristendam ya daɗa ƙaruwa.

Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa sun yaɗa gaskiyar Littafi Mai Tsarki

12 Waɗannan mutane masu aminci sun yi gagarumin aiki wajen ɗaukaka da kuma yaɗa gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki a shekarun da suka gabaci 1914! Mujallar Hasumiyar Tsaro ta Sihiyona ta 1 ga Nuwamba, 1917, ta ce: “Miliyoyin mutane a yau sun ’yantu daga tsoro saboda ƙaryace-ƙaryace kamar koyarwar wutar jahannama . . . Koyarwar gaskiya ta fara yaɗuwa tun shekaru arba’in da suka shige kuma za ta ci gaba sai ta cika dukan duniya. Magabtanta za su yi ƙoƙarin hana gaskiyar yaɗuwa, amma duk ƙoƙarinsu zai zama kamar zuba ruwa a kwando.”

13, 14. (a) Ta yaya ‘manzon’ ya taimaka don a shirya wa Sarki Almasihu tafarki? (b) Mene ne za mu iya koya daga ‘yan’uwanmu da suka wanzu fiye da ƙarni guda da ya shige?

13 Ka yi la’akari: Shin bayin Allah za su kasance da shiri ne a farkon bayyanuwar Kristi idan ba su san bambancin da ke tsakanin Kristi da Ubansa, Jehobah ba? A’a. Har ila, ba za su kasance da shiri ba idan suka ɗauka cewa rai marar mutuwa abu ne da kowa yake da shi a maimakon baiwar da Allah yake ba wasu mutane ƙalilan cikin waɗanda suka bi koyarwar Kristi. Ƙari ga haka, ba za su kasance da shiri ba idan suka ɗauka cewa Allah yana azabtar da mutane a wutar jahannama har abada! Babu shakka, ‘manzon’ ya shirya tafarki wa Sarki Almasihu!

14 Mu kuma fa a yau? Wane darasi ne za mu iya koya daga waɗannan ’yan’uwan? Mu ma muna bukatar mu nuna ƙwazo wajen karanta Kalmar Allah da kuma yin nazarinta. (Yoh. 17:3) Yayin da wannan duniyar take ƙara lalacewa saboda rashin sanin Allah, bari mu kasance da ƙwazo wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki don dangantakarmu da Allah ta daɗa danƙo!—Karanta 1 Timotawus 4:15.

“Ku Fito Daga Cikinta, Ya Al’ummata”

15. Mene ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka fahimta da sannu-sannu? (Ka duba Ƙarin bayani.)

15 Ɗaliban Littafi Mai Tsarkin sun koyar da cewa wajibi ne a daina harka da coci-cocin Kiristendom. A shekara ta 1879, mujallar Hasumiyar Tsaro ta yi magana game da “Cocin Babila.” Shin ta yi magana ne a kan shugabancin Paparuma ko kuma cocin Katolika? Ɗarikokin Furotestan sun yi shekaru suna koyar da cewa Babila da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki ita ce cocin Katolika. Amma a hankali, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun fahimta cewa dukan coci-cocin Kiristendam a yau su ne wannan “Babila” da aka yi maganarta. Me ya sa? Domin dukansu suna koyar da ƙaryace-ƙaryacen da aka tattauna a baya. b Da shigewar lokaci, littattafanmu sun soma ba da umurni kai tsaye a kan abin da masu zukatan kirki da ke coci-cocin Babila suke bukatar su yi.

16, 17. (a) Ta yaya littafi na uku na Millennial Dawn da kuma Hasumiyar Tsaro suka karfafa mutane su rabu da addinin ƙarya? (b) Me ya sa ba su ɗauki wannan kashedin da muhimmanci ba? (Ka duba ƙarin bayani.)

16 Alal misali, a shekara ta 1891, Kundi na 3 na Millennial Dawn ya tattauna yadda Allah ya yi watsi da Babila na zamani. Ya ce: “Allah ya yi watsi da dukan coci-cocin Kiristendam.” Ya ƙara da cewa: “Dukan waɗanda ba su amince da koyarwa da ayyukan ƙarya da take yaɗawa ba su fito daga cikinta.”

17 A watan Janairu na shekara ta 1900, Hasumiyar Tsaro ta ba da wani kashedi ga dukan waɗanda har ila sunayensu na rubuce a rajistar coci-cocin Kiristendam, amma suna cewa: “Ai ni ina goyon bayan gaskiya, na daina zuwa coci.” An yi wannan tambayar a cikin talifin: “Shin hakan daidai ne a ce ƙafarka ɗaya tana Babila, ɗaya kuma tana waje? Shin wannan ne irin biyayya . . . da kuma ibadar da Allah ya ce a yi masa? A’a. Duk mutumin da yake coci ya yi alkawari da cocin sa’ad da ya soma tarayya da su, kuma dole ne ya yi biyayya da dukan abin da cocin ya faɗa har sai ya . . . sanar a fili cewa ya daina tarayya da su.” Da shigewar shekaru, wannan kashedin ya yi ƙarfi sosai. c Ya zama wajibi bayin Jehobah su daina duk wata harka da addinin ƙarya.

18. Me ya sa yake da muhimmanci mutane su fito daga Babila Babba?

18 Da ba a ci gaba da yin kashedi a kai a kai cewa a fito daga Babila Babba ba, shin da Kristi, sabon Sarkin da aka naɗa zai sami rukunin bayi shafaffu da suke shirye su yi masa hidima a duniya ne? A’a, domin Kiristocin suka daina harka da Babila su ne kawai suka cancanta su bauta wa Jehobah “cikin ruhu da cikin gaskiya.” (Yoh. 4:24) Shin mu ma mun ƙudura aniyar daina harka da addinin ƙarya a yau, kamar yadda waɗannan bayin Jehobah suka yi? Bari mu ci ga da yin biyayya da wannan umurnin: “Ku fito daga cikinta, ya al’ummata.”—Karanta Ru’ya ta Yohanna 18:4.

Yin Taro don Ibada

19, 20. Ta yaya Hasumiyar Tsaro ta ƙarfafa bayin Allah su yi taro don yin ibada?

19 Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun koyar da cewa ya dace ’yan’uwa Kiristoci su haɗu su yi ibada tare, idan hakan ya yiwu a inda suke. Barin addinin ƙarya ba shi ne ake bukata kawai daga Kiristoci na gaskiya ba. Zai dace su riƙa yin ibada ta gaskiya. Tun farko, mujallar Hasumiyar Tsaro ta ƙarfafa masu karantata su riƙa taro don yin ibada. Alal misali, a watan Yuli na shekara ta 1880, Ɗan’uwa Russell ya ba da rahoto game da jawaban da ya yi sa’ad da ya yi wata tafiya. Ya ce taron da ya yi a wuraren da ya je sun kasance da ban ƙarfafa sosai. Ƙari ga haka, ya ƙarfafa masu karatu su aiko da rahotanni game da ci gaban da suka samu kuma a wallafa wasu a cikin mujallar Hasumiyar Tsaro. Me ya sa? “Don dukanmu mu san . . . yadda Ubangiji yake muku albarka; ko har ila kuna ci gaba da yin taro da sauran ’yan’uwa da suka amince da koyarwar gaskiya.”

Ɗan’uwa Charles Russell tare da wani rukunin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki a birnin Copenhagen, a ƙasar Denmark a 1909

20 A shekara ta 1882, an wallafa wani talifi a cikin Hasumiyar Tsaro mai jigo “Assembling Together” (Yin Taro). Talifin ya umurci Kiristoci su riƙa yin taro “don su ƙarfafa juna.” Ya ƙara da cewa: “Kasancewa da ilimi ko wata baiwa ba shi ne yake da muhimmanci ba. Bari kowa ya zo da Littafi Mai Tsarki da takarda da fensir da littattafan bincike, . . . da makamantansu. Ku zaɓi batun da kuke so; sai ku roƙi Allah ya ba ku ruhu mai tsarki don ku fahimci batun. Idan kun yi karatu, ku yi tunani a kan abin da kuka karanta kuma ku gwada nassi da nassi, yin hakan zai sa ku fahimci gaskiya.”

21. Wace misali ce ikilisiyar da ke Allegheny, Pennsylvania, ta ƙafa game da halartan taro da kuma ƙarfafa juna?

21 Hedkwatar Ɗaliban Littafi Mai Tsarki tana Allegheny, Pennsylvania, a ƙasar Amirka a lokacin. Sun kafa misali mai kyau na yin taro daidai da umurnin da ke littafin Ibraniyawa 10:24, 25. (Karanta.) Wani ɗan’uwa tsoho mai suna Charles Capen ya tuna yadda yake halartan irin waɗannan taron sa’ad da yake yaro. Ya ce: “Har ila, ban manta da nassin da aka rubuta a bangon majami’ar taro ba. Nassin ya ce, ‘Malaminku ɗaya ne, wato Kristi, ku duka kuwa ’yan’uwa ne.’ Ba na mantawa da wannan nassin da ke nuna cewa babu limamai a cikin ƙungiyar Jehobah.” (Mat. 23:8) Ɗan’uwa Capen ya tuna yadda suke jin daɗin taron, da ƙarfafawar da suke samu da kuma ƙwazon da Ɗan’uwa Russell ya nuna wajen ƙarfafa kowa a cikin ikilisiyar.

22. Mene ne mutane masu aminci suka yi sa’ad da aka ƙarfafa su su riƙa halartan taro, kuma wane darasi ne za mu iya koya?

22 Mutane masu aminci sun bi wannan misalin da kuma shawarar da aka ba su. An kafa ikilisiyoyi a wasu wurare kamar su Ohio da Michigan, kuma daga baya, a dukan nahiyar Amirka ta Arewa da kuma wasu ƙasashe. Ka yi la’akari: Shin kana ganin mutane masu aminci za su yi shiri don bayyanuwar Kristi ne in da ba a koya musu yadda za su bi wannan hurarren umurni na yin taro don ibada ba? Da kyar! Mu kuma fa a yau? Ya kamata mu ƙuduri anniyar halartan taron Kirista babu fashi, kuma mu riƙa amfani da kowane zarafi mu yi ibada tare kuma mu ƙarfafa juna don dukanmu mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah.

Yin Wa’azi da Ƙwazo

23. Ta yaya Hasumiyar Tsaro ta bayyana cewa wajibi ne dukan shafaffu su yi wa’azi?

23 Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun koyar cewa ya kamata dukan shafaffu su yi wa’azi game da gaskiyar Kalmar Allah. A shekara ta 1885, mujallar Hasumiyar Tsaro ta ce: “Kada mu manta cewa ya kamata dukan shafaffu su yi wa’azi (Isha. 61:1), domin an shafe su ne don yin wa’azi.” Wani talifin Hasumiyar Tsaro ta 1888 ya ce: “Umurninmu a bayyane yake . . . Idan muka ƙi yin wannan aikin kuma muka ba da hujja, hakan zai nuna cewa mu ragwayen bayi ne kuma ba za mu cancanci kasancewa shafaffu ba.”

24, 25. (a) Ban da yin wa’azi mene ne Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa suka ƙarfafa mutane su yi? (b) Ta yaya wani majagaba ya kwatanta aikinsa a zamanin da babu motoci sosai?

24 Ɗan’uwa Russell da abokan aikinsa sun nuna ƙwazo sosai wajen ƙarfafa mutane su yi wa’azi. Sun kuma soma wallafa wasu warƙoƙi da ake kira Bible Students’ Tracts, waɗanda daga baya aka kira Old Theology Quarterly. Masu karanta Hasumiyar Tsaro sun karɓi waɗannan warƙoƙin don su riƙa rarraba wa mutane kyauta.

Ya kamata mu tambayi kanmu, ‘Ina sa yin wa’azi kan gaba a rayuwata kuwa?’

25 Majagaba ne ake kiran waɗanda suke wa’azi na cikakken lokaci. Ɗan’uwa Charles Capen da aka ambata ɗazun yana cikinsu kuma ya ce: “Na yi amfani da taswirorin da United States Government Geological Survey (Hukumar Duba Yanayi na Ƙasar Amirka) ta tanadar don in san inda ya kamata in yi wa’azi a yankin Pennsylvania. Waɗannan taswirorin sun nuna dukan hanyoyi, kuma hakan ya taimaka mana mu yi wa’azi kuma mu kammala kowace ƙaramar hukuma da kafa. A wasu lokuta bayan na yi tafiya na kwana uku a ƙauyukan ina karɓan odar littattafan Studies in the Scriptures (Nazarin Nassosi), sai in ɗauki hayar karusa don in rarraba littattafan ga waɗanda suka yi oda. Nakan sauka kuma in kwana tare da manoma. Domin a lokacin babu motoci sosai.”

Wani majagaba. Duba “Chart of the Ages” da aka rubuta a jikin karusar

26. (a) Me ya sa bayin Allah suke bukata su fita wa’azi don su kasance a shirye domin sarautar Kristi? (b) Waɗanne tambayoyi ne suka dace mu yi kanmu?

26 Yin wa’azi a wannan lokacin ya bukaci gaba gaɗi da kuma ƙwazo. Da a ce ba a koya wa Kiristoci na gaskiya muhimmancin yin wa’azi ba, da sun kasance a shirye don sarautar Kristi ne? A’a! Ballantana ma, wannan wa’azi aiki ne da ke da muhimmanci sosai a lokacin bayyanuwar Kristi. (Mat. 24:14) Bayin Allah suna bukatar su kasance a shirye don su saka wannan aikin cetar da rai abu na farko a rayuwarsu. Ya kamata mu tambayi kanmu: ‘Ina sa yin wa’azi kan gaba a rayuwata kuwa? Ina yin sadaukarwa don in samu in fita wa’azi sosai kuwa?’

An Kafa Mulkin Allah!

27, 28. Mene ne Yohanna ya gani a wahayi kuma mene ne Shaiɗan da aljannunsa suka yi sa’ad da aka kafa Mulkin?

27 A ƙarshe, shekara mai muhimmanci ta 1914 ta cika. Kamar yadda muka tattauna a farkon wannan babin, babu wanda ya ga abubuwa masu ban al’ajabi da suka faru a sama. Amma, an saukar wa manzo Yohanna wahayin da ya bayyana waɗannan abubuwan a alamance. Ka yi tunanin abin da ya faru: Yohanna ya shaida “wata alama mai-girma” a sama. An kwatanta ƙungiyar Allah da ke sama da ta ƙunshi mala’iku da wata “mace” wadda ta ɗauki ciki kuma ta haifi ɗa namiji. Wannan ɗa na alama ba da daɗewa ba zai “mallaki dukan al’ummai da sanda ta ƙarfe.” Sa’ad da aka haife shi sai aka fizge ‘ɗan, aka kai shi wurin Allah, har ga kursiyinsa.’ Sai aka ji wata babbar murya daga sama ta ce: “Yanzu ceto, da iko, da mulkin Allahnmu ya zo, da sarautar Kristinsa kuma.”—R. Yoh. 12:1, 5, 10.

28 Babu shakka, manzo Yohanna ya ga sa’ad da aka kafa Mulkin Almasihu a wahayi. Lallai hakan abu ne mai ban al’ajabi, amma ba kowa ba ne ya ji daɗin abin da ya faru. Shaiɗan da aljanunsa sun yi yaƙi da mala’iku waɗanda suke ƙarƙashin ja-gorancin Mika’ilu, ko kuma Kristi. Mene ne sakamakon? Ayar ta ce: “Aka jefar da babban maciji, wato tsohon macijin nan, shi wanda ana ce da shi Iblis da Shaiɗan, mai-ruɗin dukan duniya; aka jefar da shi a duniya, aka jefar da mala’ikunsa kuma tare da shi.”—R. Yoh. 12:7, 9.

A shekara ta 1914 ne Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka soma fahimtar alamar bayyanuwar Kristi da ba a iya gani da ido ba

29, 30. Bayan da Yesu ya soma sarauta, ta yaya yanayi ya canja a (a) duniya? (b) sama?

29 Shekaru da yawa kafin 1914, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun ce lokacin shan wuya zai soma ne a wannan shekarar. Amma ba su san cewa abin da suka faɗa zai cika fiye da yadda suke tsammani ba. Kamar yadda wahayin Yohanna ya nuna, Shaiɗan zai soma yin tasiri a al’ummar ’yan Adam sosai. Wahayin ya ce: “Kaiton duniya da teku: Domin Shaiɗan ya sauko wajenku, hasala mai-girma kuwa gare shi, domin ya san sauran zarafinsa kaɗan ya rage.” (R. Yoh. 12:12) A shekara ta 1914, yaƙin duniya na ɗaya ya ɓarke kuma an soma ganin cikar annabcin bayyanuwar Kristi a matsayin Sarki a faɗin duniya. A wannan lokacin ne “kwanaki na ƙarshe” na wannan zamanin suka soma.—2 Tim. 3:1.

30 Amma, an yi farin ciki a sama. An kori Shaiɗan da aljanunsa kwatakwata daga sama. Ru’ya ta Yohanna ta ce: “Domin wannan fa, ku yi farin ciki, ya sammai, da ku mazauna a ciki.” (R. Yoh. 12:12) Tun da an riga an tsabtacce sammai kuma an naɗa Yesu Sarki, hakan ya sa Mulkin Almasihu ya yi shirin ɗaukan mataki a madadin bayin Allah a duniya. Wane mataki ne zai ɗauka? Kamar yadda muka tattauna a farkon wannan babin, abin da Kristi ya soma yi wa bayin Allah a duniya gyara. Wannan shi ne abin da ya soma yi a matsayin “mala’ikan alkawari.” Mene ne hakan yake nufi?

Lokacin Gwaji

31. Mene ne Malachi ya annabta game da lokacin gyara, kuma ta yaya wannan annabcin ya soma cika? (Ka kuma duba ƙarin bayani.)

31 Annabcin Malakai ya nuna cewa gyarar ba za ta kasance da sauƙi ba. Ya ce: ‘Amma wane ne za ya daure da ranar zuwansa? Wane ne kuwa za ya tsaya idan ya bayyana? Gama yana kama da wutar mai-gyaran ƙarfe, kamar sabulun mai-gyaran tufa.’ (Mal. 3:2) Waɗannan kalmomin sun tabbata! Daga shekara ta 1914, bayin Allah a duniya sun fuskanci gwaji da wahala iri-iri masu tsananin gaske. Da Yaƙin Duniya na Ɗaya ya ɓarke, Ɗaliban Littafi Mai Tsarki da yawa sun fuskanci tsanantawa sosai kuma an jefa su cikin kurkuku. d

32. Wace matsala ce bayin Allah suka fuskanta a shekara ta 1916?

32 Har ila, an sami matsala a cikin ƙungiyar. Ɗan’uwa Russell ya rasu a shekara ta 1916, yana da shekara 64, kuma rasuwarsa ta gigita bayin Allah da yawa. Mutuwarsa ta bayyana cewa wasu daga cikin mutanen suna girmama shi fiye da yadda ya kamata. Ko da yake Ɗan’uwa Russell ba ya son irin wannan ɗaukakar, amma mutanen tamkar dai suna bauta masa ne a zukatansu. Wasu sun ɗauka cewa mutuwarsa za ta kawo ƙarshen ƙarin hasken da ake samu game da gaskiyar Littafi Mai Tsarki, kuma saboda ɓacin rai, wasu sun yi ƙoƙarin hana ci gaban aikin. Wannan halin ne ya haifar da ’yan ridda da suka raba kan ƙungiyar.

33. Ta yaya abubuwan da ake tsammani za su faru amma ba su faru ba suka gwada bayin Allah?

33 Wani gwajin kuma shi ne wasu abubuwan da ake tsammanin za su faru ba su faru ba. Ko da yake mujallar Hasumiyar Tsaro ta nuna cewa Lokatan Al’ummai za su cika a shekara ta 1914, ’yan’uwa ba su fahimci abin da zai faru a shekarar ba. (Luk 21:24) Sun yi tsammanin cewa a wannan shekarar ce Kristi zai kai shafaffunsa sama don su yi sarauta tare. Amma hakan bai faru ba. A ƙarshen shekara ta 1917, Hasumiyar Tsaro ta sanar cewa girbin da aka soma shekaru arba’in da suka shige zai ƙare a farkon shekara ta 1918. Amma an ci gaba da yin wa’azi sosai har bayan wannan lokacin. Mujallar ta ce an gama girbin amma ba a gama kala ba. Duk da haka, mutane da yawa sun daina bauta wa Jehobah saboda taƙaici.

34. Wane gwaji ma tsanani ne ya auku a shekara ta 1918, kuma me ya sa Kiristendam suka yi tsammanin cewa bayin Allah ba za su ci gaba da aikinsu ba?

34 Wani gwaji mai tsanani ya auku a shekara ta 1918. Ɗan’uwa Joseph Franklin Rutherford shi ne ya gāji Ɗan’uwa Charles Taze Russell wajen yi wa bayin Allah ja-gora. Kuma an kama shi da kuma wasu ’yan’uwa guda bakwai da suke taimaka masa. An yi musu shari’ar rashin adalci kuma aka yanke musu hukuncin ɗauri na shekaru da yawa a kurkukun gwamnati da ke Atlanta, Georgia, na ƙasar Amirka. A lokacin, kamar dai aikin bayin Allah ya tsaya ne cak. Limaman coci-cocin Kiristendam da yawa sun yi farin ciki. Sun ɗauka cewa tun da an ɗaure “shugabannin,” an rufe hedkwatar da ke Brooklyn, kuma ana yunkurin hana yin wa’azi a Amirka da kuma Turai, ba za a sake ganin Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suna damun mutane da wa’azinsu ba. (R. Yoh. 11:3, 7-10) Amma hakan ƙarya ne!

Lokacin Farfaɗowa!

35. Me ya sa Yesu ya ƙyale mabiyansa su fuskanci mawuyacin yanayi, kuma wane mataki ne ya ɗauka don ya taimaka musu?

35 Waɗanda suke gāba da bayin Allah ba su san cewa Yesu ne ya ƙyale mabiyansa su fuskanci wannan mawuyacin halin ba. Hakan ya faru ne don Jehobah yana yin aikinsa na ‘mai-gyaran azurfa mai-tsarkake ta.’ (Mal. 3:3) Jehobah da Ɗansa suna da tabbaci cewa wannan gwajin zai gyara bayin Allah masu aminci kuma ya tsarkake su don su cancanci yi wa Sarkin hidima fiye da dā. Daga farkon shekara ta 1919, a bayyane yake cewa ruhun Allah ya yi abin da magabtan bayin Allah suka ɗauka cewa ba zai yiwu ba. Mutanensa masu aminci sun farfaɗo! (R. Yoh. 11:11) A lokacin ne Kristi ya cika wani babban annabci game da kwanaki na ƙarshe. Ya naɗa “bawan nan mai-aminci, mai-hikima,” wato, wani ƙaramin rukunin ’yan’uwa maza shafaffu waɗanda za su riƙa yi wa mutanensa ja-gora ta wurin yi musu tanadin koyarwar Littafi Mai Tsarki a kan kari.—Mat. 24:45-47.

36. Me ya nuna cewa bayin Allah sun soma farfaɗowa a ibadarsu?

36 An sake Ɗan’uwa Rutherford da abokan aikinsa daga kurkuku a ranar 26 ga Maris, 1919. Nan da nan aka shirya wani babban taron da za a yi a watan Satumba na shekarar. Kuma an soma yin shiri don wallafa mujalla ta biyu da za a kira The Golden Age. An tsara wannan mujallar da ake wallafawa tare da Hasumiyar Tsaro don yin wa’azi. e A wannan shekarar ce kuma aka wallafa fitowa ta farko ta Bulletin, wadda yanzu muke kira Hidimarmu ta Mulki. Tun da aka soma wallafa ta, tana tanadar da bayanai game da yadda za mu yi wa’azi. Babu shakka, tun daga shekarar 1919, an fi mai da hankali ga yin wa’azi gida-gida.

37. Ta yaya wasu suka nuna rashin aminci bayan shekara ta 1919?

37 Wa’azin da ake yi ya ci gaba da gyara bayin Kristi, amma masu fahariya da kuma masu taurin kai da ke cikinsu sun ƙi yin wannan aikin. Waɗannan mutanen da suka ƙi yin wannan aikin sun daina tarayya da bayin Allah masu aminci. A ’yan shekaru bayan 1919, wasu mutane marasa aminci sun yi fushi kuma suka soma tsegumi da ɓatanci, har ma suka soma goyon bayan masu tsananta wa amintattun bayin Jehobah.

38. Mene ne nasarar da mabiyan Kristi suka samu ya tabbatar mana?

38 Duk da waɗannan farmakin, mabiyan Kristi da ke duniya sun ci gaba da bunƙasa da kuma ƙarfafa dangantakarsu da Allah. Dukan nasarorin da suka samu tun daga wannan lokacin ya tabbatar da mu cewa Mulkin Allah yana sarauta! Waɗannan rukunin mutane ajizai sun ci gaba da yin nasara a kan Shaiɗan da kuma wannan muguwar zamanin ne don taimako da kuma albarka da Allah ya tanadar ta hanyar Ɗansa da Mulkinsa!—Karanta Ishaya 54:17.

Ɗan’uwa Rutherford ya ba da wani jawabi mai ƙayatarwa a wani taron gunduma bayan ’yan watanni da sakinsa daga fursuna

39, 40. (a) Ka ambata wasu fassalolin wannan littafin? (b) Ta ya ya za ka amfana daga yin nazarin wannan littafin?

39 A babobi na gaba, za mu tattauna abin da Mulkin Allah ya cim ma a nan duniya tun da aka kafa shi a sama. Kowane sashe na wannan littafin zai tattauna wani muhimmin fanni na aikin da Mulkin yake yi a nan duniya. Kowane babi yana da akwatin bita da zai taimaka wa kowannenmu ya san ko ya gaskata da Mulkin sosai. A babobi na ƙarshe, za mu tattauna abin da zai faru sa’ad da Mulkin ya halaka mugaye kuma ya mai da duniya aljanna. Ta yaya za ka amfana daga yin nazarin wannan littafin?

40 Shaiɗan yana so ka daina gaskatawa da Mulkin Allah. Amma Jehobah yana so ka kasance da bangaskiya sosai don hakan zai kāre ka kuma zai kyautata dangantakarka da shi. (Afis. 6:16) Saboda haka, muna ƙarfafa ka ka yi addu’a sosai a duk lokacin da za ka yi nazarin wannan littafin. Ka riƙa yi wa kanka wannan tambayar, ‘Shin na gaskata da Mulkin Allah kuwa?’ Idan ka gaskata da Mulkin Allah yanzu, za ka kasance da aminci da kuma ƙwazo wajen tallafa wa Mulkin har sai lokacin da kowa ya tabbata cewa Mulkin Allah yana sarauta da gaske!

a Don ƙarin bayani game da Grew, Stetson, da kuma Storrs, ka duba littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, shafuffuka na 45-46.

b Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun ga muhimmancin daina tarayya da addinan ƙarya, amma sun yi shekaru suna ɗaukan wasu mutane a matsayin ’yan’uwansu Kiristoci. Waɗannan mutanen ba sa cikinsu ko da yake suna da’awa cewa sun gaskata da fansar Kristi kuma sun keɓe kansu ga Allah.

c Wani abin da ya sa ba su ɗauki wannan kashedin da muhimmanci ba da farko shi ne, an ɗauka cewa ya shafi ƙaramin garken Kristi ne kaɗai wanda ya ƙunshi shafaffu 144,000. A Babi na 5,za mu ga cewa kafin shekara ta 1935, an ɗauka cewa “taro mai-girma” da aka ambata a Ru’ya ta Yohanna 7:9, 10, ya ƙunshi membobin coci-cocin Kiristendam; kuma za a ba su ladar zama rukuni na biyu da za su je sama domin sun goyi bayan Kristi a lokacin ƙarshe.

d A watan Satumba ta shekara ta 1920, an wallafa wata mujalla ta musamman mai suna The Golden Age (da yanzu muke kira Awake!) da ta yi bayani dalla-dalla a kan tsanantawa dabam-dabam, har da masu zafi sosai da aka yi wa ’yan’uwanmu a ƙasashe kamar su Kanada da Ingila da Jamus da kuma Amirka. Akasin haka, a shekarun da suka gabaci yaƙin duniya na ɗaya, ba a tsananta wa bayin Allah sosai ba.

e An yi shekaru da yawa ana wallafa Hasumiyar Tsaro don ilimantar da ƙaramin garken kawai.