Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 9

Sakamakon Yin Wa’azi​—‘Gonaki Sun Nuna Sun Isa Girbi’

Sakamakon Yin Wa’azi​—‘Gonaki Sun Nuna Sun Isa Girbi’

MANUFAR WANNAN BABIN

Jehobah ya sa iri na saƙon Mulkin ya bunƙasa

1, 2. (a) Me ya sa almajiran Yesu suka rikice? (b) Wane irin girbi ne Yesu ya yi maganarsa?

 YESU ya gaya wa almajiransa cewa: “Ku tāda idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi.” Kalaman nan sun ɗan rikitar da almajiransa. Sun kalli filin da Yesu ya nuna musu, amma ba su ga gonar da ta isa girbi ba domin ba a daɗe da shuka sha’ir ba. Mai yiwuwa sun yi mamaki, ‘Wane girbi ke nan, tun da yake za a yi watanni kafin a soma girbin sha’ir?’—Yoh. 4:35.

2 Amma ba girbi na zahiri ne Yesu yake magana a kai ba. Maimakon haka, yana amfani da wannan damar ce don ya koya wa almajiransa muhimman darussa biyu game da girbi na alama, wato tattara mutane zuwa cikin ikilisiyar Kirista. Waɗanne darussa ke nan? Domin mu sami amsar wannan tambayar, bari mu tattauna labarin dalla-dalla.

Gayyata don Aiki da Ke Sa Farin Ciki

3. (a) Mene ne wataƙila ya sa Yesu ya ce: “Gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi”? (Ka duba ƙarin bayani.) (b) Ta yaya Yesu ya bayyana kalmominsa?

3 Yesu ya tattauna da almajiransa a ƙarshen shekara ta 30 a zamaninmu, a kusa da garin Samariyawa da ake kira Sukar. Sa’ad da almajiransa suka shiga cikin gari, Yesu ya zauna a bakin wata rijiya kuma ya yi ma wata mata wa’azi. Matar ta fahimci koyarwarsa nan da nan. Sa’ad da almajiran Yesu suka dawo, sai matar ta gaggauta zuwa garin Sukar don ta gaya wa maƙwabtanta abin al’ajabi da ta koya. A sakamakon haka, maƙwabtanta da yawa sun yi jerin gwano zuwa wurin Yesu. Wataƙila a lokacin ne Yesu ya kalli filin kuma ya hangi Samariyawa masu ɗimbin yawa suna zuwa wajensa, sai ya ce: “Ku tā da idanunku, ku duba gonaki, sun rigaya sun yi fari, sun isa girbi.” a Sai ya bayyana cewa ba girbi na zahiri yake magana a kai ba, amma na alama ne. Yesu ya ce: “Mai-girbi . . . yana kuwa tattara hatsi zuwa rai na har abada.”—Yoh. 4:5-30, 36.

4. (a) Waɗanne darussa biyu ne Yesu ya koyar game da girbin? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu bincika amsoshinsu?

4 Waɗanne muhimman darussa biyu ne Yesu ya koyar game da girbin? Na farko, aikin na gaggawa ne. Sa’ad da Yesu ya ce ‘gonaki sun . . . yi fari, sun isa girbi,’ yana so almajiransa su ɗauki mataki. Domin Yesu ya nanata wa almajiransa gaggawar zancen, sai ya ce: “Mai girbi na samun lada.” Hakika, an riga an soma girbin kuma bai kamata a ɓata lokaci ba! Na biyu, masu girbin suna farin ciki. Yesu ya ce masu shuki da masu girbi za su “yi farin ciki tare.” (Yoh. 4:35b, 36, Littafi Mai Tsarki) Kamar yadda Yesu ya yi farin ciki sa’ad da ya lura cewa ‘Samariyawa da yawa sun ba da gaskiya gare shi,’ hakan ma almajiransa za su yi farin ciki yayin da suke yin girbi da zuciya ɗaya. (Yoh. 4:39-42) Wannan abin da ya faru a ƙarni na farko yana da muhimmanci sosai a yau. Me ya sa? Domin yana nuna abin da ke faruwa a yau, yayin da ake yin girbi mafi girma a tarihi. A yaushe ne aka soma wannan girbin? Su waye ne suke yin girbin? Kuma wane sakamako ake samu?

Sarkinmu Yana Ja-gora a Aikin Girbi Mafi Muhimmanci a Tahiri

5. Waye ne yake ja-gorantar aikin girbin da ake yi a faɗin duniya, kuma ta yaya wahayin da aka saukar wa Yohanna ya nuna cewa aikin na gaggawa ne?

5 A wahayin da Jehobah ya saukar wa manzo Yohanna, ya nuna cewa ya danƙa wa Yesu hakkin yin ja-gora a wannan aikin girbin. (Karanta Ru’ya ta Yohanna 14:14-16.) A wannan wahayin, an nuna Yesu sanye da rawani kuma yana riƙe da lauje. Wannan “rawani na zinariya” da ke kan Yesu yana nuna cewa shi Sarki ne. “Lauje mai-ƙaifi” da ke hannunsa ya tabbatar da matsayinsa na Mai-girbi. Domin Jehobah ya yi amfani da mala’ika kuma ya ce “amfanin duniya ya” nuna sosai, Yana nanatawa ne cewa aikin na gaggawa ne. Hakika, ‘sa’ar girbi ta yi,’ kuma babu damar ɓata lokaci! Sa’ad da Allah ya gaya wa Yesu, “miƙa laujenka,” sai Yesu ya ja laujensa, kuma ya girbe duniya, wato, ya tattara mutane a duniya zuwa cikin ikilisiyar Kirista. Wannan wahayin ya tuna mana cewa ‘gonaki sun . . . yi fari, sun isa girbi.’ Shin wannan wahayin ya taimaka mana mu san lokacin da aka soma wannan girbin? Ƙwarai kuwa!

6. (a) A yaushe ne aka shiga “lokacin kaka”? (b) A yaushe ne aka soma girbe “amfanin duniya”? Ka bayyana.

6 Tun da wahayin da Yohanna ya gani da ke littafin Ru’ya ta Yohanna sura 14 ya nuna Yesu wanda shi ne Mai-girbin, sanye da rawani (aya ta 14), hakan ya nuna cewa ya riga ya soma Sarauta a shekara ta 1914. (Dan. 7:13, 14) Jim kaɗan bayan haka, an umurce Yesu ya soma girbi (aya ta 15). An kwatanta irin wannan aukuwar ma a kwatancin da Yesu ya ba da game da alkama. Ya ce: “Kaka kuma matuƙar zamani ce.” Saboda haka, lokacin kaka da kuma matuƙar zamani sun fara ne a lokaci guda, wato a shekara ta 1914. Daga baya ne aka fara ainihin girbin a “lokacin kaka.” (Mat. 13:30, 39) Idan muka lura sosai, za mu ga cewa an soma girbin ne ’yan shekaru bayan Yesu ya soma Sarauta. Da farko, daga shekara ta 1914 zuwa farkon 1919, Yesu ya tsarkake mabiyansa shafaffu. (Mal. 3:1-3; 1 Bit. 4:17) Bayan haka, sai aka soma girbe “amfanin duniya” a shekara ta 1919. Nan da nan, Yesu ya yi amfani da wannan sabon bawan da ba a daɗe da naɗawa ba wajen taimaka wa ’yan’uwanmu su fahimci cewa wa’azi aiki ne na gaggawa. Ka yi la’akari da abin da ya faru.

7. (a) Wane nazari ne ya taimaka wa ’yan’uwanmu su san cewa wa’azi aiki ne na gaggawa? (b) Mene ne aka ƙarfafa ’yan’uwanmu su yi?

7 Hasumiyar Tsaro ta Yuli, 1920, ta ce: “Babu shakka, nazarin Littafi Mai Tsarki da muka yi ya nuna cewa an danƙa wa Kiristoci babban gata na yaɗa saƙon mulkin.” Alal misali, annabcin Ishaya ya taimaka wa ’yan’uwan su ga cewa wajibi ne a yaɗa bisharar Mulkin a dukan duniya. (Isha. 49:6; 52:7; 61:1-3) Ba su san yadda za su yi wannan aikin ba, amma sun yi imani cewa Jehobah zai ba su damar yin hakan. (Karanta Ishaya 59:1.) Da yake ’yan’uwanmu sun ga cewa wa’azi aiki ne na gaggawa, hakan ya ƙarfafa su su yi wa’azi da ƙwazo. Wane mataki ne suka ɗauka?

8. Waɗanne abubuwa biyu game da wa’azi ne ’yan’uwa suka fahimta a shekara ta 1921?

8 Hasumiyar Tsaro ta Disamba, 1921, ta ce: “Babu shekarar da ta fi wannan kyau kuma mutane da yawa sun ji saƙon Mulkin a shekara ta 1921 fiye da shekarun da suka gabata.” Mujallar ta ci gaba da cewa: “Amma, tsugune ba ta ƙare ba tukun. . . . Bari mu yi hakan da farin ciki sosai.” Ka lura da yadda ’yan’uwa suka fahimci waɗannan abubuwa biyu masu muhimmanci da Yesu ya koya wa almajiransa game da wa’azi: Aikin na gaggawa ne kuma masu girbin suna farin ciki.

9. (a) Mene ne Hasumiyar Tsaro ta ce game da aikin girbi a shekara ta 1954, kuma me ya sa? (b) Wace ƙaruwa ce aka samu a adadin masu shela a cikin shekaru 50 da suka shige? (Ka duba jadawalin nan “ Ƙaruwa a Faɗin Duniya.”)

9 A tsakanin shekara ta 1930 zuwa 1939, ’yan’uwa sun fahimci cewa waɗanda za su kasance cikin taro mai girma za su saurari saƙon Mulkin, kuma hakan ya sa sun yi wa’azi da ƙwazo sosai. (Isha. 55:5; Yoh. 10:16; R. Yoh. 7:9) Wane sakamako aka samu? An sami ƙaruwa a yawan masu wa’azin Mulki, daga 41,000 a shekara ta 1934 zuwa 500,000 a shekara ta 1953! Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Disamba, 1954, ta ce: “Ruhun Jehobah da kuma ikon Kalmarsa ne suka sa aka cim ma wannan gagarumin aikin girbin da ake yi a faɗin duniya.” bZak. 4:6.

ƘARUWA A FAƊIN DUNIYA

 Kasa

1962

1987

2013

Ostareliya

15,927

46,170

66,023

Brazil

26,390

216,216

756,455

Faransa

18,452

96,954

124,029

Italiya

6,929

149,870

247,251

Japan

2,491

120,722

217,154

Meziko

27,054

222,168

772,628

Nijeriya

33,956

133,899

344,342

Filifin

36,829

101,735

181,236

Amirka

289,135

780,676

1,203,642

Zambiya

30,129

67,144

162,370

ƘARUWAR ADADIN NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI

 1950

234,952

1960

646,108

1970

1,146,378

1980

1,371,584

1990

3,624,091

2000

4,766,631

2010

8,058,359

An Yi Amfani da Kwatanci Wajen Annabta Sakamakon Girbin

10, 11. Waɗanne fasalolin girma ne aka bayyana a kwatancin ƙwayar mustard?

10 A kwatancin da Yesu ya bayar game da Mulkin, ya annabta sakamakon aikin girbin. Bari mu tattauna kwatancin da Yesu ya yi game da ƙwayar mustard da kuma yis. Za mu mai da hankali ne musamman a kan yadda suka cika a kwanaki na ƙarshe.

11 Kwatancin ƙwayar mustard. Wani mutum ya shuka ƙwayar mustard. Sai ƙwayar ta tsira, ta yi girma kuma ta zama bishiya, inda tsuntsaye suke fakewa. (Karanta Matta 13:31, 32.) Waɗanne fasalolin girma ta ƙwayar ce Yesu ya nanata a wannan kwatancin? (1) Yadda ƙwayar ta yi girma yana da ban mamaki. Ƙwayar “da ta fi kowane irin da ke cikin ƙasa ƙanƙanta” ta zama bishiya mai “rassa masu-girma.” (Mar. 4:31, 32) (2) Tabbas, za ta yi girma. ‘Sa’an da aka shuka [irin] tana girma.’ Yesu bai ce, “Wataƙila za ta yi girma ba,” amma ya ce: Tana “girma.” Babu abin da ya isa ya hana ta girma. (3) Yayin da bishiyar take girma, tana jawo hankalin baƙi kuma suna samun mafaka a ƙarƙashinta. ‘Tsuntsayen sama suna sauka ƙarƙashin inuwarta.’ Ta yaya waɗannan fasaloli uku suka shafi aikin girbi da muke yi a yau?

12. Wace nasaba ce ke tsakanin kwatancin ƙwayar mustard da kuma aikin girbi a yau? (Ka kuma duba akwatin nan “ Ƙaruwar Adadin Nazarin Littafi Mai Tsarki.”)

12 (1) Girma: Kwatancin ya nuna yadda saƙon Mulkin da kuma ikilisiyar Kirista suka yaɗu sosai. An soma tattara masu girbi da ke da ƙwazo sosai zuwa cikin ikilisiyar Kirista tun daga shekara ta 1919. A lokacin, masu girbin ba su da yawa, amma adadinsu ya ƙaru nan da nan. Hakika, ƙaruwar da aka samu daga farkon shekara ta 1900 zuwa yau ba kaɗan ba ne. (Isha. 60:22) (2) Tabbaci: Babu abin da ya hana ikilisiyar Kirista samun ƙaruwa. Duk da yawan matsin da ƙaramar ƙwayar nan ta fuskanta daga maƙiyan Allah, ta ci gaba da yin girma tana haɓaka. (Isha. 54:17) (3) Wurin Sauka: “Tsuntsayen sama” da suka sauka a itacen suna wakiltar miliyoyin mutane daga ƙasashe wajen 240 da suka saurari saƙon Mulkin kuma suka shiga ƙungiyar Jehobah. (Ezek. 17:23) A nan ne suke samun koyarwar Allah da shaƙatawa da kuma kāriya.—Isha. 32:1, 2; 54:13.

Kwatancin ƙwayar mustard ya nuna cewa ’yan’uwan da ke cikin ƙungiyar Jehobah suna samun wurin fakewa da kuma kāriya (Ka duba sakin layi na 11, 12)

13. Waɗanne fasalolin girma ne aka bayyana a kwatancin yis?

13 Kwatancin Yis. Bayan wata mata ta zuba yis cikin garin fulawa, sai yis ɗin ya game garin. (Karanta Matta 13:33.) Waɗanne fasalolin girma ne aka bayyana a wannan kwatancin? Bari mu tattauna biyu cikinsu. (1) Girman ya kawo sauyi. Yis ɗin ya yaɗu har “ya game” dukan garin fulawar. (2) Girman ko kuma yaɗuwar ta game ko’ina. Yis ɗin ya game “mudu uku na gari.” Ta yaya waɗannan fasaloli biyu suka shafi aikin girbin da muke yi a yau?

14. Wace nasaba ce ke tsakanin kwatancin yis da kuma aikin girbin da muke yi a yau?

14 (1) Sauyi: Yis ɗin yana wakiltar saƙon Mulkin kuma garin fulawar yana wakiltar ’yan Adam. Kamar yadda yis yake canja garin fulawa sa’ad da aka kwaɓa su tare, haka saƙon Mulkin yake sauya ko kuma canja zukatan mutane bayan sun karɓi saƙon. (Rom. 12:2) (2) Zai game ko’ina: Yadda yis ɗin ya yaɗu har ya game dukan garin fulawar yana kwatanta yadda saƙon Mulkin yake yaɗuwa. Kamar yadda yis yake bin cikin fulawar da aka kwaɓa har ya game ta baki ɗaya, haka ma saƙon Mulkin ya yaɗu ‘har iyakan duniya.’ (A. M. 1:8) Wannan sashen kwatancin ya nuna cewa ko da yake mutane ba sa ganin mu muna wa’azi a ƙasashen da aka sa wa aikinmu takunkumi, duk da haka, saƙon Mulkin zai yaɗu.

15. Ta yaya kalmomin Ishaya 60:5, 22 suke cika? (Ka kuma duba akwatunan nan “ Jehobah Ya Sa Ya Yiwu,” shafi na 93, da kuma “ Yadda ‘Ƙanƙani’ Ya Zama “Al’umma” Mai Girma,” shafuffuka na 96-97.)

15 Shekaru 800 kafin Yesu ya yi waɗannan kwatancin, Jehobah ya yi annabci ta bakin Ishaya game da abubuwan da za a cim ma a aikin girbin nan da kuma farin cikin da hakan zai kawo. c Jehobah ya kwatanta yadda mutane “daga nesa” suke jerin gwano zuwa ƙungiyarsa. Sai ya mai da hankalinsa ga wata ‘mace,’ wadda take wakiltar shafaffun da suka rage a duniya, kuma ya ce: “Za ki gani ki sami haske, zuciyarki kuma ta motsu ta buɗe; domin albarkar teku za ta juya ta nufa wajenki, wadatar al’ummai kuma za ta zo gareki.” (Isha. 60:1, 4, 5, 9) Babu shakka, waɗannan kalmomin suna cika! Bayin Jehobah da suka daɗe suna bauta masa a yau, suna farin ciki domin suna ganin yadda masu shela suke ƙaruwa a ƙasashensu.

Dalilin da Ya Sa Dukan Bayin Jehobah Suke Farin Ciki

16, 17. Wane dalili ne ya sa ‘mai-shuka da mai-girbi suka yi farin ciki tare’? (Ka kuma duba akwatin nan “ Yadda Warƙoƙi Biyu Suka Ratsa Zukatan Mutane Biyu a Yankin Amazon.”)

16 Za ka iya tuna cewa Yesu ya gaya wa manzanninsa: “Mai-girbi . . . yana kuwa tattara hatsi zuwa rai na har abada; domin mai-shuka da mai-girbi su yi farin ciki tare.” (Yoh. 4:36) Ta yaya muke ‘farin ciki tare’ a wannan aikin girbin da ake yi a dukan duniya? Muna yin haka a hanyoyi da yawa. Bari mu tattauna uku daga cikinsu.

17 Na farko, muna farin cikin ganin hannun Jehobah a wannan aikin. Muna shuka iri a duk sa’ad da muka yi wa’azin Mulkin. (Mat. 13:18, 19) Muna girbe amfani a duk lokacin da muka taimaka ma wani ya zama mabiyin Kristi. Kuma mu duka muna matuƙar farin ciki sa’ad da muka ga yadda Jehobah yake sa irin “ya tsira” kuma “ya yi girma.” (Mar. 4:27, 28) Wasu daga cikin irin da muka shuka suna yin tsiro daga baya, kuma wasu su girbe su. Wataƙila ka taɓa shaida irin abin da ya faru da wata ’yar’uwa a Biritaniya mai suna Joan wadda ta yi baftisma shekaru 60 da suka wuce. Ta ce: “Na haɗu da mutane da yawa da suka gaya mini cewa na shuka irin gaskiya a zuciyarsu sa’ad da na yi musu wa’azi shekarun baya. Daga baya ba da sanina ba, wasu Shaidun sun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su kuma suka taimaka musu su zama bayin Jehobah. Ina farin ciki cewa irin da na shuka ya yi girma kuma an girbe shi.”—Karanta 1 Korintiyawa 3:6, 7.

18. Wane dalilin yin farin ciki ne aka ambata a 1 Korintiyawa 3:8?

18 Na biyu, muna farin ciki sa’ad da muka tuna da kalmomin manzo Bulus. Ya ce: ‘Kowane za ya sami nasa lada gwargwadon wahalarsa.’ (1 Kor. 3:8) Ana ba da lada ne dangane da aikin da mutum ya yi, ba dangane da yawan mutanen da muka koya wa gaskiya ba. Hakan abin ƙarfafa ne sosai ga ’yan’uwan da ke wa’azi a yankunan da mutane ƙalila ne kawai suke sauraron saƙon Mulkin. A wurin Allah, duk Mashaidin da ya yi wa’azi da zuciya ɗaya yana “bada ’ya’ya da yawa,” kuma ya kamata ya yi farin ciki.—Yoh. 15:8; Mat. 13:23.

19. (a) Ta yaya annabcin da ke littafin Matta 24:14 yake sa mu farin ciki? (b) Me ya kamata mu tuna ko da ba mu sami damar taimaka wa wani ya soma bauta wa Jehobah ba?

19 Na uku, muna farin ciki domin aikinmu yana cika annabci. Ka yi la’akari da amsar da Yesu ya ba almajiransa sa’ad da suka tambaye shi cewa: “Me ne kuma alamar zuwanka da cikar zamani?” Yesu ya gaya musu cewa sashe ɗaya na wannan alamar shi ne wa’azin da za a yi a dukan duniya. Shin yana magana ne game da taimaka wa mutane su soma bauta wa Jehobah? A’a. Ya ce: ‘Wannan bishara kuwa ta mulki za a yi wa’azinta cikin iyakar duniya domin shaida.’ (Mat. 24:3, 14) Hakan ya nuna cewa wa’azin Mulki, wato shuka iri, sashen alamar ne. Saboda haka, yayin da muke wa’azin Mulkin, ya kamata mu sani cewa ko da ba mu yi nasara wajen taimaka wa wani ya soma bauta wa Jehobah ba, mun ba da “shaida.” d Hakika, ko da mutane sun saurare mu ko a’a, muna saka hannu wajen cika annabcin Yesu kuma muna da gatan zama “abokan aiki na Allah.” (1 Kor. 3:9) Tabbas, wannan dalili mai kyau ne na yin farin ciki!

“Daga Fitowar Rana Har Faɗuwarta”

20, 21. (a) Ta yaya Malakai 1:11 yake cika? (b) Mene ne ƙudurinka game da aikin girbi, kuma me ya sa?

20 A ƙarni na farko, Yesu ya taimaka wa almajiransa su fahimci cewa wa’azi aiki ne na gaggawa. Daga shekara ta 1919, Yesu ya taimaka wa mabiyansa su fahimci hakan. A sakamakon haka, bayin Allah sun sa ƙwazo sosai a wa’azin da suke yi. Hakika, babu abin da ya isa ya hana mu wannan aikin. Kamar yadda Malakai ya annabta, ana yin wannan wa’azin ne “daga fitowar rana har faɗuwarta.” (Mal. 1:11) Hakika, daga fitowar rana har faɗuwarta, wato daga gabas zuwa yamma, ko da a ina suke a duniya, masu shuki da kuma masu girbi suna farin ciki tare. Kuma daga fitowar rana har faɗuwarta, wato daga safiya zuwa yamma, muna yin wa’azi da gaggawa.

21 Idan muka duba muka ga yadda ƙaramin adadin bayin Allah ya yi girma ya zama “al’umma mai-ƙarfi” a cikin shekaru 100 da suka shige, zuciyar kowannenmu ta “motsu” kuma “ta buɗe” saboda farin ciki. (Isha. 60:5, 22) Bari wannan farin cikin da kuma ƙaunarmu ga Jehobah, wanda shi ne “Ubangijin girbi,” ya motsa kowannenmu ya ci gaba da yin iya ƙoƙarinsa wajen yin wannan aikin girbi mafi girma a tarihi!—Luk 10:2.

a Sa’ad da Yesu ya ce ‘gonaki sun rigaya sun yi fari,’ wataƙila yana magana ne game da fararen tufafin da Samariyawan da suke zuwa wurinsa suka saka.

b Domin ƙarin bayani game da wannan lokacin da kuma shekarun da suka biyo baya, muna ƙarfafa ka ka karanta littafin nan Jehovah’s Witnesses—Proclaimers of God’s Kingdom, shafuffuka na 425-520, wanda ya bayyana abin da aka cim ma daga shekara ta 1919 zuwa 1992.

c Don ƙarin bayani game da wannan annabcin, ka duba Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Yuli, 2002, shafuffuka na 21-31.

d Ɗaliban Littafi Mai Tsarki sun riga sun fahimci wannan muhimmiyar gaskiya a lokacin. Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Nuwamba, 1895, ta ce: “Amma idan har za a iya tattara ƙananan alkama, to, za a iya ba da shaida sosai game da gaskiya. . . . Kowa zai iya yin wa’azin bishara.”