BABI NA SHIDA
Me Ke Faruwa da Mutum Sa’ad da Ya Mutu?
1-3. Waɗanne tambayoyi ne mutane suke yi game da mutuwa, kuma waɗanne amsoshi ne wasu addinai suka bayar?
ALLAH ya yi alkawari a cikin Littafi Mai Tsarki cewa wata rana, ‘mutuwa ba za ta ƙara kasancewa ba.’ (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Mun tattauna a Babi na 5 cewa hadayar fansar Yesu ce ta sa ya yiwu mu sami rai na har abada. Har ila, mutane suna mutuwa. (Mai-Wa’azi 9:5) Saboda haka, wata muhimmiyar tambayar da muke yi ita ce, Mene ne yanayin matattu?
2 Amsar wannan tambayar tana da muhimmanci sosai, musamman ma sa’ad da wani ɗan’uwanmu ko abokinmu ya rasu. Za mu iya yin waɗannan tambayoyin: ‘Wane wuri ya je? Yana ganin mu kuwa? Shin zai iya taimaka mana kuwa? Zai yiwu mu sake ganin shi kuwa?’
3 Addinai suna ba da amsoshi dabam-dabam ga waɗannan tambayoyin. Wasu addinai sun ce idan mutumin kirki ya mutu, zai je sama amma mugaye za su sha azaba har abada. Wasu kuma sun ce idan mutum ya mutu, zai zama ruhu kuma ya koma zama tare da danginsa da sun riga sun mutu. Ƙari ga haka, wasu sun ce idan mutum ya mutu kuma an hukunta shi, za a sake haifarsa da wata siffa dabam ko kuma ya zama dabba.
4. Wane ra’ayi ne kusan dukan addinai suke da shi game da mutuwa?
4 Addinai suna koyar da abubuwa iri-iri. Amma kusan dukansu suna da ra’ayi guda. Sun ce idan mutum ya
mutu, wata gaɓar jikinsa tana ci gaba da rayuwa. Shin hakan gaskiya ne?ME KE FARUWA DA MUTUM SA’AD DA YA MUTU?
5, 6. Me ke faruwa da mutum sa’ad da ya mutu?
5 Jehobah ya san abin da ke faruwa da mu sa’ad da muka mutu. Ya ce idan mutum ya mutu, ya daina rayuwa ke nan. Saboda haka, yadda mutumin yake ji da tunaninsa ba sa ci gaba da rayuwa a wani wuri. * Matattu ba sa gani ko ji ko tunani ko kuma yin wani abu ba.
6 Sarki Sulemanu ya ce “matattu ba su san kome ba.” Matattu ba sa iya ƙauna ko ƙiyayya, kuma “babu wani aiki, ko dabara, ko ilimi, ko hikima, cikin kabari.” (Karanta Mai-Wa’azi 9:5, 6, 10.) Kuma Zabura 146:4 ta ce, idan mutum ya mutu, “shawarwarinsa” sun lalace.
ABIN DA YESU YA FAƊA GAME DA MUTUWA
7. Mene ne Yesu ya ce game da mutuwa?
7 Sa’ad da Li’azaru abokin Yesu ya mutu, Yesu ya ce wa almajiransa: “Abokinmu Li’azaru yana barci.” Amma Yesu ba ya nufin cewa Li’azaru yana hutu. Yesu ya daɗa da cewa: “Li’azaru ya mutu.” (Yohanna 11:11-14) Yesu ya kwatanta mutuwa da barci. Bai ce Li’azaru yana sama ko tare da danginsa da sun riga sun mutu ba. Kuma bai ce Li’azaru yana shan azaba a cikin wuta ko kuma an sake haifarsa da siffar mutum ko ta dabba ba. A maimakon haka, yanayin Li’azaru yana kamar mutumin da ke barci mai zurfi. Wasu ayoyin Littafi Mai Tsarki sun kwatanta mutuwa da barci mai zurfi. A lokacin da aka kashe Istafanus, Littafi Mai Tsarki ya ce “ya yi barci.” (Ayyukan ) Manzo Bulus ya ce wasu Kiristoci ma “sun yi barci,” wato sun mutu.— Manzanni 7:601 Korintiyawa 15:6.
8. Ta yaya muka san cewa Allah bai halicci mutane don su riƙa mutuwa ba?
8 Shin Allah ya halicci Adamu da Hawwa’u don wata rana su mutu ne? A’a! Jehobah ya halicce su don su yi rayuwa har abada cikin ƙoshin lafiya. A lokacin da Jehobah ya halicci mutane, ya halicce su ne da marmarin yin rayuwa har abada. (Mai-Wa’azi 3:11) Iyaye ba sa son ’ya’yansu su tsufa kuma su mutu, Jehobah ma ba ya son mu tsufa kuma mu mutu. To, idan Allah ya halicce mu mu yi rayuwa har abada, me ya sa muke mutuwa?
ME YA SA MUKE MUTUWA?
9. Me ya sa dokar da Jehobah ya ba Adamu da Hawwa’u yake da sauƙi?
9 Jehobah ya gaya wa Adamu a gonar Adnin cewa: ‘An yarda maku ku ci daga kowane itacen gona a sāke: amma daga itace na sanin nagarta da mugunta ba za ku ɗiba ba ku ci: cikin rana da kuka ci, mutuwa za ku yi lallai.’ (Farawa 2:9, 16, 17) Wannan dokar ba mai wuya ba ce don Jehobah yana da damar gaya wa Adamu da Hawwa’u abin da ya kamata su yi da wanda bai kamata su yi ba. Yin biyayya ga Jehobah zai nuna cewa suna daraja ikonsa. Hakan zai kuma nuna cewa suna godiya don dukan abubuwan da ya tanadar musu.
10, 11. (a) Ta yaya Shaiɗan ya sa Adamu da Hawwa’u suka yi rashin biyayya ga Allah? (b) Me ya sa Adamu da Hawwa’u ba su da hujjar taka dokar Allah?
10 Abin baƙin ciki, Adamu da Hawwa’u sun ƙi bin dokar Jehobah. Shaiɗan ya gaya wa Hawwa’u cewa: “Ashe, ko Allah ya ce, ba za ku ci daga dukan itatuwa na gona ba?” Sai Hawwa’u ta ce: “Daga ’ya’ya na itatuwan gona an yarda mana mu ci: amma daga ’ya’yan itace wanda ke cikin tsakiyar gona, Allah ya ce, ba za ku ci ba, ba kuwa za ku taɓa ba, domin kada ku mutu.”—Farawa 3:1-3.
11 Sai Shaiɗan ya ce: “Ba lallai za ku mutu ba: gama Allah ya sani ran da kuka ci daga ciki, ran nan idanunku za su buɗe, za ku zama kamar Allah, kuna sane da nagarta da mugunta.” (Farawa 3:4-6) Shaiɗan ya so Hawwa’u ta yi tunanin cewa ita da kanta za ta iya sanin abin da ya dace da wanda bai dace ba. Ban da haka ma, ya yi ƙarya game da abin da zai same ta idan ta ƙarya dokar Allah. Shaiɗan ya ce Hawwa’u ba za ta mutu ba, don haka, Hawwa’u ta tsinka ’ya’yan itacen ta ci kuma daga baya, ta ba maigidanta shi ma ya ci. Adamu da Hawwa’u ba su manta dokar da Allah ya ba su cewa kada su ci ’ya’yan itacen ba. A lokacin da suka ci ’ya’yan itacen, sun ƙi yin biyayya ga doka mai sauƙi da Allah ya ba su. Ƙari ga haka, sun nuna cewa ba su daraja Ubansu na sama mai ƙauna ba. Hakika, ba su da wata hujjar taka dokar Allah!
12. Me ya sa taka dokar Allah da Adamu da Hawwa’u suka yi ya sa Jehobah baƙin ciki?
12 Rashin biyayya da iyayenmu na farko suka yi ga Mahaliccinsu bai dace ba sam. Yaya za ka ji idan ka yi wa ɗanka da ’yarka tarbiyya mai kyau, amma daga baya, sai suka ƙi bin umurninka? Babu shakka, za ka yi baƙin ciki, ko ba haka ba?
13. Mene ne Jehobah yake nufi sa’ad da ya ce wa Adamu “ga turɓaya za ka koma”?
13 Adamu da Hawwa’u sun rasa damar yin rayuwa har abada a lokacin da suka taka dokar Allah. Jehobah ya riga ya gaya wa Adamu: “Gama turɓaya ne kai, ga turɓaya za ka koma.” (Karanta Farawa 3:19.) Hakan na nufin cewa Adamu zai sake zama turɓaya, wato kamar ba a taba halittarsa ba. (Farawa 2:7) Bayan da Adamu ya yi zunubi, ya mutu kuma bai sake rayuwa ba.
14. Me ya sa muke mutuwa?
14 Da a ce Adamu da Hawwa’u ba su yi rashin biyayya ba, da sun ci gaba da rayuwa har yanzu. Amma sa’ad da suka taka dokarsa, sun yi zunubi kuma daga baya Romawa 5:12) Amma wannan ba nufin Allah ga ’yan Adam ba ne. Allah bai halicci ’yan Adam su riƙa mutuwa ba kuma Littafi Mai Tsarki ya ce mutuwa ‘maƙiyiya’ ce.—1 Korintiyawa 15:26.
suka mutu. Zunubi yana kamar cuta mai tsanani da muka gāda daga iyayenmu na farko. An haifi dukanmu cikin zunubi, shi ya sa muke mutuwa. (GASKIYA TANA ’YANTAR DA MU
15. Ta yaya sanin gaskiya game da yanayin matattu zai sa mu ƙi gaskata da ra’ayoyin ƙarya?
15 Sanin gaskiya game da yanayin matattu yana sa mu ƙi ra’ayoyin ƙarya. Littafi Mai Tsarki ya ce matattu ba sa wahala ko kuwa baƙin ciki. Ba za mu iya magana da su ba kuma su ma ba za su iya magana da mu ba. Ba za mu iya taimaka wa matattu ba kuma ba za su iya taimaka mana ba. Bai kamata mu ji tsoron su ba domin ba abin da za su iya yi mana. Amma addinai da yawa suna koyar da cewa matattu suna rayuwa a wani wuri kuma idan mun biya shugabannan addinai, za su taimaka mana ta wajen tsarkake mataccen. Idan mun san gaskiya game da yanayin matattu, za mu ƙi waɗannan ra’ayoyin ƙarya.
16. Wace ƙarya ce addinai da yawa suke koyarwa game da matattu?
16 Shaiɗan yana amfani da addinan ƙarya don ya sa mu yi tunani cewa matattu suna da rai. Alal misali, wasu addinai suna koyar da cewa sa’ad da muka mutu, akwai wani abu da yake fita daga jikinmu kuma ya ci gaba da rayuwa a wani wuri. Abin da addininka yake koyarwa ke nan, ko kuwa yana koyar da abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da yanayin matattu? Shaiɗan yana amfani da ƙarya don ya sa mutane su daina bauta wa Jehobah.
17. Me ya sa ra’ayin ƙona mutane cikin wuta har abada ya saɓa wa halin Jehobah na ƙauna?
17 Abin da addinai da yawa suke koyarwa bai dace ba ko ƙone miyagun mutane a cikin wuta har abada. Irin wannan koyarwar ta saɓa wa halin Jehobah na ƙauna. Ba zai taɓa hukunta mutane da wuta ba! (Karanta 1 Yohanna 4:8.) Yaya za ka ɗauki mutumin da ya yi wa ɗansa horo ta wajen saka hannunsa cikin wuta? Babu shakka, za ka yi tunani cewa mutumin mugu ne. Ba za ka so kome ya haɗa ku ba. Irin wannan ra’ayin ne Shaiɗan yake so mu kasance da shi game da Jehobah.
kaɗan. Alal misali, wasu suna koyar da cewa za a18. Me ya sa bai kamata mu ji tsoron matattu ba?
18 Wasu addinai suna koyar da cewa idan mutane sun mutu, suna zama ruhohi. Sun ce ya kamata mu daraja kuma mu ji tsoron ruhohin nan domin za su iya zama abokanmu ko kuma magabtanmu. Mutane da yawa sun gaskata da wannan ƙaryar. Suna tsoron matattu kuma hakan na sa su bauta musu maimakon Jehobah. Ya kamata mu san cewa matattu ba su san kome ba, saboda haka, bai kamata mu ji tsoronsu ba. Jehobah ne Mahaliccinmu. Shi ne Allah na gaskiya, don haka, ya kamata mu bauta masa kaɗai.—Ru’ya ta Yohanna 4:11.
19. Ta yaya sanin gaskiya game da matattu zai taimaka mana?
19 Idan muka san gaskiya game da matattu, ba za mu gaskata da koyarwar ƙarya ba. Kuma wannan gaskiyar za ta taimaka mana mu san alkawarin da Jehobah ya yi game da rayuwarmu da kuma abin da zai faru a nan gaba.
20. Mene ne za mu koya a babi na gaba?
20 Wani bawan Allah mai suna Ayuba da ya rayu a zamanin dā ya yi wannan tambayar: “Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa?” (Ayuba 14:14) Zai yiwu mutumin da ya mutu ya sake rayuwa kuwa? Abin da Allah ya gaya mana a cikin Littafi Mai Tsarki yana da ban sha’awa. Za mu tattauna hakan a babi na gaba.
^ sakin layi na 5 Wasu sun gaskata cewa kurwa ko kuma ruhu yana ci gaba da rayuwa bayan mutum ya mutu. Ka duba Ƙarin bayani na 17 da 18.