BABI NA BIYAR
Fansa, Kyauta ce Mafi Girma Daga Allah
1, 2. (a) Idan wani ya ba ka kyauta, me yake sa ka daraja ta? (b) Me ya sa fansa kyauta ce mafi girma da Allah ya ba mu?
SHIN wani ya taɓa yi maka kyauta da ka daraja sosai? Idan kyautar ta sa ka farin ciki ko kuma abu ne da kake bukata sosai, babu shakka, za ka gode ma wanda ya ba ka kyautar.
2 A cikin dukan kyautar da Allah ya ba mu, akwai wanda muka fi bukata. Wannan ita ce kyauta mafi girma da Allah ya ba ’yan Adam. A wannan babin, za mu koya cewa Jehobah ya ba da Ɗansa, wato Yesu Kristi, don mu rayu har abada a nan gaba. (Karanta Matta 20:28.) Kuma Jehobah ya nuna cewa yana ƙaunar mu ta wajen aiko da Yesu zuwa duniya don ya fanshe mu.
MECE CE FANSAR?
3. Me ya sa mutane suke mutuwa?
3 Fansar hanya ce da Jehobah ya yi amfani da ita don ya ceci ’yan Adam daga zunubi da kuma mutuwa. (Afisawa 1:7) Idan muna so mu gane dalilin da ya sa muke bukatar fansa, dole ne mu san abin da ya faru dubban shekaru da suka shige a lambun Adnin. Iyayenmu na farko Adamu da Hawwa’u, sun yi zunubi kuma sun mutu sanadiyyar hakan. Muna mutuwa a yau domin mun gāji zunubi daga Adamu da Hawwa’u.—Ka duba Ƙarin bayani na 9.
4. Wane ne Adamu, kuma wane gata ne yake da shi?
Luka 3:38) Jehobah yana magana da shi a kai a kai. Ƙari ga haka, ya bayyana wa Adamu dalla-dalla abin da yake bukata a gare shi kuma ya ba shi aikin da zai ji daɗin yi.—Farawa 1:28-30; 2:16, 17.
4 Sa’ad da Jehobah ya halicci mutum na farko, wato Adamu, Ya ba shi wani abu mai tamani sosai. Ya halicce shi cikakke, wato ba zai yi ciwo ba ko tsufa balle ma ya mutu. Ƙari ga haka, zai iya yanke shawara mai kyau kuma ya riƙa yin abubuwa babu kuskure. Jehobah yana kamar uba ga Adamu domin Shi ne ya halicce shi. (5. Mene ne ma’anar furucin nan, Allah ya halicci Adamu ‘cikin kamaninsa’?
5 Allah ya halicci Adamu ‘cikin kamaninsa.’ (Farawa 1:27) Jehobah ya yi shi da irin halayensa, wato ƙauna da hikima da adalci da kuma iko. Ya ba Adamu ’yancin zaɓan abin da yake so. Adamu ba kamar amalanke ba ne da yake zuwa duk inda aka tura shi. Don haka, zai iya yanke shawarar yin nagarta ko kuma mugunta. Da a ce Adamu ya yi biyayya ga Allah, da ya yi rayuwa a Aljanna har abada.
6. Wace hasara ce Adamu ya yi a lokacin da ya yi zunubi? Ta yaya hakan ya shafe mu?
6 A lokacin da Adamu ya ƙi bin dokar Allah, an yanke masa hukuncin kisa, don haka, ya yi babbar hasara. Ya yi hasarar dangantakarsa da Jehobah da ransa da kuma Aljannar da yake ciki. (Farawa 3:17-19) Adamu da Hawwa’u sun ƙi bin dokar Allah kuma hakan ya sa sun rasa begen yin rayuwa har abada. Abin da Adamu ya yi ya sa “zunubi ya shigo cikin duniya . . . mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” (Romawa 5:12) Sa’ad da Adamu ya yi zunubi, ya ‘sayar’ da kansa da mu cikin zunubi da kuma mutuwa. (Romawa 7:14) Muna da wani bege kuwa? Ƙwarai kuwa.
7, 8. Mece ce fansa?
7 Mece ce fansa? Fansa ta ƙunshi abubuwa biyu. Na farko, fansa kuɗi ne da ake biya don a yi belin wani ko a karɓo wani abu da aka kwace. Na biyu, fansa kuɗi ne da ake biya don wani abu.
8 Babu wani mutum da zai iya biyan abin da Adamu ya ɓatar sa’ad da ya yi zunubi kuma ya jawo mana mutuwa. Amma Jehobah ya yi tanadi don ya ’yantar da mu daga zunubi da kuma mutuwa. Bari mu tattauna amfanin fansar da kuma yadda za ta amfane mu.
YADDA JEHOBAH YA YI TANADIN FANSA
9. Da me za a iya biyan fansar?
9 Babu wani cikinmu da zai iya ba da fansa don ya dawo da cikakken ran da Adamu ya ɓatar. Me ya sa? Domin dukanmu ajizai ne. (Zabura 49:7, 8) Saboda haka, ya kamata fansar da za a biya ta zama ran wani cikakken mutum. Shi ya sa Yesu ya “ba da kansa” don shi cikakke ne yadda Adamu yake kafin ya yi zunubi. (1 Timotawus 2:6) Dole ne fansar ta yi daidai da ran da Adamu ya rasa.
10. Ta yaya Jehobah ya yi tanadin fansar?
10 Ta yaya Jehobah ya yi tanadin fansar? Ya yi hakan ta wajen aiko da Ɗansa da yake ƙauna zuwa duniya. Wannan Ɗan, wato Yesu shi ne farkon halitta. (1 Yohanna 4:9, 10) Yesu ya yarda ya bar Ubansa da kuma inda yake a sama don ya zo duniya. (Filibiyawa 2:7) Jehobah ya ƙaurar da ran Yesu daga sama zuwa cikin Maryamu a duniya, sai aka haife shi a matsayin mutum marar zunubi.—Luka 1:35.
11. Ta yaya zai yiwu mutum ɗaya ya ba da fansa don dukan mutane?
Romawa 5:19.) Yesu bai taɓa yin zunubi ba kuma shi ne ya ba da cikakken ransa don ya fanshe mu. (1 Korintiyawa 15:45) Za a yi amfani da cikakken ransa don a kawar da mutuwa a nan gaba.—1 Korintiyawa 15:21, 22.
11 Sa’ad da mutum na farko, wato Adamu ya taka dokar Jehobah, ya yi hasarar cikakken ransa kuma hakan ya shafi dukan ’ya’yansa. Shin akwai mutumin da zai iya kawar da mutuwa? Ƙwarai kuwa. (Karanta12. Me ya sa Yesu ya sha wahala?
12 Littafi Mai Tsarki ya bayyana irin wahalar da Yesu ya sha kafin ya mutu. An yi masa dūkan tsiya, an kafa shi a kan gungume kuma ya sha wahala sosai a gungumen kafin ya mutu. (Yohanna 19:1, 16-18, 30) Me ya sa Yesu ya sha irin wannan wahalar? Domin Shaiɗan ya yi da’awa cewa babu mutumin da zai iya kasance da aminci idan aka tsananta masa. Yesu ya nuna cewa cikakken mutum zai iya kasancewa da aminci ga Allah kome tsananin wahalar da ya sha. Babu shakka, Jehobah ya yi alfahari sosai da Yesu.—Misalai 27:11; ka duba Ƙarin bayani na 15.
13. Ta yaya aka biya fansar?
13 Ta yaya aka biya fansar? A ranar 14 ga watan Nisan shekara ta 33, Jehobah ya bar maƙiyan Yesu su kashe shi. (Ibraniyawa 10:10) Bayan kwana uku, Jehobah ya ta da shi da jiki na ruhu. Yesu yana da ’yanci ya ci gaba da rayuwa a duniya a matsayinsa na kamiltaccen mutum. Amma ya sadaukar da wannan ’yancin ta wajen koma sama don Jehobah ya yi amfani da ’yancin ya fanshi ’yan Adam. (Ibraniyawa 9:24) Jehobah ya amince da fansar kuma hakan ya sa mun sami ’yanci daga zunubi da kuma mutuwa.—Karanta Romawa 3:23, 24.
YADDA ZA KA AMFANA DAGA FANSAR
14, 15. Mene ne ya wajaba mu yi don a gafarta mana zunubanmu?
14 Mun riga mun soma amfana daga kyauta mafi girma da Allah ya ba mu. Bari mu tattauna yadda muke amfana yanzu da kuma yadda za mu amfana a nan gaba.
15 An gafarta zunubanmu. Yin abu mai kyau a koyaushe ba shi da sauƙi. Muna yin kura-kurai, kuma a wasu lokuta, muna faɗin ko kuma yin abin da bai dace ba. (Kolosiyawa 1:13, 14) Me za mu yi don a gafarta mana? Ya kamata mu tuba da gaske kuma mu roƙi Jehobah ya gafarta zunubanmu. Hakan zai sa mu kasance da tabbaci cewa an gafarta mana zunubanmu.—1 Yohanna 1:8, 9.
16. Mene ne ya wajaba mu yi don kada zuciyarmu ta riƙa damun mu?
16 Zuciyarmu ba za ta riƙa damun mu ba. Idan mun lura cewa mun yi wani abin da bai dace ba, zuciyarmu tana damun mu, wataƙila muna ma jin cewa mun kasa sosai. Amma bai kamata mu ji kamar ba za a gafarta mana ba. Idan mun roƙi Jehobah ya gafarta mana, za mu kasance da tabbaci cewa zai saurare mu kuma ya gafarta mana. (Ibraniyawa 9:13, 14) Jehobah yana so mu faɗa masa dukan matsalolinmu da kuma kasawarmu. (Ibraniyawa 4:14-16) Yin hakan zai sa dangantakarmu da shi ta yi ƙarfi.
17. Wace albarka ce za mu samu don Yesu ya mutu dominmu?
17 Muna da begen yin rayuwa har abada. “Hakkin zunubi mutuwa ne; amma kyautar Allah rai na har abada ce cikin Kristi Yesu Ubangijinmu.” (Romawa 6:23) Muna da zarafin yin rayuwa har abada cikin ƙoshin lafiya don Yesu ya mutu dominmu. (Ru’ya ta Yohanna 21:3, 4) Amma mene ne ya wajaba mu yi don mu sami wannan albarkar?
ZA KA BA DA GASKIYA GA FANSAR KUWA?
18. Me ya tabbatar mana cewa Jehobah yana ƙaunarmu?
18 Babu shakka, kana farin ciki sosai sa’ad da wani ya ba ka kyauta mai kyau. Fansar da Jehobah ya tanadar ce kyauta mafi muhimmanci da aka ba mu, kuma ya kamata mu nuna godiya sosai ga Jehobah. Littafin Yohanna 3:16 ya ce, “Allah ya yi ƙaunar duniya har ya ba da Ɗansa, haifaffe shi kaɗai.” Hakika, Jehobah yana ƙaunarmu shi ya sa ya ba da Ɗansa da yake ƙauna sosai. Mun san cewa Yesu ma yana ƙaunarmu don ya kasance a shirye ya mutu dominmu. (Yohanna 15:13) Ya kamata hadayar fansa ta Yesu ta tabbatar maka cewa Jehobah da kuma Yesu suna ƙaunarka.—Galatiyawa 2:20.
19, 20. (a) Me zai taimaka maka ka zama aminin Jehobah? (b) Yaya za ka nuna cewa ka ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Yesu?
19 Yanzu da ka koyi cewa Allah yana ƙaunarmu sosai, yaya za ka iya zama amininsa? Ba shi da sauƙi mu so mutumin da ba mu sani ba. Littafin Yohanna 17:3 ya ce za mu iya sanin Jehobah. Yayin da kake yin haka, za ka ƙara ƙaunar sa, za ka so ka faranta masa rai kuma za ka zama amininsa. Saboda haka, muna ƙarfafa ka ka ci gaba da koyo game da Jehobah ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki.—1 Yohanna 5:3.
20 Ka ba da gaskiya ga hadayar fansa ta Yesu. Littafi Mai Tsarki ya ce “wanda yana ba da gaskiya ga Ɗan yana da rai na har abada.” (Yohanna 3:36) Mene ne ba da gaskiya yake nufi? Yana nufin yin abin da Yesu ya koya mana. (Yohanna 13:15) Furta cewa mun ba da gaskiya ga Yesu bai isa ba. Saboda haka, wajibi ne mu yi ayyukan da za su nuna cewa muna da bangaskiya. Littafin Yaƙub 2:26 ya ce: “Bangaskiya ba tare da ayyuka ba matacciya ce.”
21, 22. (a) Me ya sa ya kamata mu riƙa halartar taron Tuna da Mutuwar Yesu kowace shekara? (b) Mene ne za mu tattauna a Babi na 6 da 7?
21 Ka riƙa halartan taron Tuna da Mutuwar Yesu. A dare na ƙarshe kafin Yesu ya mutu, ya umurce mu mu riƙa tunawa da mutuwarsa. Muna tuna da mutuwarsa kowace shekara kuma ana kiransa Taron Tunawa ko “Jibin Ubangiji.” (1 Korintiyawa 11:20; Matta 26:26-28) Yesu yana son mu tuna cewa ya ba da ransa domin ya fanshe mu. Ya ce: “Ku yi wannan abin tunawa da ni.” (Karanta Luka 22:19.) Idan ka halarci wannan taron, za ka nuna cewa ka tuna da fansar Yesu da kuma yadda shi da Jehobah suke ƙaunar mu.—Ka duba Ƙarin bayani na 16.
22 Fansa ce kyauta mafi girma da aka ba mu. (2 Korintiyawa 9:14, 15) Miliyoyin mutane ma da suka mutu za su amfana daga wannan kyautar. A Babi na 6 da 7, za mu tattauna yadda hakan zai yiwu.