Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA BIYU

Littafi Mai Tsarki Maganar Allah Ne

Littafi Mai Tsarki Maganar Allah Ne

1, 2. Me ya sa muka ce Littafi Mai Tsarki kyauta ne daga Allah?

YAYA kake ji sa’ad da abokinka ya ba ka wani kyauta mai kyan gaske? Za ka yi marmarin buɗe kyautar kuma za ka yi murna cewa abokinka bai manta da kai ba. Babu shakka, za ka gode masa sosai.

2 Littafi Mai Tsarki kyauta ne daga Allah. Me ya sa? Domin yana ɗauke da bayanan da ba za mu iya samu a wani wuri ba. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya gaya mana cewa Allah ne ya halicci sama da ƙasa da kuma Adamu da Hawwa’u. Yana ɗauke da ƙa’idodin da muke bukata sa’ad da muke cikin matsala. Ya koya mana yadda Allah zai cika alkawarinsa ta wajen mayar da duniya aljanna. Hakika, Littafi Mai Tsarki kyauta ne daga Allah!

3. Mene ne za ka koya yayin da kake nazarin Littafi Mai Tsarki?

3 Sa’ad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka fahimci cewa Allah yana so ka zama amininsa. Dangantakarku za ta yi ƙarfi idan ka ci gaba da koyo game da shi.

4. Mene ne ya burge ka game da Littafi Mai Tsarki?

4 An fassara Littafi Mai Tsarki cikin harsuna sama da dubu biyu da ɗari takwas kuma an buga biliyoyin kofofi. Biliyoyin mutane a duniya suna iya karanta Littafi Mai Tsarki a yarensu. Mutane fiye da miliyan ɗaya suna samun Littafi Mai Tsarki a kowane mako. Hakika, babu wani littafi da ya kai Littafi Mai Tsarki.

5. Me ya sa muka tabbata cewa Littafi Mai Tsarki ‘hurarren’ littafi ne daga Allah?

5 Littafi Mai Tsarki ‘hurarren’ littafi ne daga Allah. (Karanta 2 Timotawus 3:16.) Wasu za su iya ce, ‘Da yake mutane ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki, me ya sa za a ce littafi ne daga Allah? Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Mutane sun yi magana daga wurin Allah, ruhu mai tsarki ne yana motsa su.’ (2 Bitrus 1:21) Za a iya kwatanta hakan da manajan da ya sa sakatarensa ya rubuta masa wasiƙa. Shin wasiƙar ta manajan ne ko kuma ta sakataren? Babu shakka, ta manajan ne. Haka ma, Allah ne mawallafin Littafi Mai Tsarki ba mutanen da suka rubuta shi ba. Allah ne ya yi musu ja-gora. Hakika, Littafi Mai Tsarki “maganar Allah” ne.—1 Tasalonikawa 2:13; ka duba Ƙarin bayani na 2.

Akwai juyin New World Translation of the Holy Scriptures a harsuna da yawa

BABU KUSKURE A LITTAFI MAI TSARKI

6, 7. Me ya sa muka tabbata cewa babu rashin jituwa a littattafan Littafi Mai Tsarki?

6 An yi sama da shekaru dubu ɗaya da ɗari shida ana rubuta Littafi Mai Tsarki. Marubutan ba su rayu a lokaci ɗaya ba. Wasu suna da ilimi sosai wasu kuma ba sosai ba. Alal misali, ɗaya cikinsu likita ne. Wasu kuma manoma da masu kama kifi da makiyaya da annabawa da alƙalai da kuma sarakuna. Ko da yake mutane da yawa ne suka rubuta Littafi Mai Tsarki, abin da suka rubuta sun jitu da juna. Babu rashin jituwa a cikin littattafan Littafi Mai Tsarki. *

7 Surorin farko na Littafi Mai Tsarki sun faɗi yadda matsaloli suka soma, na ƙarshe kuma sun gaya mana yadda Allah zai magance matsaloli kuma ya mayar da duniya zuwa aljanna. Littafi Mai Tsarki ya faɗi abubuwan da suka faru shekaru dubbai da suka wuce kuma ya nuna cewa nufin Allah yana cika a koyaushe.

8. Ka ba da wasu misalan da suka nuna cewa Littafi Mai Tsarki ya jitu da ilimin kimiyya.

8 Littafi Mai Tsarki ba littafin ilimin kimiyya ba ne ko kuma na makaranta, duk da haka, idan ya yi magana a kan kimiyya, ba ya kuskure. Haka ya kamata littafin Allah ya kasance. Alal misali, littafin Levitikus ya yi bayani a kan yadda za a hana cututtuka yaɗuwa. An rubuta wannan bayanin da daɗewa kafin mutane su san yadda kwayoyin cututtuka suke yaɗuwa. Littafi Mai Tsarki ya kuma ce ba a rataye duniya a kan kome ba. (Ayuba 26:7) A zamanin dā, ba a san yadda ruwan da ke duniya yake zagayawa ba, amma Littafi Mai Tsarki ya yi bayani a kansa.—Mai-Wa’azi 1:7.

9. Wane darasi muka koya daga yadda marubutan Littafi Mai Tsarki suka faɗi gaskiya?

9 Babu kuskure a tarihin da ke Littafi Mai Tsarki. Amma akwai kura-kurai a cikin littattafan tarihi da yawa domin marubutan ba su faɗi gaskiya ba. Alal misali, ba a kowane lokaci suka faɗi lokacin da aka ci ƙasarsu a yaƙi ba. Akasin haka, marubutan Littafi Mai Tsarki sun faɗi gaskiya har sa’ad da aka ci ƙasar Isra’ila a yaƙi. Sun kuma rubuta kura-kuran da suka yi. Alal misali, Musa ya rubuta a Littafin Lissafi cewa ya yi kuskure kuma a sakamakon haka, Allah ya yi masa horo. (Littafin Lissafi 20:2-12) Yadda marubutan Littafi Mai Tsarki suka yi gaskiya ya nuna cewa Littafi Mai Tsarki, littafi ne daga Allah. Hakan ya nuna cewa ya dace mu amince da abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki.

LITTAFIN DA KE ƊAUKE DA SHAWARWARI MASU KYAU

10. Me ya sa shawarar Littafi Mai Tsarki take taimaka mana a yau?

10 Littafi Mai Tsarki “hurarre daga wurin Allah” ne, yana da “amfani ga koyarwa, ga tsautawa, ga kwaɓewa.” (2 Timotawus 3:16) Hakika, shawarar da ke cikin Littafi Mai Tsarki tana taimaka mana a yau. Jehobah ya san yadda ya yi mu, shi ya sa ya san tunaninmu da kuma yadda muke ji. Ya san mu fiye da yadda muka san kanmu kuma yana so mu yi farin ciki. Ya san abin da ya dace da mu da wanda bai dace da mu ba.

11, 12. (a) Waɗanne shawarwari masu kyau ne Yesu ya bayar a Matta surori 5 zuwa 7? (b) Wane darasi kuma za mu iya koya daga Littafi Mai Tsarki?

11 Littafin Matta surori 5 zuwa 7 suna ɗauke da shawarwari masu kyau da Yesu ya bayar a kan yin farin ciki da cuɗanya da mutane da addu’a da kuma yin amfani da kuɗi. Ko da yake ya ba da wannan shawarar kusan shekara dubu biyu da suka shige, yana da amfani sosai a yau.

12 Jehobah ya koya mana ƙa’idodi a cikin Littafi Mai Tsarki da za su taimaka mana mu yi farin ciki a iyalinmu, mu zama ma’aikata masu kirki kuma mu zauna lafiya da mutane. Ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka muku kome yanayinku da ƙasarku da kuma matsayinku.—Karanta Ishaya 48:17; ka duba Ƙarin bayani na 3.

ANNABCIN DA KE LITTAFI MAI TSARKI GASKIYA NE

Ishaya marubucin Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a halaka Babila

13. Wane annabci ne Ishaya ya yi game da birnin Babila?

13 Annabci da yawa na Littafi Mai Tsarki sun riga sun cika. Alal misali, Ishaya ya annabta cewa za a halaka Babila. (Ishaya 13:19) Ya ambata yadda hakan zai faru. Kogi ya kewaye Babila kuma birnin yana da manya-manyan ƙofofi. Amma Ishaya ya annabta cewa za a busar da kogin kuma za a bar ƙofar birnin a buɗe. Mayaƙa za su halaka birnin a sauƙaƙe ba tare da sun yi wani yaƙi ba. Ishaya ya ma annabta cewa Sairus ne zai halaka Babila.—Karanta Ishaya 44:27–45:2; ka duba Ƙarin bayani na 4.

14, 15. Yaya annabcin Ishaya ya cika?

14 Shekaru ɗari biyu bayan an rubuta annabcin, wasu mayaƙa sun kawo wa Babila hari. Wane ne shugaban rundunar? Sarkin ƙasar Fasiya ne mai suna Sairus, kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta. Sairus da mayaƙansa za su iya halaka Babila kamar yadda Ishaya ya annabta kuwa?

15 Babiloniyawa suna yin biki a daren da aka kawo musu harin. Sun yi zato cewa babu abin da zai same su domin birninsu na kewaye da kogi da kuma manyan katanga. Sa’ad da Sairus da mayaƙansa suka isa birnin, sai suka yi wa kogin hanya don ruwan ya ragu. Ruwan ya ragu ya kai yadda sojojin Fasiya za su iya hayewa. Amma yaya za su iya tsallake katangar birnin? Kamar yadda aka annabta, Babiloniyawa sun bar ƙofar birninsu a buɗe, hakan ya sa mayaƙan Fasiya sun shiga birnin ba tare da sun yi wani yaƙi ba.

16. (a) Wane annabci ne Ishaya ya yi game da Babila? (b) Ta yaya muka tabbatar da cewa annabcin Ishaya ya cika?

16 Ishaya ya annabta cewa daga baya, babu mutumin da zai sake zama a Babila. Ya ce: ‘Ba za ta zama da mutane a cikinta ba [har abada], ba kuwa za a zauna a cikinta ba daga tsara zuwa tsara.’ (Ishaya 13:20) Wannan annabcin ya cika kuwa? Wurin da birnin Babila yake a dā yana da nisan wajen mil 50 daga kudancin Bagadaza a ƙasar Iraƙi kuma babu kowa a wurin. Babu wanda ke zama a wurin yau. Jehobah ya share Babila da “tsintsiyar halaka.”—Ishaya 14:22, 23. *

Yadda Babila take yanzu

17. Me ya sa za mu iya gaskata da dukan alkawuran Allah?

17 Annabci da yawa da Littafi Mai Tsarki ya yi da suka cika sun tabbatar da mu cewa waɗanda aka yi game da nan gaba za su cika. Muna da tabbaci cewa Jehobah zai cika alkawarin da ya yi na mayar da duniyar nan aljanna. (Karanta Littafin Lissafi 23:19.) Hakika, muna da begen “rai marar matuƙa, wanda Allah, da ba ya iya yin ƙarya, ya alkawarta tun gaban madawwaman zamanu.”—Titus 1:2. *

LITTAFI MAI TSARKI ZAI IYA GYARA RAYUWARKA

18. Ta yaya manzo Bulus ya kwatanta “maganar Allah”?

18 Mun koyi cewa babu wani littafin da ya kai Littafi Mai Tsarki daraja. Surorin sun jitu da juna kuma idan ya yi bayani game da kimiyya da kuma tarihi ba ya kuskure. Har ila, yana ba mu shawara mai kyau kuma yana ɗauke da annabcin da sun riga sun cika. Ƙari ga haka, manzo Bulus ya ce: “Gama maganar Allah mai-rai ce, mai-aikatawa.” Mene ne hakan yake nufi?—Karanta Ibraniyawa 4:12.

19, 20. (a) Ta yaya Littafi Mai Tsarki zai taimaka maka ka bincika kanka yadda ba ka taɓa yi ba? (b) Ta yaya za ka nuna cewa kana daraja Littafi Mai Tsarki?

19 Littafi Mai Tsarki yana da ikon sa ka canja salon rayuwarka. Zai sa ka bincika kanka yadda ba ka taɓa yi ba. Zai taimaka maka ka fahimci tunaninka da yadda kake ji. Alal misali, za mu iya ɗauka cewa muna ƙaunar Allah. Amma don mu tabbatar da hakan, ya kamata mu bi dokokin Allah da ke Littafi Mai Tsarki.

20 Hakika, Littafi Mai Tsarki daga wurin Allah ne. Allah yana so ka karanta Littafi Mai Tsarki, ka nazarta shi kuma ka so shi. Ya kamata ka nuna godiya don wannan kyautar da Allah ya ba ka kuma ka ci gaba da bincika shi. Hakan zai sa ka fahimci dalilin da ya sa Allah ya halicci mutane. Za mu tattauna wannan batun a babi na gaba.

^ sakin layi na 6 Wasu sun ce Littafi Mai Tsarki bai jitu da juna ba, amma hakan ba gaskiya ba ne. Ka duba shafi na 4 na ƙasidar nan Littafi Don Dukan Mutane, Shaidun Jehobah ne suka wallafa ta.

^ sakin layi na 16 Idan za ka so ka sami ƙarin bayani game da annabcin Littafi Mai Tsarki, ka duba shafuffuka na 27-29 na ƙasidar nan Littafi Don Dukan Mutane, Shaidun Jehobah ne suka wallafa ta.

^ sakin layi na 17 Halakar Babila ɗaya ce daga cikin annabcin Littafi Mai Tsarki da suka cika. Za ka iya samun bayanai a kan annabci game da Yesu a Ƙarin bayani na 5.