DARASI NA 8
Me Ya Sa Muke Saka Tufafin da Ya Dace Zuwa Taronmu?
Ka gan irin adon da Shaidun Jehobah suka yi a cikin hotunan da ke cikin ƙasidar nan sa’ad da suke halartan taronsu? Me ya sa muke mai da hankali sosai ga irin tufafin da muke sakawa da kuma adon da muke yi?
Don mu girmama Allahnmu. Allah ba ya mai da hankali ga irin shigar da muka yi kawai. (1 Sama’ila 16:7) Duk da haka, sa’ad da muka taru don mu bauta wa masa, ya kamata mu nuna cewa muna daraja Allah da kuma ’yan’uwanmu masu bi. Idan za mu je gaban sarki ko kuma shugaban ƙasa, babu shakka, za mu yi shiga mai kyau wadda za ta nuna cewa muna daraja matsayinsa. Hakazalika, irin tufafi da adon da muka yi sa’ad da muka halarci taro zai nuna cewa muna daraja “Sarkin al’ummai,” Jehobah Allah, da kuma wurin da muke bauta masa.—Irmiya 10:7.
Muna so mu nuna wa mutane irin ƙa’idodin da muke bi. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa Kiristoci su yi adon da zai nuna cewa suna da ‘ladabi tare da hankali.’ (1 Timotawus 2:9, 10) Saka tufafin da ke nuna cewa muna da “ladabi” yana nufin cewa, ba za mu saka tufafin da zai sa mu zama abin kallo ba, wato, tufafin da zai ta da sha’awa ko kuma wanda zai nuna jikinmu. Kasancewa masu “hankali” yana taimaka mana mu saka tufafi mai kyau, ba marar tsabta ba ko kuma waɗanda suka wuce kima. Duk da haka, waɗannan ƙa’idodin suna ba mutum zarafin yin zaɓin da yake so. Da zarar mutum ya gan mu ko da ba mu ce uffan ba, irin shigar da muka yi za ta iya “zama ado ga koyarwa ta Allah Mai-cetonmu” kuma ta “ɗaukaka Allah.” (Titus 2:10; 1 Bitrus 2:12) Idan muka saka tufafi mai kyau sa’ad da muke halartan taro, za mu sa mutane su kasance da ra’ayi mai kyau game da bautar Jehobah.
Kana iya halartan taro a Majami’ar Mulki ko da ba ka da tufafin da suka dace da hakan. Ba ma bukatar mu saka tufafi masu tsada kafin shigarmu ta kasance mai kyau.
-
Me ya sa irin adon da muke yi sa’ad da muke bauta wa Allah yake da muhimmanci?
-
Waɗanne ƙa’idodi ne muke bi sa’ad da muke zaɓan irin tufafin da za mu saka da kuma irin adon da za mu yi?