BABI NA 1
‘Bari Mulkinka Ya Zo’
1, 2. Wane furucin Jehobah ne almajiran Yesu uku suka ji, kuma me suka yi?
MENE NE za ka yi idan Jehobah ya umurce ka ka yi wani abu? Babu shakka, za ka yi marmarin bin umurnin kome wuyarsa!
2 Abin da ya faru da manzannin Yesu uku ke nan, wato Bitrus da Yaƙub da kuma Yohanna jim kaɗan bayan Idin Ƙetarewa na shekara ta 32 a zamaninmu. (Karanta Matta 17:1-5.) Sa’ad da suke tare da Yesu, Ubangijinsu, a kan wani “dutse mai-tsawo,” sun ga wahayin inda yake sarauta a sama. Bitrus ya ga abin kamar da gaske ne har ya ce zai gina bukkoki guda uku a wurin. Yayin da Bitrus yake magana, sai gajimare ya rufe su. Bayan haka, Bitrus da Yaƙub da Yohanna suka ji wata murya da yawancin mutane ba su taɓa ji ba, wato muryar Jehobah. Bayan Jehobah ya tabbatar musu cewa Yesu Ɗansa ne, kai tsaye sai ya ce: “Ku ji [saurare, NW] shi.” Manzannin sun bi wannan umurnin. Ta yaya? Sun saurari koyarwar Yesu kuma sun ƙarfafa wasu su yi hakan.—A. M. 3:19-23; 4:18-20.
3. Me ya sa Jehobah yake so mu saurari Ɗansa, kuma wane batu ne ya dace mu bincika?
3 An rubuta waɗannan kalmomin: “Ku saurare shi” a cikin Littafi Mai Tsarki don mu amfana. (Rom. 15:4) Me ya sa? Domin Yesu kakakin Jehobah ne kuma a kowane lokaci yana koya wa mutane dukan abin da Ubansa yake so su sani. (Yoh. 1:1, 14) Da yake Yesu ya fi mai da hankali ga Mulkin Allah sa’ad da yake koyarwa, wato Mulkin da shi da abokan sarautarsa 144,000 za su yi, zai dace mu bincika wannan batun sosai. (R. Yoh. 5:9, 10; 14:1-3; 20:6) Da farko, bari mu bincika dalilin da ya sa Yesu ya fi mai da hankali ga Mulkin Allah.
“Daga Cikin Yalwar Zuciya . . .”
4. Ta yaya Yesu ya nuna cewa ya ɗauki Mulkin Allah da muhimmanci sosai?
4 Yesu ya ɗauki Mulkin da muhimmanci sosai. Me ya sa muka ce haka? Domin ana sanin abin da muka ɗauka da muhimmanci daga abubuwan da muke yawan magana a kai. Yesu ya ce: “Daga cikin yalwar zuciya baki ya kan yi magana.” (Mat. 12:34) Yesu ya yi amfani da dukan zarafi da yake da shi don ya gaya wa mutane game da Mulkin Allah. An ambaci Mulkin Allah fiye da sau ɗari a cikin Linjilar Matta da Markus da Luka da Yohanna kuma Yesu ne ya fi magana game da Mulkin. Mulkin ne jigon wa’azinsa, shi ya sa ya ce: “Dole in kai Bishara ta Mulkin Allah ga sauran birane kuma: gama saboda wannan aka aiko ni.” (Luk 4:43) Yesu ya ci gaba da tattauna game da Mulkin Allah da almajiransa bayan ya tashi daga mutuwa. (A. M. 1:3) Babu shakka, Yesu ya daraja Mulkin shi ya sa ya yi shelarsa sosai.
5-7. (a) Ta yaya muka san cewa Jehobah ya ɗauki Mulkin da muhimmanci sosai? Ka ba da kwatanci. (b) Ta yaya za mu nuna cewa Mulkin yana da muhimmanci a gare mu?
5 Jehobah da kansa ma ya ɗauki Mulkin da muhimmanci sosai. Me ya sa muka ce hakan? Jehobah ne ya aiko da Ɗansa tilo zuwa duniya, saboda haka, shi ne tushen dukan abin da Yesu ya koyar. (Yoh. 7:16; 12:49, 50) Ƙari ga haka, Jehobah ne ya hure Matta da Markus da Luka da kuma Yohanna su rubuta tarihin rayuwar Yesu da kuma hidimarsa. Ka yi tunanin abin da hakan yake nufi.
Ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Shin ina ɗaukan Mulkin da muhimmanci kuwa?’
6 A ce kana shirya hotunan iyalinka cikin albam. Kana da hotuna da yawa kuma albam ɗin ba zai iya ɗaukan dukan hotunan ba. Me za ka yi? Babu shakka, za ka zaɓi hotuna masu muhimmanci ne kawai ka saka a cikin albam ɗin. Hakazalika, Linjila huɗu da muka ambata ɗazu suna kama ne da albam ɗin hotuna domin suna ɗauke da bayanai masu muhimmanci game da Yesu. Ba dukan abin da Yesu ya ce da kuma yi sa’ad da yake duniya ba ne Jehobah ya hure Marubutan Linjila huɗun su rubuta. (Yoh. 20:30; 21:25) Maimakon haka, ruhu mai tsarki ya ja-gorance su su rubuta dukan abubuwan da za su taimaka mana mu fahimci manufar hidimar Yesu da kuma abin da ya fi muhimmanci ga Jehobah. (2 Tim. 3:16, 17; 2 Bit. 1:21) Tun da Linjila huɗun suna ɗauke da koyarwar Yesu game da Mulkin Allah, za mu iya cewa Jehobah ya ɗauki Mulkin da muhimmanci sosai. Babu shakka, Jehobah yana so mu san abubuwa game da Mulkin.
7 Ya kamata kowannenmu ya tambayi kansa, ‘Shin ina ɗaukan Mulkin da muhimmanci kuwa?’ Idan haka ne, za mu kasance a shirye mu saurari abubuwan da Yesu ya koyar game da Mulkin Allah da muhimmancinsa, da yadda Mulkin zai zo da kuma sa’ad da hakan zai faru.
Ta Yaya Mulkin Allah Zai Zo?
8. Ta yaya Yesu ya bayyana muhimmancin Mulkin?
8 Ka yi la’akari da addu’ar misali da Yesu ya koyar. Yesu ya yi amfani ne da kalmomi masu sauƙi don ya bayyana muhimmancin Mulkin da kuma abin da zai cim ma. Addu’ar tana ɗauke da roƙo guda bakwai. Na ɗaya zuwa uku game da nufin Jehobah ne, wato yadda za a tsarkake sunansa da zuwan Mulkinsa da kuma yin nufinsa a duniya kamar yadda ake yi a sama. (Karanta Matta 6:9, 10.) Waɗannan roƙo uku suna da nasaba da juna. Jehobah zai yi amfani da Mulkin Almasihu don ya tsarkake sunansa kuma ya cim ma nufinsa.
9, 10. (a) Ta yaya Mulkin Allah zai zo? (b) Wane alkawarin da ke cikin Littafi Mai Tsarki ne kake marmarin ganin cikarsa?
9 Ta yaya Mulkin Allah zai zo? Sa’ad da muka yi addu’a cewa ‘Bari Mulkinka ya zo,’ muna roƙo ne cewa Mulkin Allah ya ɗauki babban mataki kai tsaye. Sa’ad da Mulkin ya zo, zai zartar da ikonsa bisa duniya. Zai kawar da wannan mugun yanayin da duniya take ciki, haɗe da dukan mulkokin ’yan Adam kuma zai kawo sabuwar duniya mai salama. (Dan. 2:44; 2 Bit. 3:13) Mulkin Allah zai sa dukan duniya ta zama aljanna. (Luk 23:43) Allah zai ta da matattu kuma za su sake haɗuwa da ’yan’uwa da abokai. (Yoh. 5:28, 29) Mutane masu adalci za su zama kamiltattu, kuma ba za su sake mutuwa ba. (R. Yoh. 21:3-5) Bayan haka, duniya za ta zama wuri mai kyau kamar yadda sama yake kuma za a riƙa yin nufin Jehobah a cikinta! Babu shakka, kana marmarin ganin lokacin da Allah zai cika waɗannan alkawuran da ke cikin Littafi Mai Tsarki, ko ba haka ba? Ka tuna cewa a duk lokacin da ka yi addu’a cewa Mulkin Allah ya zo, kana roƙon Allah ne ya cika waɗannan alkawuransa masu tamani.
10 A bayyane yake cewa addu’ar da muke yi cewa Mulkin Allah ya “zo” bai cika a duniya ba tukun. Me ya sa muka ce hakan? Domin har ila, ’yan Adam suna sarauta kuma sabuwar duniya mai adalci ba ta zo ba tukun. Amma, albishirinku! Mulkin Allah ya riga ya soma sarauta kuma batun da za mu tattauna ke nan a babi na gaba. Yanzu, bari mu tattauna abin da Yesu ya ce game da lokacin da Mulkin zai soma sarauta a sama da kuma lokacin da zai soma sarauta bisa duniya.
Yaushe Ne Aka Kafa Mulkin Allah?
11. Mene ne Yesu ya nuna game da lokacin da za a kafa Mulkin Allah?
11 Yesu ya nuna cewa ba za a kafa Mulkin a ƙarni na farko ba, duk da cewa wasu almajiransa sun yi zaton hakan. (A. M. 1:6) Ka yi la’akari da abin da Yesu ya faɗa a kwatanci guda biyu waɗanda ya yi cikin shekaru biyu.
12. Ta yaya kwatancin alkama da zawan ya nuna cewa ba a kafa Mulkin Allah a ƙarni na farko ba?
12 Kwatancin alkama da zawan. (Karanta Matta 13:24-30.) Wataƙila a shekara ta 31 a zamaninmu, bayan Yesu ya ba da wannan kwatancin, ya bayyana ma’anarsa ga almajiransa. (Mat. 13:36-43) Ga kwatancin a taƙaice da kuma ma’anarsa: Bayan manzannin Yesu sun rasu, Iblis zai shuka zawan (jabun Kiristoci) a cikin alkama (“’ya’yan Mulki” ko kuma Kiristoci shafaffu). Za a bar alkamar da zawan su girma tare har lokacin kaka, wato “matuƙar zamani.” Za a cire zawan a lokacin kaka, kuma daga baya a tattara alkamar. Kwatancin ya nuna cewa ba za a kafa Mulkin a ƙarni na farko ba, amma sai bayan alkamar da zawan sun gama girma. Alkamar da zawan sun gama girma kuma an shiga lokacin kaka a shekara ta 1914.
13. Wane kwatancin Yesu ne ya nuna cewa ba zai soma sarauta da zarar ya koma sama ba?
13 Kwatancin fam goma. (Karanta Luka 19:11-13.) Yesu ya yi wannan kwatancin a shekara ta 33 a zamaninmu sa’ad da yake tafiya ta ƙarshe zuwa Urushalima. Wasu cikin mutanen da suka saurare shi sun ɗauka cewa zai kafa Mulkin da zarar sun isa Urushalima. Amma mene ne Yesu ya yi don ya bayyana musu cewa ba a lokacin ba ne zai kafa Mulkin? Ya kamanta kansa da “wani ba-sarauci” wanda ya yi tafiya zuwa “wata ƙasa mai-nisa garin ya samo mulki.” a Ƙasa mai nisa da Yesu ya ambata tana nufin sama, inda Ubansa zai naɗa shi Sarki. Amma Yesu ya san cewa ba za a naɗa shi Sarkin Mulkin nan da nan bayan ya koma sama ba. Maimakon haka, zai zauna a hannun dama na Allah ya jira har sai lokaci ya yi. Kamar yadda muka sani, Yesu ya yi shekaru da yawa yana jira.—Zab. 110:1, 2; Mat. 22:43, 44; Ibran. 10:12, 13.
Yaushe Ne Mulkin Allah Zai Zo?
14. (a) Yaya Yesu ya amsa tambayar da almajiransa huɗu suka yi masa? (b) Mene ne cikar annabcin Yesu ya nuna mana game da bayyanuwarsa da kuma Mulkin?
14 Kwanaki kaɗan kafin a kashe Yesu, manzanninsa huɗu sun yi masa wata tambaya. Sun ce: ‘Mene ne alamar zuwanka [bayyanuwarka, NW] da cikar zamani?’ (Mat. 24:3; Mar. ) Yesu ya amsa tambayar ta wajen yin annabcin da ke littafin 13:4Matta surori 24 da 25. Ya faɗi abubuwa dabam-dabam da za su faru a lokacin bayyanuwarsa. Bayyanuwarsa ta soma ne a lokacin da Mulkin ya fara sarauta kuma zai zo ƙarshe sa’ad da sarautar Mulkin ta kafu sosai bisa dukan duniya. Muna da tabbaci cewa annabcin Yesu ya soma cika tun shekara ta 1914. b Saboda haka, wannan shekarar ce farkon bayyanuwar Yesu da kuma lokacin da aka kafa Mulkin Allah.
15, 16. Su waye ne ‘wannan tsarar’ da aka ambata a Littafi Mai Tsarki?
15 Amma a yaushe ne Mulkin Allah zai zo? Yesu bai faɗi ainihin lokacin da hakan zai faru ba. (Mat. 24:36) Amma akwai abin da ya ce da ya tabbatar mana cewa lokacin ya kusa sosai. Yesu ya ce Mulkin zai zo bayan “wannan tsara” ta shaida cikar annabcin da ya yi. (Karanta Matta 24:32-34.) Su waye ne ake nufi da ‘wannan tsarar?’ Bari mu bincika abin da Yesu ya faɗa.
16 “Wannan tsara.” Shin Yesu yana nufin waɗanda ba sa bauta wa Allah ne? A’a. Ka yi la’akari da mutanen da yake wa magana. Yesu ya yi wannan annabcin ne a gaban manzanninsa ƙalila waɗanda “suka zo wurinsa” a keɓe. (Mat. 24:3) Za a shafe manzanninsa da ruhu mai tsarki ba da daɗewa ba. Ka kuma yi la’akari da batun da yake magana a kai. Kafin Yesu ya yi magana game da “wannan tsara,” ya ce: “Daga itacen ɓaure fa sai ku koyi misalinsa: sa’anda reshensa ya rigaya ya yi taushi, yana kuwa hudo da ganyaye, kun san bazara ta kusa; hakanan ku kuma, lokacin da kun ga waɗannan al’amura duka, ku sani ya yi kusa, har bakin ƙofa.” Mabiyan Yesu, shafaffu, ne za su ga cikar annabcin da ya yi kuma su ne za su fahimci ma’anarsa, wato, cewa zuwan Yesu “ya yi kusa, har bakin ƙofa,” ba mutanen da ba sa bauta wa Allah ba. Saboda haka, sa’ad da Yesu ya yi magana game da ‘wannan tsarar,’ yana nufin mabiyansa shafaffu.
17. Mene ne ma’anar kalaman nan “tsara” da kuma “waɗannan abubuwa duka”?
17 “Ba za ta shuɗe ba, sai an cika waɗannan abubuwa duka.” Ta yaya wannan furucin zai cika? Don mu amsa wannan tambayar, muna bukatar mu san abubuwa biyu: na farko, ma’anar “tsara” da kuma “waɗannan abubuwa duka.” A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “tsara” tana nuni ga mutane masu shekaru dabam-dabam da suka yi rayuwa a zamani ɗaya. Tsara ba ta cika daɗewa kuma tana ƙarewa. (Fit. 1:6) Furucin nan “waɗannan abubuwa duka” ya haɗa da dukan abubuwan da Yesu ya annabta cewa za su faru a lokacin bayyanuwarsa, wato daga farkon shekara ta 1914 har lokacin “ƙunci mai girma.”—Mat. 24:21.
18, 19. Yaya muka fahimci abin da Yesu ya faɗa game da “wannan tsara,” kuma mene ne za mu iya ce game da hakan?
18 Yaya za mu fahimci abin da Yesu ya ce game da “wannan tsara”? Tsarar ta ƙunshi rukuni biyu na shafaffu, na farko sune waɗanda suka shaida lokacin da alamar da Yesu ya yi maganarsa ta soma cika a shekara ta 1914. Na biyun su ne waɗanda aka shafe su a lokacin da rukuni na farkon suke raye. Wasu da ke cikin rukuni na biyun za su kasance a raye a lokacin ƙunci mai girma, wato ƙarshen wannan zamanin. c
19 Mene ne za mu iya cewa game da hakan? Mun san cewa alamar bayyanuwarsa ta shafi abubuwa a ko’ina a duniya, kuma shafaffun da ke cikin wannan tsarar suna tsufa, duk da haka, ba dukansu ne za su mutu ba kafin a soma ƙunci mai girma. Saboda haka, za mu iya cewa nan ba da daɗewa ba, Mulkin Allah zai zo kuma zai soma sarauta bisa duniya. Hakika, kasancewa a lokacin cikar addu’ar misali da Yesu ya yi cewa: ‘Bari mulkinka ya zo’ zai zama abin farin ciki sosai!
20. Wane batu mai muhimmanci ne za mu tattauna a wannan littafin kuma me za mu tattauna a babi na gaba?
20 Kada mu taɓa manta da furucin da Jehobah ya yi daga sama game da Ɗansa, sa’ad da ya ce: ‘Ku saurare shi.’ A matsayin Kiristoci na gaskiya, bari mu yi marmarin bin wannan umurnin da Allah ya bayar. Muna marmarin sanin dukan abubuwan da Yesu ya koyar game da mulkin Allah. Yana da muhimmanci mu bincika abin da wannan Mulkin ya riga ya cim ma da kuma abin da zai yi a nan gaba. Abin da wannan littafin ya ƙunsa ke nan. Babi na gaba zai tattauna abubuwa masu ban al’ajabi da suka faru sa’ad da aka kafa Mulkin Allah a sama.
a Kwatancin da Yesu ya yi wataƙila ya sa masu sauraronsa sun tuna da Akila’us, wani ɗan Hirudus Mai Girma. Kafin Hirudus ya mutu, ya zaɓi Akila’us a matsayin wanda zai gāji sarautarsa bisa Yahuda da kuma wasu yankuna. Amma, kafin Akila’us ya soma sarauta, ya yi tafiya mai nisa zuwa ƙasar Roma domin ya nemi izinin Kaisar Augustus.
b Don ƙarin bayani, ka duba babi na 9 na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
c Duk wanda aka shafe bayan mutuwar shafaffe na ƙarshe da ke rukuni na farko, wato, bayan waɗanda suka shaida “al’amura mafarin wahala” a shekara ta 1914, ba zai kasance cikin wannan “tsara” da aka ambata ba.—Mat. 24:8.